← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 43

Sashe 18

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kyar ya daure ya bata dubu goman da ya dauko ba, saboda ko driversa ya kan bashi haka a kyauta kawai,balle ita da yake jin zai iya mallaka mata duk abin daya mallaka a rayuwarsa, [8/6, 23:26] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 20 BY HANNE ADO ABDULLAHI Kusan kullum sai AlBashir ya kaiwa Zainab ziyara da safe kafin yaje office. Wahalar mashin dai yana fama da ita, amma sam ko ajikinsa. Idan Mujib yayi masa tsiya sai yace masa “muna bata lokaci ne kawai zuwa gym, but this is a better exrcise”. Shi dai Mujib tun zuwan su na farko sau daya ya kara rakiyar zance, saboda ya koma portharcourt in da yake aiki a kamfanin SHELL. Shi kuwa kullum sai ya kai ziyara gidansu saboda haka fahimtar juna na dada wanzuwa a tsakaninsu. Ya kuma fi son zuwa wajenta da safen saboda ya lura ba a interrupting dinsu sabanin zuwan yamma da kuma na dare, da bata minti biyar a tare da shi wani bai zo yakirata ba. Haka suke hirar a tsintsinke, har dai ya hakura ya tafi. Amma yau da yazo da safe lokacin da ya saba sai ya ganta tare da su Momi da duk sauran yaran gidan ana ta loda kaya a mota. Guri daya ya samu ya labe ya kuma yi sa’a ba wanda ya lura da shi. Tas suka loda kaya cike da but, mota biyu. Daddy da Momi a daya, yayin da yaran gidan suka shiga Venza. Gaba daya suka tafi. Shi har ya tsorata ya dauka ko tafiya suka yi zuwa wani gari, Zainab bata shaida masa ba. Amma Mallam na kokarin kulle gate sai ya hango ta cikin uniform dinta. Wani irin farin ciki yaji ya lullube shi. Domin kuwa ya san da tayi tafiya, zai yi kewarta ba kadan ba. Tana kokarin shiga gida sai muryarsa suna gaisawa da mallam ta tsai da ita. Shi ma kuwa da hanzari ya karaso in da take, ya bar mallam na kokarin kullo gate din. “ai yau hawan jini ya kusa kamani”. “don Allah yayi hakuri kar ya kamaka, ko don ya tausawa min”. “Ashe har kina tsorona da ciwo, amma ni ban kai ga gane hakan ba. Kin barni sai rara gefe na ke yi”. “Hm kai baka da dama”. Ta durkusa sosai tare da fadin “barka da safiya”. Ba karamin nishadi yake ji idan tayi masa irin wan nan gaisuwar ba. Sai yaji shi kamar wani basarake. “Barka kadai” shi ma ya amsa mata. Ya karasa ya zauna a wajen da ya saba zama. Itama ta karaso ta zauna a gefensa. “Mu dawo maganar dazu. Ki na tsorona da hawan jini, amma ba kya kareni daga shi”. “Gaya min abin da zan maka in hana hawan jinin kamaka”. Sai da ya dan nisa san nan yace “Idan na fada kin yi alkawarin yi min abin da nake so”. “In har bai fi karfi na ba, nayi maka alkawarin yi maka duk abin da ka ke so” “Ki kwalli cikin idona kice min I love you my sweet heart.yin haka zai saka ni inji sanyi a cikin raina. In kuma daina kokwanton matsayi na a zuciyarki”. Kasa tayi da idonta san nan cikin sanyin murya tace “ba kullum baki kan furta asalin abin da ke cikin zuciya ba, amma idan mutum ya lura halayyar dan Adam kan iya yi masa nuni da abin da ke cikin zuciyar”. Sai da ya dan yi tafi san nan yace “yarinyar nan ashe wayo gareta ban sani ba. Amma hakan ma ya gamsar da ni. Tun da kullum cikin kykkyawan yanayi na ke ganin ki. To amma ina mutan gidanku suka tafi dukkansu kika yi saura sai ke kadai, ko da sauran mutane a gidan”? “Su farida ne zasu koma makaranta shine duk suka yi musu rakiya”. “A wane gari suke karatun”? “A sudan”. Cike da mamaki yace “Sudan? To ke me ya hanaki tafiya Sudan din”? Fuskarta ta dan nuna damuwa, san nan tace “Tun farko na sanar da kai bani da kokarin boko. Kaga Farida Medicine take yi. Farisa kuma computer”. Cike da haushi yace “and they left you to be their maid”. Ta dago ta kalle shi san nan tayi murmushi tace “ina ga kana mantawa na gaya maka ban iya turanci ba”. “aikuwa in sha Allahu zaki koye shi. Yaushe zasu dawo”? Ta daga kanta alamar tunani. Ta tuno da lissafin da Momi tayi mata, in da ta bata dubu goma a kan ta dinga sayen abinci a ciki. Amma fa ta hada da gargadin idan anyi ciniki kar ta taba mata ko kwabo, ta kuma lissafa mata yadda tafiyarsu zata kasance, san nan tace “eh to watakila suyi wata biyu, saboda sunce idan sun je Sudan suka gama ko ragisrarashin, sai su wuce Saudiyya suyi ummara. Daga nan kuma su kaiwa anti Bilki ziyaraa can kasar sin”. “yanzu ke da waye a gidan”. “daga ni sai Baba laure ko da yake ita tana wajenta a baskwata”. Sai da ya daga kai ya kalli girman gidan san nan yace “kuma ke ba kya tsoron kwana ke kadai a cikin gidan nan”? Ta dan yi murmushi san nan tace “ni bana wani jin tsoro.kuma ma na saba suyi tafiya su barni ni kadai”. Take yaji ransa ya baci. Tabbas matar nan is wicked, ba abin da ya dameta da safety ko tarbiyyar yarinyar nan. Amma ya danne bacin ransa yace “me ye ragisrarashin”. Abin da dalibai suke yi idan zasu koma sabon zangon karatu”. “OK you mean registration”. “Eh shi”. “ok repeat after me re-gis-tra-tion” Sai da ta maimaita wajen sau uku kafin ta samu ta fade shi daidai. Sai da yaga ta samo wan nan yace “to daga yau idan nazo zamu yi English lesson na atleast one hour”. Ta gyada kanta alamar ta gane. Amma duk da haka sai da ya saka ta ta fahimci ma’anar kowacce kalma da ya fada. Ganin gidan bakowa sai suka samu sake. Washegari da zai zo ya taho mata da wayar TECHNO irin ‘yar dubu hamsin din nan. Da yake ba sanin darajar waya tayi ba, bata fahimci mai tsada bace. Haka zalika ya jibgo mata tarin litattafan koyon turanci da kuma spelling. Kullum kuwa yazo haka zai kashe lokaci yana koyar da ita turanci. Bayan nan ya dauki sarar yawaita Magana da turancin a tsakaninsu, kuma zai bata lokaci ya bata dama tayi ta canka har sai ta gano ma;anar abin da yake nufi. Haka zalika yana yawaita encouraging dinta data yi simple sentences da turancin. San nan ya bata lokaci wajen koya mata amfani da wayarta ta yadda zata shiga dictionary ko kuma google ta gano ma’anar kalmomi da kanta. Haka nan kullum idan yazo zai sakata, ta koyi spelling at least 10 new words da kuma meaning dinsu. Ba shi ba ni kaina na yaba da kokarin Zainab. Saboda dai simple sentences ta iya constructing din su da kyau. Haka nan ta na fahimtar zancen da ya kan yi mata da turancin. Haka kuma dan chatting din da ya koya mata suke yi lokuta masu yawa shi ma ya taimka mata wajen fahimtar yaren turancin. Abin ya so bani mamaki amma sai na tuna zancen wani malami da ya ce duk wanda ya iya harshen larabci, koyon ko wan ne irin yaren a duniya ba ya masa wahala. To itama advantage din data samu ke nan. Zainab dai na samun attention amma aikinsa Allah ya sa yana da mataiamaka na kwarai da an samu matsala. Amma Alhamdu Lillah kwalliya tana biyan kudin sabulu, saboda kuwa dan dai turanci daya biyu na kare yawa yana samuwa. Haka zalika rubutu ma ana samun ci gaba. Ga kuma jajircaccen malami ga kuma daliba maikwazo sai komai ya tafi daidai. Yau su Momi sun dauki sama da sati hudu basa gida. Ba abin da ke hada su illa idan an kira Momi a waya ana bukatar snacks ta yi wa Zainab waya ta bata instruction din abin da ake nema. Damuwarta kadan ce saboda da dama ko suna gidan ba wata mu’amala da ke hada su in dai ba wani abu za a sakata ta yi ba. Farida ce kawai dama dama, domin ita har hira tana zama tayi da ita. Ga kuma yawan alkhairin da ta ke mata. Domin ko wan nan shopping din da suka je sai da ta sayo mata roll on na sure guda biyu da kuma body spray din su. Ta hado mata da turaren splash na VICTORIA SECRET GAEDEN. Da zata tafi kuma ta bata kayan sawa wadan da ta cire zata bayar saiti shida kuma duk masu kyau da tsada, haka nan ba su ji jiki sosai ba. Da kuma wasu designer turararruka da kadan suka yi kasa da rabin kwalbar, guda biyu. Ita ma kuwa haka ta dage da kanta ta tambayi Momi kaji aka sayo tayi musu dambun nama mai dan Karen dadi. Ta yi mata fura wacce baba Laure ta koya mata ta shanya ta bushe. Ga su tankwa da busasshen attarugu duk ta hada musu. Har da yajin daddawa aka sayo kayin hadi Mama hajjo ta hada mata. Ita kuma ta kai inji nika ta tankade musu shi. Saboda haka ba wani kewar su tayi ba da ba sa nan. Balle kuma yanzu da take cloud seven watau duniyar masoya. Ba karamar kewa Balan ta mai gwanjo yake dauke mata ba. Kullum sai ya kawo mata ziyar da safe da kuma yamma, san nan da dare su sha waya da shi. Ita ba sayen katin waya take ba, saboda haka bata san tsadarsa ko arahar sa ba. Sai kuma ya kara da yi mata wayo, inda ya sanya mata dubu hamsin a wayarta, yace da ita tayi ta waya ko yaushe MTN ne suka bata bonus na dubu hamsin din. Haka kuwa ta yarda. A wan nan rana da ya shigo da safe ya sanar da ita zai kawo abokanan sa su gaisa da ita. Bayan ya gama koyar da ita karatu yayi sallama ya tafi da alkawarin zuwa shi da abokansa bayan la’asar. Nan take ta shiga tunanin me zata basu idan sun zo. Kudin da Momi ta bata ta dinga sayen abinci tana
Chapter 18 · 0% Book details