Sashe 11
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan su kosa ya hakura ya bar gidan. Ya kuwa tafi zuciyarsa cike da tunani 'yar kyakkyawar budurwar da ya gani wadda ta sa shi karya azumi da kuma yin abin da ba dabi'arsa ba watau cin abinci a gidan mutane. [8/6, 23:15] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👨👧👨👧 IN FIKI A MIKI💑💑💑💑 Page 12 BY HANNE ADO ABDULLAHI Al bashir Usman matashi ne dan kimani shekaru ashirin da bakwai. Kyakkyawan saurayi dogo wanka tarwada mai kyakkyawar kira. Irin dan nan ne da ko wadan ne iyaye suke burin samun irinsa. Ga ilmi addini dana boko san nan ya kawata rayuwarsa da kyawawan dabi'u. Da ne ga Hajiya Rakiya da hamshakin mai kudin nan wanda ya kasance daya daga cikin masu kudin garin nan watau Alhaji Usman Ahmad Babba. Bayan gama karatun AlBashir sai ya dauki wani layi sabanin irin business din da ya tashi ya samu mahaifinsa yana yi watau harkar sufuri na jiragen ruwa. Textile company ya bude a China shi da wani abokin karatun sa dan asalin kasar mai suna Kim Suen. Lokaci daya ya zama mamallakin rabin hannun jari a kamfani buga kaya me suna KIMBASH. Kusan a kasuwar garin nan babu wasu kananan kaya da suke samun kasuwar nasu. Su kan saka kananan lesuka da kuma atamfofi da yadudduka na maza da mata. Komai tsadar zaninsu ba ya wuce dubu hudu a hannun masu saye daidai. Amma ingancinsu sai mai goyo sai ta shekara hudu tana amfani da shi ba abin da yayi. Hakan ya sa suka samu kasuwa sosai. Karamar riba suke bi. A wata atamfar bai fi a samu naira goma kan kowanne turmi ba amma fa a rana za a iya sayar da turmin miliyan. Bai fi shekara biyu da fara wan nan harka ba ya biya mahaifinsa baashin kudin da ya bashi ya fara kasuwancin da su. Da a kasuwar duniya za a tallata shi darrajarsa zata kai naira biliyan hudu. Ga shi dan gata na kin karawa saboda shi ne suta a gidansu. Yayyensa mata hudu. Yaya Ai. Yaya Rabi . Yaya maryam sai kuma wacce yake bi Yaya Bilkisu. Dukkasu kowacce tayi aure da nata iyali. Amma yaya Ai wacce suke kira da Maama, ta bar mata rikon babbar 'yarta mai suna Meena. Wata irin rayuwa suke ta tsananin kauna da kuma mutunta juna. Idan ka gansu tare da mahaifansu sai ka dauka abokan juna ne. Amma hakan ba zai hana Bilkisu da take karama ta saka Al Bashir ya canza wa danta pampers ba. To wan nan rikakken dan gata gaba da baya da kuma tsananin wayewa da yayyensa suka ci buri a kan auren sa shi ne ya gama zaga duniya ya kasa gano kowacce irin mace sai Zainab diyar dana dade ban ga yarinya marar gata irin nata ba. Tun da ya yi ido biyu da ita a gidan chief accountant dinsa watau Sulaiman gaba daya ya rasa sukuni. Da kyar ya daure ranar da ya fara ganinta ya bar gidan. Saboda gaba daya tagama ruda shi. Ga shi dai bai gama sanin ko wacece ita ba saboda ko sunanta bai sani ba. Amma 'yar zirzirgar da tayi na kimanin awa biyu, yana hankalce da ita. Hakan ya sa ta dasu a ransa kamar dashen tsohuwar bishiyar kuka. Su dai masu gida alkhairin da ya kai musu shi ya sanya su tsananin farin ciki. Yan mata dubu dari cas ya ajiye musu da sunan su sa kati. A zuciyarsa kuwa niyyarsa sakon ya kai ga sabuwar masoyiyarsa. Ba shi da masaniyar ba ta ma da masaniyar anbada wata kyauta. Ita kuwa maijego dala dubu ya bata da sunan a sayawa jariri pampers. A wan nan rana tunanin Khadija bai barshi yayi bacci ba. Saboda haka kamar yadda ya saba kwana yayi yana sallah da karatun AlQurani mai girma domin neman dauki a wajen shugaban halitta. Washegari kuwa daga masallaci dakin ummansa ya shigo kamar yadda ya saba duk safiya. Duk kudinsa ya kasa tashi daga cikinsu. Dakinsa ciki da falo yana daga gefen babban falon gidan. Da sallama ya shiga dakin Ummansa. Kamar yadda zata lazumi ya sameta ta na yi kamar kullum. Amma yau sabanin lokutan baya da zai zauna ya jira ta ta gama shi ma kuma yayi nasa a gefenta. Yau kam kasa hakurin haka yayi. "Ummana barka da asuba " ya fada yana mai dora kan sa a kan cinyarta kamar wani karamin yaro. "Barka ka dai" itama ta amsa tana mai shafa kansa. Ba sai ya gaya mata ba shakuwa irin tasu, tasa ta gano tabbas yau da matsala. Tana kokarin tambayarsa taji sallamar Abbansu ya shigo. Shima bayan gaisuwa a tsakaninsu ya juya ya kalli dan nasa, yace "yau kuwa kalau dan uwan Ummansa yake na ga yau autancin ya motsa"? Tashi yayi daga cinyar mahaifiyarsa ya koma ya rabu da uban kamar marar lafiya, san nan cike da kaskantar da murya kuma cikin ladabi ya shaida musu halin da ya tsinci kansa . An tambayi sunanta yace bai sani ba. Yar gidan waye bai sani ba. Abu daya ya sani a kanta gidan da ya hadu daita. Abbansu ne ya ba shi shawarar ya koma ta inda aka hau ta nan ake sauka. Saboda haka ya umarce shi da ya koma gidan Sulaiman ya yi duk binciken da zai yi daga wajensa [8/6, 23:18] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👨👧👨👧👨👧 IN FIKI A MIJI💑💑💑💑 Page 13 BY HANNE ADO ABDULLAHI KimBash textiles ba sa budewa sai wajen tara. Shi kuwa oga ya kan kai goma bai shigo ba. Amma ran nan masinja da mai shara ne kawai suka riga shi zuwa. Oficce din accountant Sulaiman Bello ya fara kaiwa ziyara saboda shine makasudin zuwan sa da wan nan sanyin safiya, sai dai fa ya daki gurbi, domin kuwa bai shigo ba. Ya buga wayarsa a kulle. Ya aika kiransa yafi sau bakwai ana dawo ma sa da sakon bai zo ba. Shi da kansa masinjan hankalinsa ya tashi ganin wan nan sako na duk bayan minti biyar da ake aikawa accountant. Bai san cewa shi mai sakon ba ya ganin sakon a kai a kai ba. Wanda yake aiken gani ya na yi yana ba da ratar wajen minti talatin. Hankali a tashe ya nufi gidan accontant. Saboda bai san kiran na menene ba. A round din Obasanjo suka yi clear da shi. Saboda haka ya juyo da mashinsa ya dawo office. Yana parking shi ma Tasi'u masinja yana karasowa. Da hanzari ya nufi inda yake kokarin kulle motarsa. Yana kokarin gai da shi shi kuwa da sauri yake fadin "yi sauri ofishin chairman. Aiken sa takwas oficce dinka yana nemanka". Shi ma kiran ya ruda shi. A tunaninsa ba laifin da ya aikata. Haka zalika jiya ogan nasa ya kai masa ziyara har gida. Kuma yadda ya saba mutunta ma'aikatansa shima a haka suka rabu da shi. Me ya kawo irin wan nan sammaci haka? A rikice ya karasa wajensa cikin hanzari. Ya na shiga kuwa ya tarar da shi yana safa da marwa a office din. Yana ganinsa ya saki ajiyar zuciya. Kafin ya karasa shigowa ya isa wajensa shi da kansa ya kamo shi. A kujerar bakin table din sa ya zaunar da shi. Shi ma ya ja daya ya zauna suna fuskantar kujerar AlBashir ta asali. "Lafiya yallabai naji ance kana ta aiken nema na. Bari in dauko laptop dina da ga mota sai muji dadin discussing koma meye". "Manta ba aikin office ya sa ni kiran ka ba? Wacce yarinya ce jiya na hadu da ita a gidanta". Ya dan daga kansa alamun tunani. San nan yace "Jiya yallabai 'yanmata uku ne a gida na. Farida dake karanta medicine a Sudan. Sai kanwarta Farisa itama a sudan take sai kuma kanwata Aisha. Su ke nan su ukun a falon". Da wani irin shauki, Albashir yace masa "Ta nan wata doguwa light skinned tana tafiya kamar amaryar dawa. So humble yet classy and well mannered. Wata data kawo min ruwa da abinci". Damamaki a fuskarsa yaga ga haddadun 'yanmata da suka ci kwalliya ta birgewa amma sai nannadaddiya ce ta burge oga. Cikin mamaki yace "yallabai ba dai Zainab kake nufi ba". "ZAINAB"! AlBashir yaja sunan cikin makogaransa mai dauke da wani irin shauki. "Beautiful name. Itace wata mai wadansu itin xarazaram fingers looking so beutiful in her Hijab". Cikin dariya Sulaiman yace "yallabai i have never notice her beuty.amma dai she is the only one wearing hijab a cikinsu". "To ita din nake magana a kai. Yaya kuke da ita?." "Dukkansu 'ya'yan sister Bilkisu ne. Kuma a gidansu ta girma. Babansu shine commisioner of finance na garin nan. I know their family very well. Ya dan dada rankwafowa kusa da shi san nan yace "ka san ni da kyau. Ka san family background dina . Zainab ma kuma na fahimci ka san su very well tun da kayi aure from the family". Sai da Sulaiman yaja numfashi san nan yace "amma yallabai iam very suprise by your choice. Naga ga more sophisticated girls around but you chose the most backward. Na ga maza yanzu sun fi son polished 'yan mata amma kuma kai naga......." sai kuma ya kasa karasa maganarsa. "Bad choice". In ji AlBashir. San nan ya ci gaba da cewa "ka san ni 'yan uwana mata ne. I know a real lady and a fake one. Look at the respect she gives. How well mannered she is as well as her caring nature. That is what makes a good wife". "Haka ne yallabai. Amma akwai matsala daya. Kaga dai kasa dai dai ce a duniyar nan baka zaga ba. So akwai banbancin exposure a tsakanin ku". "Duk ka manta da wan nan. Ni zan bata irin exposure da nake bukata ta samu. Ai ba kowacce exposure namiji yake bukatar matarsa ta samu ba. Ni dai ka yi min jagora zuwa gidan in samu shiga. In ka min haka ka gamamin komai". Nan dai suka daidaita a kan da la'asar zasu kaiwa Zainab ziyara. Ana fitowa daga masallaci kuwa Albashir ya aika fagge wajen telansa aka karbo masa sabuwar shaddarsa president bugun switzerland ba chinaba. Cream colour da ita ta sha wani irin dinki irin na manyan kekunan nan na