Sashe 22
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
Venza take hawa. Yayi mamakin dalilin zaman su a kauye. Sai kusan la’asar ya sanya su, su fito ya karasa da su kauyen kera domin gai sawa da kakanin Zainab. Har sun fito zasu shiga motarsu honda accord 2016 sports version yace “a’a gwanda mu hau mai dan tudu saboda yanayin hanyoyi namu”. Tafiyar da bata fi ta dauke su minti talatin ba amma sai da suka dauki kusan awa daya. Can ma Mallam Usman ne yayi hidimar gabatar da su a wajen su Baffa.sun dai sha tsokana. Domin shi Baffa Abdullahi yace a kwai bashin bulalar shadi guda dari a kanta, saboda haka sai Al Bashir ya shirya ya karba, Cike da farin ciki suka baro garin bayan dimbin alkhairin da suka ajiye musu, wanda su Baffa suka yi fada akai. Amma cikin wasa Mustafa yace “cin hanci muka baku saboda ku saki auren Zainab mu mu samu mu aura”. Haka suma su Nenne kakaninta su kuma suka ce musu sadakin su ne suka biya saboda su yiwa kawarsu zaman daki. Cike da farin ciki suka baro garin. A gidan Mallam Usman ne dai ba su basu kudi ba, amma sun bawa yaran gidan kyautar dubu dari da sunan su sha ice cream. [8/7, 21:39] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 22 BY HANNE ADO ABDULLAHI Hajiya Rumaisa kuwa da ta debi yara da sunan mai da su makaranta sai da ta yi yawon shakatawa da su san nan ta mai da su. Ni kaina ban sani ba dama hutun nasu bai kare ba ko kuwa tsabar gata ne ban san abin da ya faru ba. Da farko sun shiga Sudan suka dau tsawon kwana hudu. Nan suka ce tun da karatu bai yi zafi ba,za su bi Momi da Daddy yawo. Inda zaka san da plan dinsu duk visa su iri daya ce. Bayan sun bar Sudan, China suka wuce direct, anan ne Momi ta karbi makudan kudade a wajen Daddy da sunan zata yiwa yara sayayyar kayan aure. Komai na mutum uku ta saya. Daddy yaji dadi matuka ganin yadda ta hada Zainab da yaranta ta sai musu komai iri daya. Bilkisu taji dadin wan nan ziyara ta su. Ga Momi ga Daddy ga Farida ga Farisa ga kuma ‘yar uwarta Sakina. Sosai tayi murna da ganinsu. Anan ne kuma aka ragargaji sayayya. Daga nan suka yi tunanin shiga makka domin Ummara, amma ita ma tun da sukaje harami sau daya, basu sake komawa ba. Sai yawan mall mall da suka dinga yi. Malam Usman ma, ya debi nasa iyalan sun je ummara saboda alkawarin da ya yayi wa Hafsa na cewar idan jarrabawarta tayi kyau zai kaita ummara. Ya kuma cika mata alkawari har kannenta ma suka samu albarkancinta. Ya san kwana biyu kafin tahowarsu Al bashir ya kai musu ziyara. Kuma tabbas bayan nan ko ranar da zasu taho sun yi waya da Hafsa kuma ba wanda yaji labarin za su zo kasa mai tsarki. Saboda tun da Albashir yaje zuwan farko zumunci na waya kullu tsakanin ta da mutan gidan da mahaifiyarta ta ke aure. Gaskiya daga Dr Abdalla har hajiya Rumaisa ba su ji dadin yanayin da suka ga Khadija da mijinita a ciki ba. Ga kyawawan ‘ya’yansu masu dimbin ladabi da biyayya. A wulakance su Rumaisa da nasu 'ya'yan suka gaishe su kamar yadda suka saba gai da dangin mahaifinsu. Shi kuwa Mallam Usman bA wan nan ne a gabansa ba. Rashin ganin Zainab tare da su shi ya daga masa hankali. Ya san kawaicin matarsa. Ko meye zai faru ba za ta taba nunawa ko a fuska rashin ganin su da Zainab ya sosa ranta ba. Saboda haka suna shiga masauki, da hanzari yace “Hafsa nemo min wayar yayarku”. Da sauri ta buga. Ringing daya na biyu ana uku ta dauka. Cike da murna tace “’yar kanwata kina lafiya”? “lafiya kalua Zainabu. Ba ita ba ce Abban kune”. Cikin dariya mai nuna ladabi tace “Lah Abba ban san kai bane. Abba barka da war haka”. Ta gaishe shi tare da dan rusunuwa kamar tana gabansa. Wan nan kuma al’adar ta ce. Domin ko shi Al Bashir idan zata gaishe shi a waya sai ta dan rusuna kamar yana kallonta. Shi ya ci gaba da Magana, yace “zainab ina mutan gidan ku”. “Abba sun yi tafiya. Sun je kai su Farida makaranta”. “Tun yaushe ke nan sukayi tafiyar”? Ta dan daga kanta alamar lissafa wani abu. San nan tace “Abba yau satinsu shida da kwana hudu”. Kamar zai ce wani abu sai kuma yayi controlling kanshi. Yace “shike nan ba damuwa. Abin da nake so dake ki kiyaye mutuncin kanki ki kuma tuna komai ki ka yi Allah na kallonki. Kar ki yi san ranki don ganin ba idon dan Adam a kanki”. “In sha Allahu Abba zan kiyaye. A dai ci gaba da samu a addu’a”. “ba komai Zainab. Me kike so na sayo miki in zamu dawo”. “Nan take ta tuna ankon bakar after dress da zasu yi naa sauka. Saboda haka da hanzari tace “Abba in so samu ne ina son bakar after dress”. “Bayan nan fa”? Ta sake cewa” Abba ita kadai nake so”. Ba yadda bai yi da ita ba ta fadi wani abun, amma sam taki. Daga bisani ya mika mata ummanta da sauran kannen suka gaisa. Hafasat ce ta fita da wayar domin su dan sha hira da yayarta. Gashi dai dan kwanaki ne da fara mu’amalar ta su amma kai kace sun dade da juna yadda suka shaku. Sukan iya kashe sama da awa daya suna hira a waya. Sai da ta shiga daki. San nan tace “Yaya Zee ina ya Bala”? nan dai suka dinke da hira. Sai da za suyi sallama ita ma ta bata sakon turare mai dadi saboda lura da tayi Balan ta mai son kamshi ne. Tsaftar sa da kuma iya gayunsa yasa ya ke dada birgeta. Ba wanda zai kalle shi yace talaka ne a tunaninta. Sai da ma Fatu ta gaya mata ai masu san’ar gwanjo haka suke da gayu saboda suna samun kaya masu kyau kuma da sauki. Da suka dawo kuwa driver ya dauko su a airport sai da suka fara zuwa wajen Zainab, saboda sanin da suka yi na cewa ita kadai ce a gidan. Tayi murna matuka da ganin mahaifiyarta da kuma sauran ‘yan uwanta da kuma Abbansu Hafsa. Rabonta dasu tun ran da taje Garko wajenta babanta yayi mata dukan kawo wuka. Ba yadda bata yi da su ba su shiga sam suka ki. Anan cikin mota suka gaisa. Akwati guda Abban ya mika mata a matsayin tsaraba. Ita ma Hafsa ta bata wata ledar mai dauke da turarrruka har shida duk kuma designer. Na mata uku na maza uku. Anan ne kuma ta san ashe Mallam ya san Abbanta. Ya kawo kudi ya bashi,san nan sukayi sallama suka tafi. Da AlBashir kuwa ya kawo mata ziyara da la’asar ta debo kayan da Abbanta ya sayo mata, wanda ya kasance after dress masu kyau da tsada guda goma da kuma wasu rin dogayen riguna na Morocco masu dan veil a kansu suma kala kala guda goma. Ta dai dauki after dress guda biyu da kuma doguwar riga daya. After din da doguwar rigar ta bawa Fatu. Ta bawa mama Hajjo turare guda daya. Daya kuwa ta bawa Baba laure. Sauran kayan nan haka ta hada su sai ga AlBashir ya kawo mata ziyara. Nan dai inda suka saba tsayawa da shi bakin verender Mallam nan suka tsaya. Bayan sun gaisa. Ta debo tsarabar nan baki daya ta bashi. Tace “ka sayar da kayan na dauki daya na kuma bawa Fatu daya. Ga kuma turare Hafsa ta kawo maka”. Ya dauki turaren Giogio for men ya bude shi sai da ya shaki kamshinsa san nan ya bude kwalbar yana fesawa. Wani dadin kamshi ya baibaiye su. Sai da ya lumshe idonsa domin dadin turaren, san nan yace turare dai na dauka, amma banda kayanki. Idan na dauka inyi me dasu. Ki ajiye mana ki dinga yi min kwalliya ina ganinki ina jin dadi. Da ace ina da hali ai da kin ga kayan kwalli…….” Ita kanta bata san sanda ta kai hannunta ta rufe bakinsa ba alamun bata son maganar da yake yi. “Please na roke ka kar ka kuma yi min makamanciyar maganar nan. In ba haka ba zamu bata. Haka na ganka kuma haka nake son…..” Sai a lokacin kuma taji kunya ta kamata na abin da tayi da wanda ta fada. Shi kuwa he kind of froze saboda dadin kalamanta. Ya san tana son sa amma bata taba fitowa ta fada kuru kuru ba sai yau. Akwai dai alamun kauna da kyautatawa da ta ke nuna masa. Ba shiri ya yi wani dana tsalle tare da juyin 360. Ya bude kwalbar turaren ya ci gaba da fesa musu shi da ita yana fadin “bari kawai yau ayi kamun amarya da ango, tun da yau amarya da kanta ta furta asirin zuciyarta”. Kunya ce ta kamata ba shiri ta tashi da saurin tana kokarin guduwa. Take ya gano wayon da take son yi. Ba shiri shi ma kuwa ya cafki gefen hijabinta ya rike yana fadin “please kar ki kashe min tsananin farin cikin da nake ji a a yau din nan. Na san ki na kaunata, amma nayi ta mafarki ki furta sai yau kuma na samu amma ki na neman ki guje min. haba Putri salju na”. Da kyar ya rarrashe ta ta tsaya, amma fa still yana rike da hijabinta. Tace to ka sakar min hijab mana ai na fasa guduwa”. “tab di jan naki wayon. In saki kigudu ki barni” ya fada da maganar yara, wacce ta sa ta dariya. Haka ta saki jiki suka ci gaba da hirarasu. Su Momi ba su dawo ba sai bayan kwana hudu da dawowar su Mallam Usman. Saboda daga Saudiyya sai suka nemi long transit VISA suka kwana uku a a Dubai. Na ma dai wasu kudin aka sake murkushewa. Wan da daga nan ne suka yi sallama su yaran suka hau jirgin komawa Sudan har da Khalil da yayi joining dinsu wan nan shekarar. Su kuma suka dawo da Halim da Hanif