← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 43

Sashe 31

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta cikin hijabinta ya dada rungomata jikinsa, yana mata hira mai dadi. Nan kuwa ya tafi da hankalinta har jirgi ya daidaita a sama ba ta masan an tashi ba. Sigh of relief ya saki lokacin da ya ga ba tayi reacting to take off din su ba. Ita ce a zaune bakin taga saboda haka ya rankwafo ta gefenta yana mata explaining wasu abubuwa har kuma suka shiga gajimare sosai suka daina ganin komai. Haka nan da aka kawo abinci shi ya dinga bata a baki. Sosai taji dadin abincin. Shauki ya hana su baccin duk su biyun duk da kashe fitila da a kayi saboda dare ko wasu na bukatar yin bacci a cikin jirgin. Tana rungume a jikinsa suna hirar su kasa kasa. Awa biyar cur suka sauka a airport din birnin Ma’aiki SAW. Hotel din su daf da shabbaki yake. Tsananin murna tun a lokacin taso shiga. Ya lallabe ta sai da suka yi wanka san nan suka shiga anan kuwa suka yi sallar asuba. Tana dosar masallacin ba ta san lokacin da hawaye ya zubo mata ba saboda wani shauki da ya shige ta na murnar ganin abin da tafi muradi yau ta samu. Kullum idan su Farida suka dawo daga ummara ko aikin hajji suna bata labari ta kan ji ta kawatu da son zuwa inda suka je. Nan ne kadai idan sun bata labari take jin son zuwa, amma sauran kasashen da suke zuwa suna bata labari ba su taba dada ta da kasa ba. A ranar dai bayan sallar asuba, baccin gajiya suka yi. Ko karyawa basu samu yi ba sai kusan azahar. Bayan sun idar da sallah ya shiga da ita Raudha. Wayyo kukan dadi kawai take yi. Ya dade yana tsimayin fitowarta har ya fara tsammanin bata tayi tun da wajen shigar mata daban dana maza. Sai bayan kusan awa daya ta fito. Tun daga wan nan lokacin ba abin da suka sa a gaba sai ibada. Kullum karfe biyu na sulusin dare suke zuwa masallaci. Bayan sun gama nafilolin da suka sawwaka, zai dakko Qur’ani mai girma ya bata izu biyar shima ya dauki biyar. Kwana shida cif suka sauke shi. A kawan na takwas suka nufi garin macca domin aikin hajj. Ta ga gata matuka a wajensa. Duk in da zata tana makale a jikinsa kamar za a sace ta. Haka lokacin da za a fita zuwa Minna a karamar motar suka tafi kuma ta wani titin daban wan da duk travelling agency su ne ya yi musu organizing as part of their VIP package. A nan din ma a Camp A ya kama musu tent su biyu kawai sai kananan gadaje guda biyu a ciki da kuma dan karamin bandakinsu attache to the room. Babu wata wahala data fuskanta, saboda ba kananan miliyoyi Al Bashir ya saki ba domin ta samu easy and comfortable Hajj. Ranar da suka yi jifa na farko ranar babbar sallah ke nan ranar suka shiga Macca domin yin dawafin aikin Hajj da kuma sa’ayi. Bayan sun kamalla jifa na biyu da na uku suka dawo hotel din su dake daf da harami a Zam Zam towers. Da magariba suka shiga ka’aba suka yi sallah. Sai da suka yi isha da shafa’I da wuturi. Ya kuma kara da wata nafila da ita dai ba ta san ta meye ba. Ya dade yana addu’a wacce ta fuskanci rayuwarsu da ita yake tayi wa wan nan addu’ar a gaban dakin Allah. Bayan sun fito suka nufi inda zasu ci abinci. Abu daya ta lura dashi yau wata irin annshuwa yake ji a cikin ransa. Bayan sun koma masaukinsu, ita ta fara shiga tayi wanka san nan shi ma ya shiga. Sabanin lokutan baya yau wata irin silk negligee ya ajiye mata a kan gado. Ita data daga ma ta dauka shimi ce. Ba ta san ta meye ba ta mayar da ita ta jiye, ta dauko zulumbuwar rigar da ta saba sakawa ta saka. Tana gyara gashinta ya fito daga wanka. “ya haka”? ya tambaye tare da kai kallonsa wajen rigar da ya ajiye mata. Bata kula shi ba ta ci gaba da abin da take yi na kokarin gyara inda zata kwanta, wanda tun da suka zo Saudiyya kullum a kan couch din dakin yake kwana ya bar mata gadon. Ta ci gaba da kokarin shimfida masa quilt da kuma pillow domin yaji dadin kwanciya. Ya dan daure muryarsa alamun ba wasa yace “ke ba dake nake Magana bane kin yi banza da ni”. Ta dan tsorata jin yayi mata Magana da muryar da bata taba jin yayi zance da ita ba. “Wai da shimfida nake kokarin yi maka”. “ban saki ba, ba kuma naso. And kafin raina ya baci ki cire wan nan buhun da kika zuba ajikinki ki dau kayan da na ajiye miki ki saka”. Ta kai kallonta kan rigar amma ta kasa dauka. Tsawa ya sake daka mata “wai ba Magana nake miki ba”. A firgice ta dau rigar ta shiga bandaki a guje. Dariya ya saki kasa kasa ganin yadda ta tsorata, amma ba ya son bata fuskar yi masa musu sai ya dada shan kunu. Ta sa riga amma ta kasa fitowa, saboda haka da taji alamar murda kofar yana fadin “ba zaki fito bane” a tsorace ta dau bath robe din data cire ta zurma ta dora a kan night gown din data saka, wacce ta bi ta lafe a jikinta ta fitar da duk wani asirin kyau da ta boye cikin hijabinta. Yana ganinta haka bai san sanda dariya ta so kubuce masa ba. Shi ya karasa inda ta tsaya yan fadin “to karaso mana, na rasa wan nan sanyin naki na yau na menene. Ni ne fa Balarabenki ba wani ba”. Ta bayan ta ya tsaya ya rankwafo ta bayanta. Hannayensa ya saka ya cire nata daga rikon rigar wankan da tayi. Ya salube ta, san nan ya tsaya ya na kare mata kallo, wanda bai taba yi mata irinsa ba sai yau din nan. Allah ya sani da kyar ya iya karasa alkawarin bakacen da yayi wa ubangiji na cewar idan har Allah ya sa ya auri Zainab zai daurewa zalamarsa har sai ya kawota gaban dakin Allah san nan komai zai kasance tsakaninsu. Haka ya faru ne sakamakon wata hira da suka taba yi shi da ita. Tambayarta yayi yace “Putri a duniya wacce kasa kike da burin zuwa a rayuwarki”? Da wani irn excitement a fusakar ta tace “ai ni ba inda nake son zuwa irin kasa mai tsarki. Ranar da duk na ganni a garin macca da Madina ban san irin farin cikin da zan yi ba. Kullum idan su Farida suka je suka dawo suna bani labara sai in ji kamar in yi tsuntsuwa in je”. “Amma ya akayi suka je ke ba ki samu zuwa ba bayan kece babba”. Kasa tayi da murnarta and all the excitement left her voice. Cike da rauni tace “saboda ni bani da kokari bana cin jarrabawa”. Ya tausaya mata matuka. Ganin yadda take da ilmin addini da kuma yadda take jin larabci ya san kawai muguntar matar gidan ce ta hana ta zuwa. Wan nan shine dalilinsa na yin wan nan bakace. Ni da na ga shiru ba a fara honey moon ba, har na tsorata na dauka ko maganar MomI ce ke son tabbata, ashe shi baka ce ne kansa. Ya kai minti uku yana kare mata kallo. Wata irin kirar jiki gareta da shi dai a iya yawonsa bai taba ganin perfection irin nata ba. Da yake ganinta cikin hijabi, ya dauka flat take, ashe all the curves are in the right places. Jikinta so beautiful. Da ya kai hannunsa kuwa ya taba skin din jikinta, sai da ya saki wani irin numfashi. So soft and silky. Taushin hannunta ya dade yana bashi mamaki. Ga shi kullum cikin aiki take, amma hakan bai sa hannayenta tauri ba, saboda bata rabo da shafa man kadanya a hannu nata. Ya saba da jin kamshin jikinta, amma hakan bai sa yana jin ya gaji da shaker sa ba. Wajen wuyanta ya tsaya yana shinshinarta. Ya kuwa shaki kamshin ta sosai, kafin ya sauke labbansa akan nata. Take jikinta ya dauki rawa na abin da taji da bata taba jin irinsa ba. Ta saba da dan light kiss da yake mata, amma wannan French kiss din is different. Take jikinta ya dauki rawa. Kafafunta suka kasa daukarta. Jin zata zube a wajen ya dauke ta kamar karamar yarinya, ya shimfideta a kan gadon, shima ya bita . To alhamdu Lillah kazafin Momi ya tabbata karya, saboda a wan nan rana ya tabbatarwa da Zainab cewa shi lafiyayyen namiji ne mai tsananin kwazo kuwa. Saboda asuba ita dai ta kasa ko motsi, amma shi ya daure a gaggauce ya samu raka’a daya a masallaci. Sai da ya dawo san nan ya taimaka mata ta gyara jikinta tayi wanka. Sallah dai bata samu ba sai bayan shida na safe. Ita dai duka tayi sanyi saboda bata tsammaci haka daga gareshi ba. Yayin da shi kuwa murna kamar ta zautar da shi. Gaba daya ya rude mata sai rawar jiki yake. Ga shi ya hana ta matsawa ko nan da can kamar za a sace ta. Kwana biyu kawai suka kara a Macca suka shiga Riyadh wajen wani abokinsa da suke kasuwanci tare a nan kasar. Na ma dai amarcin da suke ragargaza ya fi komai. Da zasu tafi kuwa kyautar sarka babba da awarwaron gwal guda shida suka bata. Daga nan suka wuce China saboda shi kansa ya san yayi neglecting aikinsa. Gidansa na zhoungou anan suka sauka. Bilkisu taji dadin ganinta. Shima dai nan din aiki rabi da rabi ne. saboda baya sama da awa uku a factory bai zo inda take ba. Ta dai sha tsokana wajen Bilkisu. [8/8, 22:27] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 29 BY HANNE ADO ABDULLAHI Soyayya dai ana rangada ta tsakanin Al Bashir da Zainab. Ga karatun ta na koyon turanci da suka dage dashi. Kullum kafin ya fita zai koya mata newa words da spelling da pronunciation dinsu. Haka zalika zai bata example yadda zata yi constructing sentence da su. San
Chapter 31 · 0% Book details