← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 43

Sashe 28

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 3 min read

sai an zo wani waje. Da sun yi Magana da ko a nan unguwarsu an dauka. Amma sabanin yadda tayi tunanin wannan hoton daban ne, saboda har su yatsun hannu aka dinga daukar hotonsu. Bayan an gama sun fita sun shiga mota Mujib yace “ango har yanzu baka sanar da ni inda zan kaiku ba. Kaga dai auren da muka taru domin sa kayi hijacking, tun da dai ni da kai ba za mu iya attending ba”. “You know what, da nayi niyyar mu wuce gida, but on second thought why should I deny may deer and her mother the right to enjoy and cherish this moment. So I think mu wuce Garko kawai’”. “kaga idan kai da Zainab murnar angwancewa ta sa kun mance komai. Ni yunwa nake ji, saboda haka kafin mu wuce find me some thing to eat please”. A wani haddaden restaurant suka tsaya. Nan fa ya sha daga da Zainab akan taci abinci amma ganin sa da kuma idon Mujib ya sa ta kasa ci. Ya juya ya kalli Mujib yace “please dan bamu privacy mana”.” "yanzu kuwa” ya fada yana mai mikewa domin kuwa shi dama ya gama . Yana fita ya jawo kujerarsa daf da tata wadda har kafadarsu tana gogar juna. Ya debo abinci a spoon yace “Ha’ ta so ta noke,amma bai bata damar yin haka ba, sai dai ma threat din dura da yayi mata. Sai da ya tabbatar ta ci yadda ya kamata san nan ya kyaleta. Kuma har ya tabbatar ta koshi bai daina bata da hannunsa ba. Ita kam kunya ce ta lullube ta na ganin wani Balan da bata san da shi ba. Suna shiga mota taga sun dauki hanyar Maiduguri. Da sauri ta kale shi tace “ba gida zaka mai da ni ba”. “a’a garko zan kai ki wajen umman Hafsa”. “Wai gashi ban taho da kaya ko daya ba. Da zaka yi hakuri kayana da na dinka suna gidan su Hafsa da naje na dauko”. Wani irin kallo ya watsa mata. San na yce “saboda ni kuma bani da wayo. In koma filin dagar yakin da na sha da kyar. Yau dai kiyi managing da na Hafsa, gobe in sha Allahu zan kawo miki. Haka nan suna hirar su cikin annashuwa suka isa gidan mallam Usman. Nan kuwa suka shaida masa akan cewa kawo Zainab suka yi wajen mahaifiyarta ta yi mata irin bikin da ta ke so. Kwarai daga shi har hajiya Khadija sun ji dadin abin da suka yi musu. Nan dai suka yi sallama suka juya saboda suna son halartar bikin da dama shi suka taru domin sa. Washe gari kuwa sai gashi da kayanta da Fatu da Kuma Mama Hajjo wacce ta hado kayan gyaran jiki rankatakaf da turarurruka masu kamshi domin gyaran amarya. Anan kuma mallam Usman ya sanar da shi shawarar da suka yanke ta kai biki kera. A gida kuwa Momi kamar wata zautacciya ta koma saboda tsabar bakin ciki. Balle data gano waye mijin asalinsa da matsayinsa sai da taji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. Su dai masu aure sun samu an zarga musu shi ita kuwa mai bakin ciki sun barta da abinta.
Chapter 28 · 0% Book details