Sashe 6
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
[8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA👪 IN FIKI MIKI💑 Page 6 BY HANNE ADO ABDULLAHI Ita dai Khadija da Mallam Usman sun samu nasarar tsara rayuwarsu ba tare da dogaro da aikin gwammnati ba. A yayin da shi kuma Dr Abdullahi yake ta samu nasara a fannin aikin nasa. Ita ma Hajiya Rumaisa watau matarsa kuma uwar goyon Zainab itan ma tana samun ci gaba a fannin aikin nata. Zainab ce dai take samun ci gaban me hakan rijiya. Tana dada girma wahala na karuwa a kanta. A sunan itace babba momi ta dora mata gyaran dakinsu da kuma wankin bandakinsu kafin su tafi makaranta. Hakan ya sanya kullum sai ta makara. Ai da farkon zuwanta da yake bata makara tana da kokari a makaranta. Amma daga baya da zuwan nata daukar karatu ya fara zama mai dadash dash sai ta ja baya. Hakan ya faru ne saboda dokar da momi ta bayar ta cewar duk wanda ya haura bakwai da minti ashirin baya cikin school bus to driver yaja ya tafi. Tun hudu take tashi. Ta sawa kowa abincin lunch box amma ban da ita. Saboda sau daya tayi zawo, Mummy ta yanke hukuncin wai cikin ta ba ya san kayan zaki. Saboda haka dan lemon makaranta da kuma su biskit da dan chocolate duk a haka tayi wayon haramta mata su. Uniform din kannenta da kuma na su Anti Sakina da suke manyan 'yan secondary tun dare take fitowa da kowa nasa. Ta dora su singlet da socks da kuma vest akai. Kowa ta jera nasa. Amma idan su Sakina suka ga dama sai sun zo sakawa suce ta sake goge musu da iron. Ta jira 'yan mantan su yi wanka. San nan tayi wa kananan maza guda biyu ta shirya su. Ta dawo ta gyara gadajen da bata da ikon hawa. San nan ta wanke toilet. Ta jika inner wears da suka cire da sunan idan ta dawo ta wanke su. Kuma duk haka ba zai yiwuba sai sun gama shiryawa sun fice daga dakin. Amma duk hanzarinta kafin ta gama sai dai taji tashin motarsu sun tafi sun barta. Kafin term biyu kuwa ta koma jakar aji. Da Momy ta ga ta samu nasara a haka sai kuma ta kirkiro dabarar kyautatawa ga wadanda suka ci jarrabawa. Ko kayan sallah za'a dinka maka sai kaci jarrabawa. Ita ta cusawa Daddynsu wan nan akidar. Kuma saboda salon yaudara irin tata sai ta nuna masa saboda Zainab ta kirkiri yin hakan ko zata zuciya ta dago. Shi kuwa ya yarda da hakan. A wan nan term din ma sun kawo report dinsu. Farida da Farisa kamar ko yaushe Farida first, Farisa kuma second. Ita kuwa ta dauko ajin gaba daya. Daddy fada yake yi kamar zai ari baki. Momy tayi saurin tare shi da cewar "ka dinga hakuri daddyn Farida. Ka san kowa da irin yanayinsa". "Wanne irin yanayi"? Ya fada cikin muryar fadar. Sauran kannenta su kai biyu garesu da suke iya daukar karatu ita bata dauka. Ai in dai haka zaki yi nikuwa ba zamu shirya dake ba". Ya fada yana mai wurga mata report card din ta. Da yake shi a boko ya samu tasa nasarar gani yake yi idan dai ba boko kayi ba to kuwa baka da wata madafa. Ya yanke shawarar dauko lesson teacher, amma shima sai dai sauran kannenta su mora. Amma ita sai Momi tace wai Farida ta koya mata. Ita kuma ta kora ta kicin ko kuma ta sata gyaran dakinta ko dai wani aiki na tsakar dare. Idan kuma Faridan ta dage da niyyar koya mata, uwar ta hana ta. Ta kora ta tace ta je ta ci gaba nata karatun. A lokacin da Momi ta sake haihuwa ta samu twins dinta. Halim da Hanif shi ke nan abu ya dada jagulewa Zainab. Duka duka a lokacin sherarta goma, amma hatta kwana da jinjirayen nan ita take yi. Uwar ta dira su kan shan madara. Hakan tasa Zainab ta koma kamar uwarsu. Ga su da dan banzan kukan dare haka take fama kwana rarrashinsu. Da safa kuma ta dora da hidimar yayyensu guda uku da kuma ta unties din su guda biyu. Saboda haka a dan lokutan da ta samu ta leka makarantar ma , bacci take yi a lokacin ajin. Malaman sun yi punishment har sun gaji. Don ko sata akayi ta tsaya da sunan horo tsaf Zainabun ka zata iya bacci a tsayen da take. Sau biyu tana reapeating class three da four. Suma kuma kyale ta kawai akayi ta wuce ba don taci ba. Tana da shekara sha daya da rabi aka yi common entrance ta makarantar gwamnati. Ita din ma faduwa tayi. Farida Farisa kuwa da kaninsu sai prizes suke amsows a makaranta. Haka nan isalamiyyar itama sai dai sauki. A gida suke karatun Mallam maigadin su shi yake biya musu. Idan ta tashi zuwa sai Momi ta hado ta da su Halim a zummar basa yadda da kowa sai ita. Kuma hakan ne tunda ita suka budi ido suka saba gani tana hidima da su. Uwarsu ko kwana nawa zatayi bata nan bai dame su ba. Amma ita Zainab kullum suna nanike a jikinta. Fadan wannan term din yafi na kowanne term. Saboda hukumar makaranta dai tace sai dai Zainab ta sake reapeatin class five, amma su ba za su barta ta tafi secondary ba. Daddy kuma yace ya gaji da asarar kudin makaranta a kanta. Tun da ita kowanne aji sai ta maimaita shi san nan ta wuce. Ita dai tana tsugunne sai kuka take yi. Momi na budar baki tace "kaga Daddyn Farida ba fa laifinta bane. Ka san shi kokarin yaron daga nonon uwarsa yake shansa. Ba ka ganin sauran kannenta. Ka yi hakuri its not her fault". "Yanzu kina nufin haka zan zauna ina asarar kudi na a banza". "Eh to kaima kana da gaskiya. Amma abin da za a yi. Kaga stantard din makarantar su Farida yayi mata tsauri. Abin da za a yi ka dawo da ita islamic school din kasan unguwar nan. Sai a samo mata lesson teacher. Idan ta dan ware sai a mayar da ita". Ha kan kuwa akayi. Ta dawo makarantar islamiyya ta gwamnati ta nan bangaren masu karamin karfi a nan unguwarsu. Ita ta samuta huta da fadan babanta shi kuma ya daina asarar school fees. Kuma dadinta da makaranta tara ake shiga a taso sha biyu. Sai hakan yayi mata daidai da schedules dinta. A hankali ma gyaran gidan gaba daya ya koma kanta tunda bata fita da wuri. Idan ta dawo kuma ta dora da renon kannenta. A hankali kuma Momi ta fara dora mata larurar girkin gidan. Shi ma kuwa ba a fi shekara da farawa ba tukunyar gidan ta zama tata. Baba larai matar Mallam watau mai gadin gidansu ita ke taya ta da wanke wanke da kuma sharar waje. Itama sai ta fi samun sauki a haka. Kafin a kai haka ai ta sha bulala a wajen babanta. Amma yanzu kalau suke zaune. Ba ya yi mata fada da yawa balle a kai ga duka. Balle da ke tayi ma kanta horon yi nayi, bari na bari. Dama Farisa ita ta fi janyo mata duka. Ita ma kuma da ke ta gano yanda zata zauna da ita sai ta samu lafiya. Duk abin da tayi mata ko zagi ko rashin kunya ko kuma ta bata mata kaya bata kula ta sai dai ta gyara ta kyaleta. [8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧IN FIKI A MIJI 💑 page 7 BY HANNE ADO ABDULLAHI Haka nan Zainab ta dinga rayuwa cikin ukubar kannenta da kuma momi wacce ita ke zuga uban. Da abin da ya isa da wanda bai kai ba sai tayi ta zuga shi yana dukan baiwar Allah nan. Wani abin tausayi da ya taba faruwa. Sakina ce ta tashi tana holon bata ga dan kunnenta na gwal ba. Bayan kuma ta ajiye shi a gefen kayanta. Bayan nan ne kuma Zainab tazo raba kayan guga. Inda ta sa na kowa a inda yake ta kuma hada da gyara musu zaman kayan nasu. Ita dai tana baya tana malmala tuwon da ta gama kwashewa taji kiran Momi da karfi. Saboda firgita ba ta san sanda ta saki tuwon da kokon suka zube a kasa ba. Sauri take kamar zata kifa. Tana isa ta tarar da Momi da kannenta da kuma 'ya'yanta sun keyawe ta. "Gani Momi" ta fada tana mai durkusuwa gabanta. Bata ji amsa ba sai saukar mari tare da karajin muryar Momi tana fadin "shegiya barauniya ina kika kai dankunne Sakina"? "Wallahi Momi ban ga dankunnenta ba". Cikin muryar kuka take fada. San nan ta juya wajen sauran kannenta tana fadin "don Allah Farida ki gaya mata. Ai bana sata ko. Don Allah ba kullum idan na tsinci kayanku ina nuna muku ba". Farida ita ta rike ta tana cewa "anti Sakina muje ki sake dubawa". "A ina zata sake dubawa? Shegiya barauniya. Uwarki ma haka na sha fama da ita da wan nan sacen sacen. Ashe kin gado ta ban sani ba. Amma idan ni kince karya nake miki ai ubanki zai shigo. Shi ya saki ki fadi gaskiya. Kuma zaki ......." Karar shigowar mota shi ya tsayar da Momi daga maganar data fara. "Yawwa ga shi nan ma ya shigo. Yanzu kya fadi gaskiya". Daddy kuwa na shigowa ya tarar da su duk sun taru a falonsa. Momi na ganinsa ta fara magana cikin muryar rarrashi tana fadin "ki lura ki gane abin da nake gaya miki. Gidan wani zaki nan da 'yan shekaru kadan. Idan kika ce halin banza zaki dinga yi na dauke dauke wahala zaki sha. Gaba daya 'yan uwanki zasu hada baki su miki karya ne. Duk kansu sun yadda ke kika dauka." Daddy jin haka ya sanya shi ya dauko dorinar da ya ajiye domin dukan yara a cewarsa amma fa bata taba shan jinin kowa ba sai na Zainab. Farida na ganin haka ta yi saurin fita daga falon. Ita kuwa Farisa sai dada fadin "ai idan kin ji duka kya fada" take yi. Nan Daddy ya sata ta kwanta rub da ciki ya kuwa kafa mata shaidar zai mata bulala