← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 43

Sashe 33

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 3 min read

da dining dinsa, wanda daga karshensa katon kitchen dinta yake. Shi kuma a gefensa faffadar staircase ne wanda zai kai ka saman gidan, yayin da a bangaren hagu kuma ta sake ganin wata kofa a rufe, sannan suka hau inda ta samu manya dakuna guda uku da falo dan madaidaici da kuma dan wani ofis na aiki a cikin gida da yayiwa kansa. Daga dakunan har falon ni dai na san ko Rakiyan Jagi da Amina ba zasu hada gida ya fi haka kyau ba. Labulayen nan har sheki suke yi kamar da silk aka yi su. Haka carpets din dake shimfede suma abin kallo ne. Da ta shiga dakin daya ya nuna mata a matsayin nata, kawai hawaye ne ya zubo mata. Closet ta samu dankare da kayan sawa sun fi kala dari. Kuma a cikin kayan nan Holland ce mai karamin kudi. Ga takalma da jakunkuna birjik da su. Fiye da rabin kayan a dinke suke. Ga turarurrka designer fal kan dressing table dinta. Haka nan toilet shima an kawata shi da copboards masu dauke da towels da kuma kayan shafa daga wani lungu. Ko a mafarki bata taba haskowa kanta irin wan nan rayuwa ba. Meena ce da ta zo kawo musu abinci take shaida mata ga lefenta inji su Maama. Ta gane Yaya A’I take nufi da wan nan suna. Ita ta kama mata suka dan dada gyara abin da ba a rasa ba, san na tayi musu sallama ta shiga main house. Washegari bayan sun dan taba kailula, suka zauna ware tsaraba. Shi ya sa ta ware na mutan garko daban na mutan kera daban san nan na ‘yan gidansu. Suma kuma nan gidan haka ta dauki tasu tsarabar rankatakaf ta kai musu. Fatu kuwa da mama Hajjo da ‘yan gidansu akwatin su daban. Bayan nan ya bude mata daya kofar da ke rufe a kasa. Wani irin industrial kitchen ta gane mai dauke da injuna yin snacks da katon oven da zaka iya gasa cake dari biyar a lokaci daya. Shi kuwa samosa makinga machine din sai dai ta hada fillings idan ta kwaba flour a mixer wacce a lokaci daya zata yi kwaben flour na kwano uku. Asa dough din a wani waje a sa fillings a wani waje, sai dai ka dainga daukar finished samosa din ka ko spring rolls ko meat pie daga karshe depending on mould din da ka saka. Ita ma kuma a cikin awa daya tana nada maka samosa ko spring rolls ko meat pie dari biyar. Ga su chopper da meat mincer da dai duk wani abu da zata bukata to enhance her business. Abu daya zata iya tunawa suna China aka nuno irin wan nan kitchen din da yadda ake operating dinsa. Cike da exicitement tace “how I wsih I could get some thing like this”. Bai ce mata komai ba bai ma nuna ya na da interest a kan abin data fadi ba. Juyowa ta yi ta rungume shi ba tare da sanin tayin hakan ba. Sai godiya take zuba masa. “Hold on. The kitchen is your wish, idan kin so kiyi sana’a idan baki so just let it be, because you don’t need to”. Albashir yace da ita. Ba ta samu shiga gidansu ba sai wata washegarin da la’asar ta nufi gidan ba tare da ta san irin tarbar da momi zata yi mata ba.
Chapter 33 · 0% Book details