← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 43

Sashe 30

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko su shagide su fara sekem, ko su fara wani karkada kafar su suna azanto ko shaku shaku. Ana nan ana ta shan dabdala, kawai ba sai mai kida ya canza salo ba. Ba a ankara ba, sai gani Baffan Nene akayi a tsakiyar fili, yana tsuma. Ya wulwula sanda sama ya café habawa sai wuri ya dau tafi da ihu. Ashe wai taken su ne suna samari shi da amininsa baffan Khadija. Shi kuma Baffan Khadija ya taso ya shigo ya daga sanda kamar zai kwala masa, sai kuma ya shafa ta a jikinsa kawai. Nan fa tsoffin nan suka shiga wani takun rawa da matasan kauyen kaf ba su san da irin ta ba. Ai kuwa shi kansa AlBashir da ya dauko wrapper ta dubu ya dauki daya ya mikawa Zainab daya sai da kudin nan suka kare. Na dade banje bikin da naji dadin sa irin wan nan ba. Kusan kowa had fun a wajen. Biki dai bai tashi ba, sai kusan hudu na asuba. Momi na gefe zuciyarta in ban da tafasa ba abin da take yi. Wai wan nan shegiyar Zainab din ce ta samu wan nan daukakar. Sai wani gumi take yi. Najuya naga sansanyar iskar da ke kadawa ba ta sa ko masu rawar sun yi gumi ba sai ita. Nace to ina ga jininta ne ya hau. Bayan an yi sallar asuba da yawa suka samu suka dan runtsa. Daga nan aka fara shiryen shiryen daukar amarya. Da azahar suka bar garin tare da dangin Zainab masu yawan gaske saboda yaya A’I ta sanar da cewar suma can yinin biki ne ke jiran su, shi ne ma dalilin da aka tafi da wuri. Tana shiga gidan su Albashir aka zarce da ita sashensa mai dauke da daki da falo da kuma bandaki. Sallah kawai ta yi, wata mai make up ta fara aikinta. Ta tsantsara mata kwalliya cikin wani leshi da ina kyautata zaton bai yi kudi ba a saye shi 150k. Aka dora mata gwaggwaro mai stones da kuma mayafinsa. Idan ka ganta kamar wata bakuwar balarabiya. Bayan ta gama kintsawa sai taga kowa ya na ficewa daga dakin, aka barta ita kadai. Kamshin turarensa ta fara ji kafin ta jiyo takunsa. Shima ya bayyana cikin wani danyen voil mai tsananin kyau. Sai wani walai walai yake. A gabanta ya durkusa ya rike hannayenta duka biyu. Ido kawai ta dago ta kalle shi. Ganin yadda ya kura mata ido ya sanya taji kunya ta sauke nata. Hannayensa ya sa ya tallabo fuskarta ya kissing din goshinta. San nan yace “welcome home my Putri”. Ba ta iya magana ba sai murmushi kawai da ta aika masa. Shi ya dago ta daga zaman da tayi ya rike hannuwanta, ita kuwa ta bishi kamar rakumi da akala. A haka suka fito daga falonsa zuwa bakin verender dakin nasa. Daga kasan matattakala guda biyar da zaka taka kafin zuwa dakinsu ‘yan uwa ne damkan. Suna fitowa sai guda yiyiyiyi, kamar Gidan bikin larabawa. Inda kuwa kasan irin celebrities din na sun fito paparazzi na daukar su hoto haka aka dinga yi musu. Sun dauki kusan minti biyar tsaye a wajen, kafin Ya Maryam ta samu ta sa mutane suka basu hanyar wucewa wajen zamansu. Suna tafiya wakar shimfida fuskar ta wuce ta tabarma na tashi daga speaker DJ. Saboda haka sai yaya A’I ta hana su karasawa wajen zamansu. Nan suka tsaya suna wata rausaya mai daukar hankali, kafin kace kwabo dangi sun yanyame su ana ta ruwan kudi. Nan ma an ci an sha an raba souvenier, inda aka raba kyautar atamfar buyers batik da kuma sallaya mai laushin gaske ‘yar Turkey da hijabi dinkin Indonesia mai dauke da hijab da burmemen skirt a cikin wata jaka mai kyawun gaske. Sai goshin magariba taro ya waste. Inda kuma akai kaita wajen Umma da nata ‘yan uwa suka sa mata albarka. Tana idar da sallar isha sai gashi ya shigo da alama shima daga masallaci yake. Yana zama a bakin gadon dakin, yaya Ai tayi sallama tana mai ajiye musu kwandon abinci. Shi ta juya ta kalla tace “maza ku ci abinci, kar ku Makara saboda nine za’a fara checking in”. Bata jira amsar sa ba ta juya ta fice. Shi ya tilasta mata ta dan ci abinci ba laifi, san nan ta canza kayan jikinta zuwa atamfa super wadda ta dora hijabin da ya dace a kai. Cikin kayan da mamanta ta dinka mata ne. Shima ya canza kaya zuwa riga da wando kawai na shadda ba babbar riga. Hafsa ce tayi sallama janye da trolley tana fadin “Umma tace kuyi sauri kar ku Makara”. San na ta juya wajen yayarta tace Ya Zainab ga kayanki na gama hadawa”. “na gode budurwar kauye “ya fada yana mai karbar trolley daga hannunta. Shi ya dauki nasa da nata. Ita dai ta rataya jaka kawai ta bishi ba tare da sanin ina zai kaita ba. A haka suka shiga mota cikin rakiyar ‘yan uwa bayan sun yiwa Umma sallama suka nufi airport. [8/8, 22:16] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 28 BY HANNE ADO ABDULLAHI Tun da suka kama hanya bata yi Magana ba. Sai shine ya matso kusa da ita. Hannayenta ya kama yana wasa dasu a cikin nasa. Ta dago a kunyace ta kalle shi. Kamar zata yi Magana, sai kuma ta fasa ta saukar da kanta kasa cike da jin kunya. Kallon da yake mata shi ke dada sa ta jin nauyinsa. He pierced her with his eyes yarda tana jin kallonsa har cikin jininta. Hakan ke hanata yi masa Magana, saboda tsoron bude bakinta take yi kar ta tona wa kanta asirin zuciyarta. Ko sanda suke video call da shi, ba ta san yadda ake ta ke biyewa kalaman soyayyar da yake tsarata ba ita ma kuma ta kan dan mayar da martini. Sai call ya kare idan ta zauna ta tariyo abin da ta ringa fada sai kuma ita da kanta taji kunyar kanta. To yanzu ma shi ke hanata Magana. Kar asirin zuciya ya fito ta lebe . Shi ya katse mata tunanin da ta ke yi ta hanyar dan matsa hannunta da ke rike cikin nasa. “me amaryar Bala Mai gwanjo take tunani ne”? Ta dago ta kalle shi amman irin kallon da ya ke mata shi ya sanya ta kasa fadin abin da tayi niyya, ta saukar da kanta kasa. “Okey I get it you are wondering ina zan kaiki. Kar ki damu na tabbatar zaki ji dadin surprise din dana shirya miki”. Sai da suka shiga airport ta gane abin da zai faru. Tafiya zasu yi. Allah ya sa ba a jirgi zai dora ta ba. Ita tsoron shiga jirgi ta ke yi tun da bata taba hawa ba. Kuma ta kan ji labarai cewar wasu suna amai har da gudawa idan suka hau jirgi. Take kuwa tsoro ya bayyana a fuskarta har ya gano hakan. Yace "Putri ba dai tsoron hawa jirgi kike ba, naga yadda fusakar ki ta canza da ganin mu a airport”. “na dauka duk abin da ya zama na farko a rayuwa ka kan tsorata da shi”. Itama ta bashi amsa a sanyaye. Sai da ya dada lankwasa muryarsa san nan yace " ke nan kina tsoron aure na da ke”? “A’a sam bana tsoro because kai na au……” ta kasa karasa Kalmar da tayi niyyar fada saboda kumya. Dada rungomata jikinsa yayi cikin dariyar jin dadi yadda take kokarin nuna kaunar ta a gare shi duk da kunya kan mata handbreak. “thank you for trusting me. Haka zalika kar kiji tsoron komai in dai kina tare dani. Zan yi iyawata in tabbatar ba abin da ya gagare ki”. Take kuwa taji ta yarda da hakan sai ta sakar masa murmushi me nuna ta yarda da shi da kuma duk abin da yace. Departure lounge suka dosa. Kwarai tayi mamakin ganin yadda ma’aikatan wajen suka sanshi suke kuma yi masa gaisuwar ban girma. Wani babban ma’aikaci ne ya karaso suka gaisa san nan ya karbi passport din su yace da wani staff din wajen “maza a kammalawa KIM BASH checking dinsa”. VIP section na departure lounge din suka je ya nema musu wajen zama. Suna zama kuwa attendant din wajen yayi approaching dinsu yana tambayar me zasu sha. Sun nuna basu bukatar komai, amma ya nemi da ya sayo masa peppermint. Ba su fi minti biyar da zama ba aka kawo musu passport din su tare da boarding pass. Haka nan mai sayen peppermint shi ma ya dawo. “ga dukkan alamun kai sananne ne a wajen nan”? “in ban da neman aurenki ba abin da ya taba ajiye ni a kasar nan for more than a month ban yi tafiya ba”. Da alamun damuwa wadda ke nuna bata kaunar rabuwa da shi haka zalika ba ta san sanda bakinta ya yi subutar fadar “Ke nan yanzu haka zaka ci gaba da tafiye tafiyen”? “kwarai kuwa but with you by my side, gorgeous”. A nan kuma taji sanarwa ta loud speaker. Ba dai san ta meye ba, amma taga ya mike tare da dago ta daga inda take zaune. A cikin jirgin ma a VIP suka zauna. Har da wani dan labule da ya raba cabin din su da na wasu, san nan ga kujeru idan kaso ka kwantar da su kamar gado. Shi ya daura mata seat belt dinta bayan sun zauna. Sai da aka fara sanarwa a cikin jirgin ta gane ashe jirgin Saudi air suka shiga zuwa kasa mai tsarki. Murna ce ta kamata. Idan bata manta ba, yau 24 ga watan dhulkida. Hakan ya sa ta gane zata samu damar sauke aikin hajji. Da su Farida sukayi candy daddy ya kai su. Aka ce ba za a je da ita ba, saboda bata ci jarrabawa ba. Haka nan da auren su anti Sakina sun sake zuwa har da su Sakinan nan ma ba a je da ita ba akan ba wanda zai kula da su Halim. Shi kansa ya lura da farin cikin da take cike. Shi ma kuma yaji dadi matuka. Balle da ya tuna maganar yayyensa inda suke tsokanrsa da cewar wa yake zuwa macca honey moon. Hannunsa ya sanya
Chapter 30 · 0% Book details