Sashe 15
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
da shi saboda sunan danta na fari ke gareshi. Ba abin da ya basu mamaki irin yadda tunda suka gaya wa Momi cewa cirani iyayen su suka zo daga katsina, bata sake bibiya taji asalinsu da kuma irin binciken da addini ya sa a yi a kan masu neman aure ba. Nan take kuwa ta gano cewa ta samu inda zata kai Zainab inda zata kaskanta ta wahala. Saboda haka ta juya wajen miji tace “ina ga Daddyn Farida ka ba shi dama ya fara neman aurenta tun da dai yana da sana’ar da zai riketa, kar mutane su dauka ko don kana Commisiner ni kuma ina director ‘yarmu tafi karfin auren talaka”. Ta sake mai da hanakalinta wajen su Mujib tace “ka iya ci gaba da neman aurenta. Amma duk abin da za a yi ka tabbatar nan da wata uku za a aurar da ita. Idan ka kasa zuwa neman aurenta nan da wan nan lokaci zamu aurar da ‘yarmu. Kuje ku jira ta a waje zan turo muku ita yanzun nan”. Sukayi mata sallama suka fita. Mujib bai san sanda ya saki wani irin zagin ba. Yace “matar nan she is a real evil. Gaskiya ko da ban ga Zainab ba I will want you to take her away from this wicked woman”. Momi kuwa da murnar ta ta shiga gida. Zainab na kwashe kayan Kwando ta same ta a kicin. Sai da ta rangada mata guda a ka san nan tace “uwar neman maza sai ki godewa Allah. Neman ya kare miki kije ubanki ya fitar miki da miji kafin ki fitar masa da abin kunya. Ga shi kuma mai sana’a mai riba. ‘yar garaugarau dai da kuma riga da wando ko skirt na gwanjo ba sa gagare ki ba”. Ta sake fashewa da dariya “san nan tace ki wuce kije yana jiranki. Amma ki tabbatar kin shigo gida nan da minti ashirin saboda bar ganin zaki wajen saurayi ba uban da zai dora miki abinci dare. Su Farida karatu ya sha musu kai, saboda haka idan kika haura hakan zaki hadu da ni”. Ita dai saroro tayi tana kallonta saboda tama kasa fahimtar abin da Momi take nufi. Sai da ta fita san nan Baba Laure tace “wuce kije kin ji uwata”. Sanye cikin hijabinta wanda ya kusa rufe dunduniyar kafarta ta nufi wajen bakon da bata san shi ba.“ [8/6, 23:22] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 17 BY HANNE ADO ABDULLAHI A nan wajen Mallam ta same su tsaye. Tun da ta dosu su suka tsaya da zancen da suke yi. shi dai Mujib mamakinsa ya tafi ne akan yadda take spreading wata irin aura even though ko ina na jikinta a lullube yake. shi kuwa sarkin masoyan duniya nurnar ganinta ce ta saka shi ya kasa ci gaba da zancen da su ke yi. cikin zazzakr muryarta ta durkusa har kasa tace "barkanku da yamma" "barka kadai gimbiya" inji Mujib. "Da fatan mun same ki lafiya kalau"? "lafiya kalau ". kunma har a wannan lokaci tana durkushe bata mike ba.Mujib ne ya sake cewa "to gimbiya Zainab mike mana ai mun gama gaisawa". "a'a ba komai hakan ma yayi" ta sake fada. A tare bakin nata suka hada ido sai kawai suka zube a gabanta suma suka durkusa. cike da mamaki tace "lah ya haka kuma"? "Tun da gimbiya na durkushe ai kuwa ba mu ga ta tsayuwa ba". Bata san sanda wata 'yar gajeriyar dariya ta subuce mata ba. san nan ta mike tsaye. mikewar tata yayi dai dai da zuwan Mallam wanda ya karaso wajensu dauke da kujerun roba guda biyu. hakan ya sanya su suka zauna a kujerun yayin da ita kuma ta zauna a dan dakalin dake bakin varender gate din. Bayan nan suka sake sabuwar gaisuwa. mujib ne ya nuna mata Al Bashir ya ce "kin gane shi"? ta dan dago ta saci kallansa sai kuma ta girgiza kanta alamun a'a. cike da zolaya yace "da gaske Zainab baki gane ni ba. ni kuwa tun randa na fara ganinki na yi printing din fuskar ki a zuciyarta". murmushi ta sake yi cike da jin kunya san nan tace "Allah da gaske nake kayi hakuri ban gane ka ba”. “Amma dai ina fatan daga wan nan haduwar zaki gane ni ba tare da na sake introducing kai na ba”. “In sha Allahu” ta amsa masa tana mai nuna jina kunya. Mujib ne ya sake gyaran muryar tare da cewa “to malama zainab ni dai suna na Mujib Sani shi kuma wanda kika kase ganewa sunan sa Bash. …” mintsinin da ya kai masa shi ya hana shi karasa sunan da ya fara fada. Nan take ya gane me yake kokarin shaida masa. Take kuwa ya gyara kuskurensa yace “shi kuma sunansa balarabe. Kuma shi ya ganki yaji kuma yana da ra’ayin ki zamo abokiyar rayuwarsa idan har kin aminta da shi”. Shiru ita dai bata yi Magana ba sai wasa da take da hannayenta ta cikin hijabinta. Kiran sunanta da Mujib yayi shi ya sanya ta sake dago kanta. Tana dagowa kuwa suka hada ido da AlBashir wanda ya kura mata ido. Itama ta dan yi tsai da idanuwanta cikin nasa san nan ta yi kokarin kau da nata idanuwan. Nan dai Mujib ya yi ta kokarin ganin ya dasa bishiyar kaunar Al Bashir a cikin ranta. Duk da dai basu sami tartibiyar amsa ba, amma sun gamsu da yadda ta yi musu. Shi kuwa AL Bashir duk da ba wata Magana mai yawa ya samu yayi da ita ba, Amma tsayuwar ta kawai kusa da shi ya sanya shi jin wani nishadi. Khalil ne ya karaso inda suke tsaye cikin gatsali yace “ke kizo momi tace ki zo ki dora abincin dare”. Bata jin dadin yadda ya tsinka ta a gaban bakinta ba. Kuma tabbas suma sun gane bata ji dadin hakan ba. Da yaji shiru bata bashi amsa ba ya sake cewa “ko in je ince ba zaki zo ba. In kuma na fada kin san sauran jikinki ne zai gaya miki”. Ya juya zai tafi, Mujib ya yi sauri janyo shi yana fadin “yi hakuri abokina. Yanzu zata zo kaji kar ka gaya wa Momi komai”. Ya kalleta cike da tsiwa. Yace “kin yi sa’a. da yau na kalli kukan yaya babba tana shan duka”. Yana fadin haka ya juya ya bar wajen. Al Bashir ya lura da kwallar da ta ke kokarin sharewa cikin dabara tana kokarin kar su ganta. Yayi ajiyar zuciyar na takaicin abin da aka yiwa Zainab dinsa. San nan yace “waye wannan”? “kanina ne” ta amsa masa a takaice. Ya sake ajiyar zuciya y ace “shi ke nan Zainab shiga gida. Sai gobe idan na sake dawowa”. Ta sake durkusawa har kasa tace “na gode ku gai da gida”. San nan ta juya ta bar su tsaye a wajen su kuma suka rakata da kallon tausayi. Ba su tafi ba sai da suka yiwa mallam sallama. Shi kuma ya sanar da shi lambar wayar Zainab, wacce itama Baba laure ya sa ta dauko masa wayar. Ba ko kbo a cikinta saboda haka sai please call me yayi zuwa wayarsa san nan ya samu damar kwafar lambar tata. Suka fita mashin kuma yaki tashi haka suka hakura suka tura shi suna tafe suna tattauna yadda suka samu Zainab. Albashir ne ya fara tambayar Mujib yace “yaya is she worth the trouble”? “She is worth more than that. Ta bani tausayi matuka. And from yadda kaninta yayi embrassing dinta a gabanmu is a clear indication na bata da wani galihu a gidan. Amma fa gaskiya abokina tayi. Such rare beauty is very scarce”. “Ok fine kaima daga yau bazan kara zuwa da kai ba. Dama ai zancen farko ne kawai aboki yake rakiya. Daga yau kagama”. Dariya ya saka san nan yace “ai kaima ka san ko ba serious relationship bane once ka furta ni kuwa na haramta kaina zuwa wajen. So just trust me. Kuma kasan na gaya maka ni Meena nake jira ta gama secondary ka bani ita”. “au wai da gaske akan wan nan small girl din”. “shi yasa na ga wadda muka baro wajenta is over thirty five. Ita ma wan nan ta girmi Meenan ne”? “Fine kaje neman auren Meena. Amma bani zan raka ba. Don bazan je gaban ‘yata ina wage baki da sunan na rako abokina zance wajenta ba”. “Ai tunda na shigar maka kasuwar gwanjo zaka iya yi min duk wulakancin da kaga dama. Nima bance zan kiraka rakiya ba”. Haka suna hira suna tura mashin din nan basu yi realising ba sai ganin su suka yi daga Hotoro NNDC gidan su Zainab har sun iso round din Ahmadu Bello Way. Wanda su kuma Alu Avenue zasu shiga inda gidansu yake. Sule mai mashin dai Allah ya taimake shi, saboda suna isa gida aka bashi kudi ya sayo sabon mashin su kuma ya gyaro musu wan nan saboda zuwa wajen Zainab. [8/6, 23:24] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 18 BY HANNE ADO ABDULLAHI Da misalin sha daya na dare, zainab zaune a kicin din gidansu. Kowa yayi bacci banda ita. Yini tayi ta na murjin meat pie guda dari biyar da Momi ta samu odar sa. Da karfe bakwai na safiyar washe gari tayi alkawarin masu shi su zo su dauka. Kunnenta sanye take da ear piece tana sauraron radio ta cikin wayarta. Duk wanda ya santa, ya san ta da wan nan dabi’ar. In dai tana aiki to kuwa sauraron radio take yi. Da haka take saurare direct daga radion, sai ranar da Farisa ta ringa yi mata masifa akan tana damunsu da jiye jiyen radion ta, wanda ita kuma itace abokiyar hirar ta. Hakan ya sanya take manna ear piece a kunnenta. Ta san programmes din kusan kowacce tasha da kuma lokutan yada su. Amma yau abin da ya bata mamaki, ringin taji a wayarta ta, wanda ya katse mata shirin duniya labari da take sauraro a tashar freedom. Da sauri ta matsa amsawa a tunaninta Momi ce zata bata wani sakon.amma tana sallama kamar yadda ta saba sai taji bakuwar murya ta amsa mata sallamar da