Sashe 43
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
karamin kunya zata sha ba na mitar da mijinta ke yi. Sa’ad kuwa ya taimaka matuka, saboda a ranar aka gama case din Momi. Tana fitowa daga inda aka tsareta taga Zainab, har kasa ta durkusa tana yi musu godiya ita da Albashir. Zainab ta dago ta rungunme ta a jikinta tana bata hakuri. Abin mamaki wai yau ita Momi ke shiwa albarka. An gama case. Sai dai kuma an sauke ta daga aiki. Tare suka juyo zuwa kano washegari. Dadi kuma yayi tsallen arziki yace ba gidansa ba. Ba irin rokon da ba su yi masa ba yace shi kam ba zai maida ita ba. Akwai wasu kananan gidaje da Albashir kan gina masu dauke da dakuna uku a jere sai falon a karshen dakin farko da kuma kitchen da tsakar gida suna kallon dakunan daura da falon ke nan. Sai kuma daga karshen dakunan akwai dakin waje da toilet dinsa da kuma shago dan madaidaici. Ko wacce shekara ya kan gina irinsu guda goma ya bayar sadaka. Zainab ta bude daya tasa aka wanke shi. Take ta sayo kayan gida har da su Ac aka gyara gidan sosai. Ba ita ta gama ba sai kusan magariba. A ranar momi ta tare a sabon gidan da Zainab ta bata. “Eh haka kawai saboda mutum yaga ba a iya fushi da shi sai ya dinga min hawa kawara. To bulukutu maragatan” Ita dariya ma mitar ta Albashir take bata sai kace Ammace take fada da Amir. Jawo shi tayi jikinta sai da ya samu daidaita natsuwarsa ya fara manta a ina yake san nan tace “kayi hakuri. Ba zan iya ganin Farida cikin tashin hankali in kyale ta ba. Momi kuma ai uwace a wajena”. Cike da shauki yace “tsokanarki nake yi Putri. Kin san I can do koma meye for you”. “Alhamdu lillah. Yanzu sauran ka abu daya. Yadda ka sama wa su Hafsa mazan aure nagartattu ka taimaka Ita ma Farida ka samu wani mai hankali cikin jama’arka ka hada ta da shi”. “kai Putri akwai ki da naci. Kusan shekaru takwas ke nan kullum sai kin yi min maganra in aurar da farida. Yaya ki ke son in yi. In lokacin auren ta yazo ai za ta yi ne”. To Momi dai daga babbar ma’aikaciya ta dawo zaman shago. Dan provision Farida ta zuba mata take sayarwa tana dan samun na batarwa. Duk da dai Zainab bata barta haka ba. Yadda ta sauke a gidan mahaifin ta haka take saukewa a gidan Momi. Amma yau da gobe sai Allah. Sai daga baya Farida ta samu auren wani nurse in charge ne a asibitin su . Yana da kirki sai dai matarsa da uwarsa ba bayani. Masifaffu ne na nuna wa sa’a. da sun yi zai barta ta kama gidan ta, amma daga baya matar ta zuge uwar tace mata “inna idan kika barsu suka kama gida su kadai dadi zasuje suna ci mu su bar mu a anan tun da ance babbar likita ce tana da kudi. Ki sa shi ya kawo ta nan ayi komai akan idonmu”. Haka kuwa akayi. Daki ciki da falo aka bata a gidan sa. Duk tarin da momi tayi na auren ta ya tashi a banza. Momi taso taki auren ita kuwa she is being practical tace “mh mh Momi kyale ni iam not getting any younger. Iam almost thirty”. Haka ta lallaba tayi auren da take ganin zai zamo mata rufin asiri, sai dai fa abin da kamar wuya. Ba a raba tunuya ba. Haka dole take cefane na mutum goma sha biyar. Inna da kanne mijinta hudu. Mariya da ‘ya’yanta bakwwai. Ga kuma bazawarar kanwarsa da ‘yarta duk a gida daya. Ba wani cikakken privacy a gidan. Duk wanda yaji ko da sartse ne ita zata kai shi asibiti ta kuma sayo magani. Cefanen gidan ita ce. Shi nasa albashin sai Innar ta karbe ta bawa useless kannensa. Dama shi kadai ne responsible a gidan. Ga ‘yar banzar rashin kunya da suke labta mata. Ga sata. Yanzu haka ta hakura da sayen waya mai tsada ta koma nokia mai torch light. Saboda in dai ta saya yau gobe kuwa zata neme ta ta rasa. Ba kuma ta isa tayi cigiya ba. Saboda ko ganin ta tayi a gidan za ace ai ba ita kadai nasara yayi wa wayar ba. A haka ta haifi diyarta mai sunan Momi. Lokacin da ta tashi zata saka ta anursery aka ce sam ba za a raba musu makaranta da sauran yayyen ta ba. Saboda tana son Iman ta samu karatu mai kyau, haka ta hakura ta dau responsibility yaran takwas ta hada da tata tara. She works for like sixteen hours daily just to meet her financial abligations. Ko motar hawa ta kasa saya. Duk ta tsofe kamar ba ita ba. Ranar da Zainab ta haifi ‘yarta ta hudu Khadija, taje mata barka. Haka ta tantsa yaran nan a adaidaita sahu, saboda ta dauko su daga makaranta ke nan, don ta san idan ta koma gida ba zata samu fitowa ba. Zainab na zaune a falo ta ga yara sai fitowa suke daga adaidaita. Sai da mutum goma suka fito daga cikinsa. Take hankalinta ya tashi na ganin kanwarta ce cikin wan nan situation din. Sai da sukaci abincin dare san nan suka tashi tafiya. Ta fito raka ta driver zai ajiye ta agida, sai kawai ta tuna da sienna LE2004 dake zaune a gidan wai saboda ko da za aiki driver. Bata san sanda ta shiga daki ta dauko key ba. Har sun gama duruwa cikin motar ta range rover tace wa “Farida sauko ungo wan nan ai dai zata kai ki point A to B. cike da murna ta shiga gida da sabuwar motar da yayarta ta bata. Washe gari har da maigidan aka fito ana ta murnar samun sabuwar mota. Aka lalauba babu mota babu dalilinta. Ana kakabin an sace sai ga waya daga police station yazo an kama kannesa sun buge wani mutum da mota. Haka mijin Farida ya nufi police station din. Ashe wai ta window dakinta suka shiga tana wanka suka dauke key din da daddare. Yayi belinsu Farida ta tsaya kan medical treatment din wanda suka buge. Daga ya dawo gida yana musu fada, kishiyar farida Mariya tace tana jin san da Faridan ta zuga shi. Nan kuwa suka tarar mata. Duk da kokarin da yayi na hansu sai da sukayi mata ligif da jikinta san nan suka kyaleta. Shi ya kaita asibiti yana bata hakuri kamar yadda yake mata ko da yaushe. Shi ai yana sonta. Family shi ne wasu bunch of hooligansa. Zainab da danyen jego ta je ta ga yadda kanwarta ta koma saboda dukan dangin miji. Ba yadda bata yi da Dadi ba yace ai shi ya fitar da hannunsa akan Rumaisa da ‘ya’yanta. Da kyar ta samu ta lallaba shi. Tare suka je gidan mijin su Farida. Nan kuwa tadage takardar kanwarta za a bata, ko kuma a raba musu gida. Shi dai kabiru yana son zama da matarsa, saboda haka ya samu ya lallaba uwarsa akan cewa idan suka bar farida ta bar gidan yara sun daina zuwa makaranatar kudi saboda ita take biya, haka kuma dan dadin da suke ci da kuma ‘yar sutura mai kyau duk zata gagare su saboda ita ke tallafawa. Da wan nan ya samu ya dora ta ta yarda akan Farida ta koma gidanta, amma sai tayi alkawarin zata ci gaba da dawainiyar yara ta makaranta. A nan unguwar Zainab ta samu dan gida madaidaici ta saya mata. Aka kuma yi mata iyaka da kannen mijin. In dai suna son ganinsa sai dai su kira shia a waya, amma ban da shiga gidan Farida. A haka ta samu ta kwato mata ‘yancin ta. Ta kuma ci gaba da tallafa mata, saboda albashinta ba zai dauki nauyin dake kanta ba. Ga Sakina da yaranta biyar ga tata ga na mijinta guda bakwai da kuma ‘yar kanwarsa duk ita ke biyan school fees dinsu. Tayi aikin gwamnati tayi private duk don ta rufwa kanta asiri. Yau shekarar Zainab da Albashir goma cif da aure. Ba tare da saninta ba ya shirya mata hadaddiyar dinner. Ya sa ta shirya ita da ‘yanmatan ta cikin wani hadaddaen lace yayin da shi da Amir suka hade a shadda suma anko babbar riga. Sai da ta zauna a matsayin guest san nan ta fuskanci ita ce host na taron. Ba abin da ya dada birgeta irin yadda Albashir ya dada tababatar mata da soyayarrsa a gaban mutane. Allah yasa ma su yasu ne kawai matasa. Wakar da aka musu ta shimfidar fuska ranar bikin aurensu, ya zauna yayi miming da kansa ya rera mata a cikin bainar jama’a. Ai kuwa bata san sanda ta shiga fili ta dinga falle ‘yan dubu dubu tana lika masa ba. Shi kuma ya riko hannunta yana taka rawa da ita a hankali. Nan kuma sauran abokansu suka kewaye su ana ta zuba masa kudi. Mujib ne yayi jawabin godiya inda yake cewa “lokacin da muka je neman auren a’yan gwanjo muka je. Yau kuma mun koma mawaka after ten years. Ban sani ba nan da wata ten years idan har muna raye ban san wacce sana’a zamu fara ba. Amma dai kam iam sure of one thing. The circumstances might change but the love of Albashir and Zainab will remain where it was yesterday”. ALHAMDU LILLAH