Sashe 41
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
amsa. A falo ta tarar da Dadi ya fadi. Duk jikinsa ya baci abin ba kyan gani. A guje ta fita ta kirawo driver ta shi ya taimaka mata suka daga shi. Sai da ya gyara masa jiki tukun na san nan suka dauke shi zuwa asibiti. Sai da tazo fita ita a zaton ta ba kowa a gidan, sai ga Hanif ya fito daga dakinsu wanda ke nuna tashin sa ke nan daga bacci. Kuma tabbas ko sallar asuba bai yi ba. “me ya hana ka zuwa makaranat?” Yana soshe soshe yace ‘Makara mukayi”. Har za ta sake Magana sai ta tuna da halin da Dadi yake ciki. Ba tayi masa Magana ba ta shiga mota kawai suka wuce asibiti. Tana fita ya dauki waya ya kira Momi yana gaya mata cewar Zainab ta zo ta dauke Dadi. Da kuwa ta buga mata waya a lokacin sun isa asibitin ana kokarin ba shi taimakon gaggawa. Tana ganin wayarta da hanzari ta amsa da sallama, saboda damaa kokarin kiran ta ta ke yi. Ai kuwa bata amsa sallamar ta ta ba sai zagi da masifa. Tana kokarin yi mata bayani ba ma ta tsaya ta saurare ta sai bakaken maganganu take ta lafta mata, har tana ce mata duk tsiyar ta bata isa ta aure shi ba, da take wani kaffa kaffa da shi. Uwarta ce kuma ita da Dadi har abada. Sai da ta gama bala’in ta sannan Zaainab ta kashe wayar. Ita da ta juya ta ga yadda Dadin ya zama taushe duk ciwo ya tsufar da shi sai abin ya bata dariya. Balle da ta tuno yadda Abbn Garrko yake kula da umma ga rayuwarsu cike da kwanciyar hankali. Sai ta dada tabbatar wa kanta ko zabi aka bawa Umma tabbas ba zata zabi Dadi ba. An samu ya farfado. Ita tana tsoron ma ko wani stroke din ya dada samu, sai akayi sa’a sugar sa ne yayi kasa, saboda rashin abinci. Daga baya ma da Albashir yazo suka yanke shawarar fita dashi, zuwa waje. Ba ta gaya wa kowa cin mutuncin da Momi tayi mata ba ta hada musu zuwa India. Duk abin da ta san zasu bukata sai da ta bawa momin kudin nan. Sun so hada su da Farida su tafi tare amma yanayin aikin ta ya hana. Amma abin haushi bayan sati daya da suka je ganinsa ita da Albashir, suka tarar duk test din da ya kamaata ayi masa ba a yi ba, saboda rashin kudi inji Dr. Ita kuwa tun da tazo ta kawo shi asibiti ta shiga ta biya abin da bai takakara ya karya ba sai ta shiga kasuwa da sauran kudin. Ta kuma nuna masa ita fa dama da zasu taho ba wani abin kirki Zainab ta bata ba. Yana ganin Zainab da Albashir sai kawai kuka ya kwace masa. Su sun dauka ma wani ciwon akace yana da shi. Zainab ma sai kuka. Albashir ne yace “don Allah dadi kayi hakuri koma menene Allah zai kawo mana shi da sauki”. “haba Albashir da girma na zan yiwa ciwo kuka? murnar ganinku kawai nake yi.zainab matso kinji share hawayen da kike zubarwa”. “sannu dadi Allah ya baka lafiya”. Zainab ta amsa masa. Bayan nan ta shiga tambayar sa abin da likita yace da kuma abin da akayi masa a sibiti. Bai san komai ba, saboda haka tare suka shiga wajen likita ita da mijinta. Sunyi mamakin amsar da likitan ya gaya musu na cewar kusan ba abin da a kayi masa saboda rashin kudi. Sun yi mamaki kwarai da gaske, saboda sun san cewa sun bawa Momi dala dubu talatin amma kuma ace ba kudi. Albashir bai tsaya dogon bincike ba, ya bada umarni a ci gaba da duk abin da ya kamata na nemawa Dadi lafiya. Hatta daki sai da suka canza masa. aka mai da shi VIP na asibitin. Momi kuwa ba su suka hadu da ita ba, sai da suka kwana suka yini. A nan suka kwana a adjacent room da ke dakin. Lokacin da taje dakin da ta yasar da mijinta, aka shaida mata cewar an canza masa dakin. Tana shiga ta ga Albashir da Zainab, sai ta fara buyagin karya. Tana fadin “ai sai ka gaya min mowar ‘ya’ya ce ta zo shi yasa ka banzantar da ni. Dadin abin dai sai dai kudin amma jahilci yayi katutu”. Har Albashir zai yi mganaa sai Zainab ta rike hannunsa, su na hada ido ta girgiza masa kai. Fita kawai suka yi suka barta a dakin. Haka kuwa akayi wan nan zaman asibiti, kullum suka je sai ta nemi maganar da zata yaba musu. Su kuwa ba sa kulata. Sun tabbatar da Dadi ya samu kulawar da ta dace. Ita kuma ta lodi sarin kaya. Suna dawowa ta takura sai da Zainab ta kaita gidan malamin da aka tsare Khalifa. Shi ma kuwa tana zuwa da danta ta dawo. Ba a dade ba kayan da ta auno daga Indiya suka zo. Wanda bata mori komai ba, saboda kaya dai sun iso har Nigeria, amma ana debo su daga warehouse, motar data dauko kayan ta kama da wuta kurmus komai ya kone. Tana tsaka da wan nan bakin cikin ta dawo gida ta tarar da Khalifa wanda ya dan samu aka sako shi daga gidan Mallam, ya hada party a gidan saboda Dadi ba ya nan ya je Kera. Ba kuwa wanda ya san ya akayi abokansa tas suka kwashe gold din da Momi ta kwashi sama da shekaru ashirin tana Tarawa. Saboda ita a al’adarta bata sayar da gold, sai dai in taga wani ya bata sha’awa ta saya ta kara. To kuwa tas suk shiga suka kwashe su. Ranar da ta nemi kayan ta rasa ta kuma gane sacewa a kayi ga shi an nemi Khalifan an rasa, sumewa tayi da kyar aka samo kanta. Ta gama da jinyar wan nan wanda ta dau tsayin sati tana jinya, sai ga labari yazo mata na cewa Farisa sun kwashi tsiya da mijin bana har ya karya ta a hannu. Tana masifa ta tafi da niyyar yau dai kam kashe auren zatayi ta dawo da ita gida saboda ta gaji da wan nan masifaffen aure. Uwar Salim ta kada bakitace “nima na gaji da shari’a. da kin dauke marar kunyar ‘yarki da kowa ya huta”. “’Yata marar kunya ko danki masifaffe azzalumi. Kullum ya sha kwayarsa ya bugu ya zo ya kama yarinya da duka”. “shaye shayen ai dan kowa yana yi. Sai dai shi da kudinsa yake yi baya satar na kowa. Ke kuwa bayan dan shaye shaye ai har da barawo kika Haifa”. Momi ta harzuka ta daga hannu da niyyar kaiwa maman Salim mari, da kyar nurse ta shiga tsakanin. A harzuke ta karasa dakin da aka kwantar da Farisa. Abin haushi a jikin mijinta ta same ta rungume tana shagawabwa. Shi kuma yana kokarin feeding ita abinci. “Tashi aure ke da shi na kare shi daga yau. Kotu zan shigar da kara ya baki takardarki”. A yatsune ta dago ta kalleta tace “momi wacce irin takarda kike Magana akai”? “takardar sakin auren ki dole ne ki rabu da wan nan kallagaggen auren”. “Rabuwa Momi? Dama nace miki nayi aure don in rabu da mijina ne? kin ga don Allah Momi ki barni in yi rayuwata. So kike nima in koma yadda Anti Sakina ta koma. Kin zugata ta rabu da mijinta na farko, ga shi nan yanzu aurenta biyar. Kullum kuma dada ci baya take. Daga bungalow ta dawo face me I face you. To ni ban shirya rabuwa da mijin ba. We have our fights and we make up. So meye problem dinki. Ga Farida nan ko mijin ta rasa ni kuma da na samu kina neman rabani da shi. Please Momi let me be. Kije kiji da problems dinki ni ban shirya rabuwa da mijina ba. Kuma ban neman advice dinki ba”. Duk kuma maganr da ta ke tana rungume jikin mijinta, shi kuma sai shafa ta yake yi ko kunyar surukarsa baya ji. Daga bakin kofa taji dariyar maman salim tana fadin “to kin dai ji amsar ki a wajen ‘yarki saboda haka fice ki bamu waje. Sakarya uwa mai neman kasha auren ‘yarta”. Haka ta baro asibitin cikin bakin ciki. Duk da kuntatawar da tayi wa Zainab bata taba maida mata Magana ba amma ga ‘yar cikin ta nan tana caccaba mata a gaban Surakarta da kuma surukinta. Ta dawo kuma ta tarar da Sakina itama ta debo nata bakin cikin. Auren kisan wuta tayi da driver gidan da tayi aure wani Alhaji mai kudi. Karamar rigima ya dankara mata saki uku. Akan tana son komawa ta lallabi driver akan suyi auren sakin wuta. To an yi aure na sati uku amma sama da wata uku yaki saki. Kuma ga shi da kokari har gida ya kama mata haya ciki da falo da kuma falle guda nasa a nan cikin limawa, ya kuma yi mata iznin tahowa da ‘ya’yanta guda biyar akan zai taya ta rike su. Matsalar sa muni kamar a yankar wukar. Idan ta kalle shi har gabanta faduwa yake. Ta nemi saki yace bai san zance ba. Ta kai shi kara ta rasa hujjojin da zata bayar na ya sake ta. Kotu kuwa ta bashi aure. To yauma wan nan bakin cikin tazo take zayyanawa Momi. Ita kam tama rasa yadda zata yi da rayuwarta. Ga Khalifa an neme shin an rasa ga kuma auren ‘yan gata yanda ya kasance. Bilkisu kuwa tayi musu ta ‘yan duniya. Ba ruwanta da kula kowa. Dama ba cikin su daya da momi ba. Ta wurgar da su ta rungumi uwarta da ‘kannenta ‘yan dakinsu. Ganin bakin ciki da talauci zai daureta ta tattara ta koma Abuja inda ta samu sabon aiki. Nan kuwa Boss dinta ya dinga sakata tana tabargaza da kudin gwamanati. Haka rayuwa taci gab da Garawa. Zainab ita tasa aka nemo mata Khalifa. Ta sake mai da shi gidan kangarrarun yara. Sai da kuwa ya shekara ya fito ya warke tas kansa ciki da Qur’ani. Nan ta nuna masa son ya koma makaranata. Shi kuma ya nuna yafi kaunar ya tafi Saudiyya ya karanta Islamic studies. Jin wan nan zance Momi ranta ya baci ta