← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 43

Sashe 25

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

[8/8, 21:42] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI 💏💏 PAGE 24 BY HANNE ADO ABDULLAHI Tun da su Al Bashir suka fita yake cikin bacin rai, na ganin abin da Momi tayi musu. Har wata karkarwa yake ta bacin rai. Mujib ne yayi karfin kiran mallam Usman. Bayan ya gaishe shi ya sanar da shi duk abin da ake ciki. Ya basu shawara suje su sanar a gida. Idan yaso duk abin da mahaifansu suka yanke shi za su bi. Shi kuma ya dada kwantar musu da hankali akan su yi tawakkali komai zai faru. Su dauka haka Allah ya kaddara. Ba suyi kasa a gwuiwa ba kuwa suka je. Sun kuwa yi sa’ar samun Abban su tare da yayan ummansu watau takwaran shi Al Bashir wanda shine dalilin da take kiransa da dan uwana. Nan Mujib ya zayyane musu komai. Shi kam bacin rai ya hana shi Magana. Nan Ummansu ta shigo aka kira yaya A’i. Ita ma ta karaso aka sanar da ita abin da ake ciki. Nan dai suka yanke shawara zuwa gidan su Zainab ranar jumma’a wanda ya kasance dai dai da kwana tara da wa’adin da aka diba musu. Umma ce ta tuntsire da dariya tace “wai zan so inga wan nan zarar mata da ta saka dan uwana a kwana har ta kaishi da zuwa kasuwar gwanjo da kuma hawa mashin”. Yaya A’I ma dariyar da take ke nan. Ita kuwa tun da abin nan ya faru ta rasa natsuwarta. Gani take yi ta rasa Al Bashir. Bata san haka ya shiga ran ta ba sai yanzu da ta ga tana neman rasa shi. Ta rasa dalili wanda ke sayen snacks a wajenta tun da su Momi suka dawo bai kara zuwa ba, balle ta samu kudin shiga. Ba tare da sanin ta ba Al Bashir ya daina zuwa saye saboda tunanin aiki zai yi mata yawa Fatu ta nema su ka kwashi rigunan da Abbanta ya kawo mata daga Saudi. Ba wanda ya sani suka tafi Camp. Tayin farko ma rigunan ‘yan Morocco a sha biyar aka taya su. Su kuwa after din dubu ashirin da biyar. Take suka yanke shawarar yi musu kudin goro. Kowacce dubu ashirin. Ita ba ta san ma masu tsada bane sai a lokacin. Fatu ce ta bata shawarar ta dauki riga biyu daga ciki da kuma after daya, don ta samu na kwalliya. Ita kam da an bi ta tata ta fi son ta sayar duka ta bawa Balan ta kudin. Suka sayar da after guda bakwai da rigunan suma guda bakwai. Kudin su dari biyu da tamanin haka suka dawo da su cas. Fatu ta sake saka ta ta dauki tamanin daga cikin kudin. Suka shiga kofar wambai ta sayi zannuwan gado guda biyu na gwanjo ‘yan dubu bibiyu. San nan suka shiga wajen masu kayan kicin ta tsintsinci ‘yan kayan kicin dai dai na dubu hamsin har da risho ta saya. Daga nan suka tsaya shagon mudassir a filin parking. Nan ma ta sai atamfa ‘yar 4500 guda hudu. Ta sai wata shadda barauniyar bazin ta dubu hudu. Ta sai leshi guda biyu na dubu biyar biyar.. kwarai ta haura budjet din ta da dubu biyu, amma haka ta dada daurewa ta sai masa shadda ‘yar dubu goma yadi goma da zummar ta sai masa ta daurin aure. Ta kuma saya masa guda biyu ‘yan dubu biyar biyar yadi biyar. Ta fito bakin shagon ta sai masa hula guda biyu ‘yan 2500. Suna sauka daga adaidaita a kofar gidan su Fatu, shi kuma yana karasowa a kafa. Suna ta kakabin sauke kaya ta bayansu suka ji ance “yan mata adon gari inzo in yi dako ne”? Da hanzari suka juya. Suna ganin shine duk suka saki dariya. Bayan sun gama sauke kaya. Fatu ta shiga gida ta fito masa da ruwan pure water da mamanta take sayarwa da kuma kunun zaki. Sai da suka shiga suka yi sallah duk yana jiransu a dakin yayan Fatu, san na suka sake fitowa. “wai daga ina kuke ne haka na ganku a gajiye”? Daga wajen mai magani muke ta isheni da kuka za a raba ta da masoyinta, shine na kaita wajen wani mai magani yace mu samu hawayen kuda da kwan sauro sabuwar kyankyasa da kuma kafar kiyashi ta hagu zai hada mana lakanin da ruwa da iska ba mai rabaku”. “saboda Allah Fatu kina ganin halin da muke ciki amma zolayar mu ma kike yi”. Cikin dariya ta ci gaba da cewa “ina kuwa zolaya kana ganin yadda na dage taya ku neman magani” ta fada tare da mikewa don kokarin fita daga dakin. Sai da ta fita yace “Putri Salju ina labari”? “lafiya kalau. Amma ya na ganka a kafa ina mashin dinka”? “Ba jiya na sanar da ke zan sayar ba ai har anci kasuwarsa”. “amma ban so ka sayar da shi ba. Ka ga ai zai taimaka maka zuwa kasuwa da yana nan”. “kasuwar ba sai a je a kafa ba in dai za a sameki”. “Allah yayi mana jagora”. Fatu ce ta shigo da tray din abinci. Tana ajiye wa ta fita ta barsu a dakin. Ita ta bude food flask din. Birabiskon gero ne da miyar yakuwa. “Allah ya sa ka iya cin abincin bare bari” ta fada tana mai zuba masa a plate. Yana ci suna hira. Ya kuma ci da yawa, ko don dadin zancen da take masa. Sai da taga ya ci sosai, san nan ta fito da kudi daga cikin zaninta ta mika masa dari da sittin. Cike da mamaki ya kalleta yace “inaa kuma kika samo kudi masu yawa haka. Na fa lura hajiyata kudi gareki. Wadan nan kuma daga ina”? “kudin kayan da kaki karba ne wannda Abba ya kawo min tsaraba daga Mecca”. Nan ta shiga lissafa masa yadda ta sayar da su da kuma abin da ta saiwa kanta. Cike da tausayin irin son da take masa ya ke sauraron bajintar ta. Bata lura da yanayin sa ba, cike da zumudi ta shiga fitaar da kayan da suka sayo tana nuna masa. Ta kuma dauko shaddar da ta saya masa da hulunansa guda biyu ta mika masa. Har wata kwalla ce ta subuce masa na tsananin tausayinta. Yanzu ya lura ashe ba mace ta tsara maka kalaman soyayya ne zai nuna son da take maka ba. A’a sadaukarwarta da kuma kula da kai shine hakikanin soyayya ta gaskiya. Ji ya ke kamar ya tashi ya rungumeta saboda tsananin murna. Ya dago ya kalleta cike da wani irin shauki a ransa. San nan yace “Zainab na gode da irin son da kike min. ni kuma nayi miki alkawari da iznin Allah ba zaki taba kuka da aure na ba. Zan nuna miki kauna. Zan baki farin ciki da baki taba tsammanin samun irin sa ba. Yanzu a ina kika ga ya kamata mu nemi dan gida da zamu zauna”. “tace ka san ni ba sanin gari nayi sosai ba. Amma duk inda zaka nema ka nemi inda ba zaka sha wahalar zuwa kasuwa ba” “Ni da ce ma zaki yarda sai mu ci gaba da zama a gidan mu kusa da Ummata. Ina da daki ciki da falo daga waje da kuma dan bandaki na. In yaso ko daga verender sai an rufa miki kitchen”. “Amma lalle kuma ina gidan sai Umma ta yi girki, sai kace ban san ciwon kai na ba. Kabar mana kitchen daya ya ishe mu. Wadan nan kaya kuma ka tafi dasu. Tun da Momi tace kai za ka yi komai, sai ka tafi dasu wajenka. Amma kayan sawar ka barmin zan dinka da kaina a keken mama Hajjo”. “Sana’a nawa kika iya. Ban da snacks da kike yi har dinki kin iya”. “lah aihar zanen lalle da gyaran jiki na amarya na iya. Dama zance idan zaka amince min sai nima in dan dinga sana’a a cikin gida. Ko dinkin ko gyaran jikin ko kuma snacks din duk wanda ka zabar min”. “To putri Salju ni da nake burin mai da ke sarauniya kuma kina debowa kanki aikin wahala”. A shagabe tace “ni dai kayi min izzni in gwada wata sana’ar kaji mi……” Bai san sanda ya sa hannu ya lakace mata kumatu ba yace “da wanan muryar taki ai ko duka na kika nemi iznin zan barki kiyi balle sana’a. amma dai ni complain dina daya kar neman kudi ya hana a kula da ni. “Zan maka alkawari daya. Matso kana gida zan ajiye komai in maida hankali na da duk wata kulawa ta gareka”. “da gaske matata”. “Da saura tukun na”. “A’a wai da na ji kin kira ni mijin ki sai na zama convince of my status”. Kunya ta kamata ta kasa amsa masa sai ta basar da zance. Ganin haka shima ya kyale maganar yace “Amma ki bani har kayan sawar taki in tafi dasu. Zan nuna wa Ummana gobe zan dawo miki da su”. Nan kuwa taa hada masa har da kayan kicin din data saya. Su kam da niyyar ya barsu a a gidansu kawai. Yana shiga ya jibgewa Ummansa kaya a gabanta, yana fadin “Umma kuna tsokana ta na shiga gwanjo saboda Zainab. Ita ku duba irin abin da take yi sabo da ni”. Yaya Maryam da ta shigo taji labarin abin da Zainab tayi na kokarin ganin ta taimakawa Albashir ya aureta, ita ta ba da shawarar a bata duk atamfofin sai da kuwa ta samo original super kowacce haka ma shaddar ta sayyo ‘yar 40k dinta. Leshi ne aka kasa samun manyan su irin wadan nan. Zainab ganin ta hada da wan nan ta mai da hankalinta kan saukar da za suyi hankalinta kwance. Ta san dai kudin nan ko ba su cika dari biyar ba sun kusa. Shi kuwa shi da Mujib duk abin da aka yi sai sun bugawa mallam Usman watau Abban Hafsa sun sanar da shi. Ranar jumma’a da misalin goma na safe su Alhaji Usman da kuma ‘yan uwansa suka tunkari gidan Dr Abdallah Zubair domin nemar wa dansu aure. Ga shi dama suna da daurin auren ‘yar wajen Alhaji Bashir saboda haka suka nufi gidan da niyyar daga nan sai su wuce daurin auren wanda ita ma
Chapter 25 · 0% Book details