Sashe 21
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
[8/7, 21:33] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 21 BY HANNE ADO ABDULLAHI Haushi bai kara kama Al Bashir ba sai da ya ga irin garar abincin da Zainab ke shirya mishi. Abin da ya faru, wata rana ne ya je wajenta suna hira. Ta lura da hamma da yake ta dokawa. ta kalle shi ta ce “kamar kana jin yunwa”? “wallahi kuwa” ya amsa mata. San nan ya ci gaba da cewa “kin san sana’ar tamu. Yau da ciniki gobe sai godiyar Allah. So nake ma in fara daukar dealer tawa ta kaina, in daina tsinta, saboda yin haka yafi riba. Hmmm” wata hammar ta sake katse shi. “ina zuwa “ kawai tace da shi. Ta juya ta shiga gida. Dama ta dan tsinto kayan abinci da ribar cinikin da ta ke yi. Tana shiga cikin sauri ta dafa masa jollof din taliya wadda ta wadata da busasshen kifi da kuma alabasa. Sai da ta dakko dahuwa, san nan ta nika dan attarugu ta da sweet pepper ta zuba a ciki. Ta kara kayan kamshi kadan ta rage wuta ta barta ta karasa a hankali. Ta yanka gwanda kanana, ta hado ta doro komai a tray. Nan dai bakin vereander Mallam inda suka saba zama ta kai masa. Tana bude flask din wani daddadan kamshi ya bugi hancinsa. Sai da ya shaki kamshin abincin nan san nan ya hadiye yawu. Nan kuwa ta zauna tana zuba masa yana ci tana dada wata daga gefen plate din domin tayi sanyi. Kafin ya gama da ta gabansa ta sake tura masa wadda ta fifita masa. Yaci abincin nan sosai. Sai da ya gama ta zuba masa ruwa ya sha. Ta tura masa plate din gwanda, yana sha sannan tace “kuma dealer da kake son dauka da tsada”? “Kai tsadar ma. Tana kaiwa dubu saba’in zuwa da biyar”. “idan nayi wani abu kayi alkawarin ba za kayi min musu ba” “come on don’t trick me ki sani yin abin da yafi karfina”. “Allah nayi alkawarin ba zai fi karfin kaba”. “To shi ke nan nayi”? Kudi ta ciro daga cikin hijabinta kashi kashi. Tace “taya ni kirga wan nan”. Ya dinga ware su yana hadawa. Sai da ya gama hada su tsaf san nan ya kirga. Dubu dari da sittin da shida da dari biyar ya samu. Ya gaya mata san nan ya mika mata. “barsu dai a wajenka. Lissafi zamuyi. Bani twenty daga ciki”. Ya kirga ya mika mata. San nan ta sake cewa. “ka sake ware min sha biyar din ka bani”. Ya sake yin yadda tace. Yana bata yana fadin “lallai hajiyata ashe kudi gareki haka. Shine baki aika an kawo miki security ba”? “meye security”. “sorry tsaro nake nufi. Ko da yake kina da masu tayaki zama a gida saboda haka ba wani tsoro ma da zaki ji. “Ka manta ne amma tun farko na sanar maka ni bana jin tsoron zama ni kadai. Na saba zama ni kadai a gidan nan, ba tare da kowa ba”. Da hanazari ya maida kallonsa wajenta. “ban gane kin saba zama ke kadai ba. Kina nufin da su Momi suka yi tafiya ba wanda ya zo tayaki zama? Da ki ka gaya min hakada farko na dauka tsokanata ki ke yi, ko kuma za a turo masu tayaki zama daga baya". Ba tare da nuna damuwa ba tace “Mh mh ni kadai ce”. Sai da ya daga ido ya kalli gidan san nan yace “yanzu duk girman gidan nan ke kadai ce, ba kowa a cikinsa”? “lah to meye ai na saba. In dai nayi addu’a ba tsoron da nake ji” Muryarsa can kasa yayi zagin da bai san sanda ya kubuce ya fito daga bakinsa ba. “bloody awful people” ya furta. “Sorry Magana kake ban ji me kake cewa ba”. Nan da nan ya waske yace “mh mh ina mamaki ne kawai saboda ni har yanzu na kasa rabuwa da mamana. Ga dakina ga nata. In fita kofar gida ma na kasa, saboda tsoro”. Dariya tayi tace “wan nan kuma ba tsoro bane shakuwa ce”. “eh amma ni kin yi min laifi. Tun da nake zuwa baki taba bani ummanmu a waya mun gaisa ba”. Nan da nan yanayin ta ya canza alamun damuwa kadan ya bayyana a fuskarta. Ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun ta. Tace “kayi hakuri nima bani da numberta shi yasa”. “yaya zaki ce baki da number mahaifiyarki”? “eh to dalilin ne ya faru. Rabona da ita na kai ten years. Ba ita ba rabona da inje Kera ma haka”. Wani irin tausayinta ne ya tsirga masa. Nan ya dinga bugar cikinta cikin wayo har ta sanar da shi inda kakanninta da kuma Umman ta suke. Sai da ya gama digesting wan nan information din san nan yace “kin barni da tulin kudi a hannu baki ce min komai ba”. Ba ta ce komai ba sai da tattare kwanukan da ya ci abinci. Ta mike da niyyar shiga gida, san na tace “ashirin ta ishe ni biyan kudin sauka. Sauran kuma sun ishe ni in saro kayan snacks dina. Saboda haka kayi amfani da sauran ka dauko mana dealer da kake Magana akai. Amma please ka ware dubu daya da dari biyar na kai, kayi mana sadaka saboda samun sa’a”. “A’ a ba za ayi haka ba”. “gaba kawai yai abinta tana fadin “kace ina gai da Umma da su Yaya Ai”. Bata bashi damar amsa komai ba tayi shigewarta gida. Tun daga wan ana rana kuwa ta daukarwa kanta ciyar da shi da safe da kuma yamma da yake zuwa wajenta. Kullum kuwa ya zauna ta kwashi dariyar santi. Ya gwada kawo mata dan cefane wai ya tallafa mata. Kaji hudu ya saya ya kawo mata. Yadda ya kawo su haka ta gashe masa su ta saka a foil ta ba shi. Sai da ta zo raka shi yaga ta saka leda a kwandon gaban babur din. Kafin ya tambayeta meye ta shiga gida. Sai da ya isa gida ya tarar da yayyensa biyu da kuma ummansa da kuma kanneta maza guda biyu. Ya shiga da kullin a tunaninsa ma ko snacks ta zuba masa. Amma ana budewa wani kamshi ya doke su dukkansu. Nan kuwa suka dinga ci suna santi. Uncle Sani har da tambayar ina ya sayo shi ma ya bi ya sai ma iyalinsa. Ya ce masa bashi akayi. Ba tare da saninta ba yayi kokari ya nemi inda mahaifiyarta take aure a garko. Yana tsammanin yaga gidan talakawa. Yayi mamakin ganin irin arzikin mijin mahaifiyarta ta. Gida ne bulo da bulo. Ga rufin kwanon jinin talaka an shimfida shi. Da ya shiga cikin gidan kuwa ko ina marbles ne a shimfide banda wajen harabar gidan da ya sha interlocks. Mallam Usman yayi murnar ganinsu matuka. Su hudu su ka je shi da abokansa. Duk da a Bala mai gwanjo da kuma abokansa suka je ya mutunta su kwarai da gaske. Babban falonsa ya sauke su yana ta murna diyarsa ta samu miji. Nan kuma masu aikin gidan suka shiga hidimar kawo entertainment. Ba a san da zuwansu ba, amma hidimar kabakin abincin da aka sauke su da shi sai kace wadanda suka halarci hadaddaen party. Sai da su kan dan huta san nan akayi musu sallama da Maman Khadija domin su gaisa. Da ganin kyakkyawar suturar dake jikinta da kuma yanayinta ka san matar da ake so ce kuma ake kula da ita. Babu alamun hustling a tare da ita. Duk da dai cikin hijabi tazo amma hakan bai hana su ganin kyawunta da kuma tsananin kamar da suka yi da Zainab ba. Tana fita kuwa Sa’ad yace “Allah ya sani wan nan mata tana da kyau mai tsanani”. Dariya suka saka. Mujib tace “bari mai gidan yaji kana yaba matarsa. Kaga sai kasa muyi asarar wadda muka zo nema. Mukoma da kai an yi mana rotse”. Sai da ya daidaici sun gama san nan ya dawo falon. Sabanin mahaifin Zainab, shi kam MallamUsman ya tsaya tambayar yar kure na son sanin asalinsu da kuma sana’ar su. Har Mustafa ya fara bayanin gwanjo, Mujib ya dakatar da shi da fadin “Mallam kayi hakuri cikar kamalarka ba zata bari muyi maka karya ba. Mun boye asalin mu da kuma sana’ar mu saboda da farko da muka nuna kanmu a zahiri an so hana mu Zainab, amma da muka dan yi basaja sai kuma muka samu sa’a." Nanya zauna ya gaya masa asalin ko su su waye. Kusan duk wanda ke nahiyar Kano ya san sunan mahaifin ALBashir. Take Mallam Usman yace “kai kanin Aisha Usman ne”? “mallam ashe ka san yaya Ai”? ya amsa a cikin ladabi. “kwarai na santa mun yi BUK tare. Duk da dai ba fannin mu daya ba. Amma harkar student union ta sa muka san juna sosai. Kuma maigidanta abokin wani yayana ne. domin shi ko kwanaki da sukaje Ummara mun hadu dasu”. Take murna ta kamasu na ganin akwai sanayya a tsakaninsu. Ya kuma gamsu da nasabar su duk da dai bai san halayyar yaron ba. Amma yaji dadin ganin akwai ta inda zai bincikin halayyar yaron. Duk da ya san bada aure ko hanawa ba nashi bane, amma hakan bai hana shi binceken ba. Kannenta ne suka shigo da driver wanda ya kai su kano sukayo shopping din su a Shoprite. Sun yi murna kwarai da bakin da suka gani. Nan kuma hira ta koma sabuwa da kannen nata. Ganin wanda zai aureta ya sanya sukaji kamar ita suka gani. Saboda in ban da Hafasa da kuma kaninta mai binta Faruk sauran duk ba za su iya shaida ta ba. Sai dai labarinta da suke ji a wajen Abbansu. Su Albashir sun yi mamakin ganin yadda kannen nata suke wayayyu. Kamar ba girman kauye ba. Ga kanwarta hafsa da ya tambayeta inda take karatu ta sanar da shi ta gama Turkish. Yanzu NTI university zata. Da ta dauko wayarta kuwa domin karbar number Zainab yayi mamakin ganin IPhone ce a hannunta. Kannenta ma guda hudu duk a nan suke boarding section dinsu. Shi kuwa mallam Usman yayi mamakin irin arzikin da ya same shi da shi. Motar hawa ma TACOMA 2014 yake hawa, yayin da ummanta