← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 43

Sashe 13

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 9 min read

Lokacin da Mallam mai gadi ya dawo wanda shi kuma Sulaiman yaje daukko mota domin su tafi, yayi mamakin ganin bakon a wani yanayi. Yanayin sa ya banbanta da farkon shigowarsa gidan. Farkon da ya shigo gidan cikin fara’a ya shigo. Amma yanzu bayan dan bayanin da Sulaiman yayi masa, da ka kalle shi kasan cikin tashin hankali yake.
“yallabai lafiya dai? Naga kamar wani abu ya daga maka hankali”? mallam ya tambayeshi.
Sai da ya shafi fuskarsa da tafukan hannunsa. San nan ya dan yi tsai da dubansa akan fuskar Mallam yace “ka san dan adam idan ya kallafawa ransa samun abu, ya kuma gaza samun wan nan abu to ya kan shiga damuwa. To nima abin da ya faru da ni ke nan. Na kallafa raina akan samun Zainab a matsayin matar aure to kuma ashe ba rabona bace. Ashe an bayar da ita. Shine naji duk hankalina ya tashi”.
Cike da tsananin mamaki Mallam ya dago ya kalleshi. Amma jin kugin mota na kusanto su ya sanya ya kasa yi masa bayani. A iya saninsa ya wuce matsayin maigadi a gidan, saboda amfanin da yake yiwa mai gidan.
Duk wata harkarsa ta office ko kuma abin da ya shafi yaran gidan shi ya kan sanya yayi masa addu”a da kuma sauka. Wanda shine ma babban dalilin da ya sanya yake zaune da shi. Gadin nasa carmouflage ne. ya kuma san babu yadda za ayi a bayar da auren Zainab bai sani ba. Amma ya yi niyyar yin bincike akai. Saboda haka cikin hanzari yace masa “ka bani lokaci ina son ganawa da kai akan wata muhimmiyar Magana wacce bazata yiwu yanzu ba. Amma idan har ka amince zan maka dan wani bincike idan har na gano gaskiyar lamarin zan zo maka da bayani nagartacce akan wan nan yarinya”.
Take kuwa yanayinsa ya canza ya koma wata sabuwar murnar. Cike da godiya ya dakko katinsa ya mika masa shi ma kuma ya karbi lambar wayarsa.
Bai fi minti biyu da bawa Mallam katin nasa ba, Sulaiman ya karaso da motar. Nan ya shiga suka tafi da Sulaiman wanda bai yi kasa a gwuwa ba wajen sanar da shi sakon Momi akan cewa suna da burin hada zuri’a da shi saboda haka zata bashi auren ko Farida ko kuma Farisa duk wadda ya ke so a ciki. Shi ma kuma kokarin tura tasa kanwar yake yi watau Aishan da ya same su tare a gidan.
Saboda kawai baya son yaci fuskarsa ya kasa gaya masa a inda ya jiye kannen nasa. Yaran da ganinsu zasu yi girman kai sabanin ita wadda ya gani ko ba a gaya masa ba, ya san zata kasance mai sanyin hali da kuma mutunta mutane. Tsaf tsarinta yayi na irin matar da yake so.
Bai tanka masa ba, sai da shi Sulaiman din yace masa “kuma yallabai you are not on the same level da ita. Exposure dinta is quite minimal”.
Ya katse shi da fadin “Iam looking for a wife not a colleague. So ni iya yadda nagan ta yai mina a haka”.
“Na sani yallabai amma ka duba sauran ‘yan uwanka. Kaga Yaya Ai is a qualified pediatrician while Yaya Rabi na san director ce a CBN. Tun da ka sha aikena wajenta. While Yaya Maryam although bata aiki na san business take yi ga kuma mijinta ambassador ne.
Kai ko Anti Bilki da take matar ambassador tayi mata nisa. Ba ka ganin kamar Zainab ba zata iya mingling da su yadda ya kamata ba”?
“Sai kuma ka manta ko kuma ban taba gaya maka ba, wacce ta haifo duk wadan nan succeful matan bata taba zuwa makarantar boko ba. But yet hakan bai hana su bata respect din da she deserve ba. Haka zalika mazansu irin matan da suke so ke nan. Ni kuwa I want a homely person for my wife. That is what I saw in Zainab ban kuma ganshi a wajen sauran da kake nuna min sun fi dacewa da niba”.
Zai sake yi masa bayani ya ce “ kaga manta kawai. Allah ya sa haka shi yafi alkhairi.
Amma a can gida kuwa ba a bin da ya faru da Zainab ba ke nan. Momi ta zageta ta kuma yi mata tijara. Ta kira ta da karuwa. Yadda ta nuna mata, ita ta ke neman Al Bashir, ba shi yace yana sonta ba. Bayan ta lakada mata dan banza duka wanda ta dan kwana biyu rabon da a yi mata shi tace mata “kuma idan ina numfashi aure iri na uwarki zaki yi sai dai kema ki koma kauye kiyi auren daka da sussuka. Amma ke da jin dadi a rayuwa har abada”.
Ku san ko da yaushe ta na da ‘yar masaniya na dalilin duka ko kuma fadan da aka yi mata amma na yau bata da idea na dalilin fadan da zagin cin mutunci da aka yi mata.
Allah sarki duniya. Momi bata san cewa ita ma Khadija mahaifiyar Zainab Allah ya yassare mata ba. Noma da suka sa a gaba da kuma kiwo ita da mijinta, Allah ya tallafa musu. Saboda ba zuwa take ba, da ta ga gidan da ya kera mata a Garkon. Noma da kiwo Allah ya sa musu albarka, ya zama hanshakin mai kudi. Kullum yana China domin shigo da sabbin na’urorin noma da injuna irin na su busar da kifi.
Hatta kifin da yake kiwo, busar da shi yake yi ana fita da shi wajen kasar nan container container. Shinkafa kuwa, ya samu hadin gwuiwa da wani babban dan kasuwa wanda ya bude ma’aikatar zazzabar shinkafa a nan garin. Da yake ya san kan noma shinkafar da aka fi sani da kilaki saboda kyawunta ya sanya kusan shine babban supplier na shansherar shinkafa ga wan nan kamfanin. Ga ‘yar kyakkyawar matarsa da kyawawan ‘ya’yansa guda biyar. Hafsa ce babba sai Sadam sai kuma tagwayen mazan su biyu da suke bi musu Ahmad da Aliyu. Sai kuma auta Anisa.
Zama ne kawai ace suna Garko. Amma gata da sutura sun kerewa Zainab sosai. Ko ba komai su har turanci suna ji sosai, saboda tsayuwar iyayensu akan haka. Sabanin ita da ta dai yi sa’ar samun karatun addini amma na boko sai a hankali. Sa’a daya tayi islamiyar tasu tana da kyau sosai, saboda haka ba’a yadda dalibai suyi Magana da wani harshe ba a harabar makaranta sai dai larabci kawai. Hakan ya sanya ta iya larabci matuka.
Sun dan samu turanci sama sama, saboda policy da ministry ta saka na cewar manyan isalamiyoyi su dinga koyar da dalibai karatu da rubutu na turanci da kuma lissafi. Ta dai dan samu abin da ba a rasa ba. Amma lissafin kam ta iya shi ko don cinikin Momi.
Ita fa ko ‘yar wayar nan ta zamani da matasa su kan rike ita bata da ita. Yar Nokia ce mai torchlight irin wadda samarin kan kira talk to me sharp sharp. Ita ma din taji jiki sai da kyauro take riketa.
Mu dawo asalin labarin. A ranar da Al Bashir ya je neman auren Zainab, a wan nan rana duk dauriya irin ta Baba Laure sai da ta suke. Bayan ta koma wajen ta ta ke cewa da Mallam maigadi watau mijinta, “anya kuwa Mallam ba zamu hakura da zaman gidan nan ba”
“Saboda me kika fadi haka “? Shima ya tambayeta.
“Wallahi Mallam na gaji da ganin azabar da matar nan take yiwa Zainab. Kullum yarinya a cikin tashin hankali zaka ganta. Ko wata baiwar tafi ‘yar nan gata”.
Cike da mamaki yace “yau kuma me ya hada su”?
“Yo ni ina na sani. Ita kanta yarinyar ba ta san me tayi ba yau tayi mata wan nan dan banzan duka. Ni dai naji tana banbanmin wai ta ga wani mai kudi tace yazo ya aureta. Har tana ikirarin in dai tana numfashi aure irin na uwarta zatayi. Shashasha ko an gaya mata auren uwar Zainab abin assha ne. ita in banda zaman birni akwai abin da zata gwada mata. Ina ce ko ni da kai zaman da muke yi ke nan a gidan nan. Ba mijin uwar ne ya roki arzikin mu zauna saboda mu dinga sa ido akan ita Zainab din ba tun lokacin da ya zo ya tambaye ka akan yadda take rayuwa ka sanar da shi rikon sakainar kashin da ake yi wa tarbiyyarta. Ya roki arzikin ka kula da ita. Akwai kaunar da ta fi wannan. Ni in ba don Zainab ba da tuni na dade da bar musu gidansu. Mata kwata kwata ba Allah a ranki”
Jin bai ce mata komai ba ta sake kallonsa tace “mallam kana ji ina ta fada ka zuba min ido kawai ba ka ce komai ba”
Sai da ya nisa san nan yace “a iya saninki kina da labarin anyi mata miji”
“Ina take da niyyar aurar da ita. Ta fi son ta ajiye ta, tana mata bauta” .
Duk da haka yayi karambani da suka hadu a masallaci da mai gidan ya kebe shi yake sanar da shi wani yaro ya ga Zainab ya kuma nemi da ya yi masa hanyar nemanta. Da baban ya tambayeshi sana’ar me yake yi, bai san ya akayi ba, sai ji ya yi bakinsa yayi subul da baka yace “gwanjo yake sayarwa a kofar wambai”.
Bayan sun tattauna da Momi shi da kansa ya nemi ganawa da yaron.
Washe gari kuwa bai yi sanya ba, ya nufi ofishin Alhaji Al Bashir. Bai samu matsala ba ya samu ganinsa. Daga yadda yaga ma’aikatar da kuma yanayin hadahadar da ake a wajen hakan ya tabbatar masa da lalle babban mutuum ne.
Conference room ya sanya aka kaishi. Shi ma kuma a can ya same shi. Bayan sun gaisa. Ya ce da shi “yallabai kana ganin zaka iyan auren Zainab a duk yanayin da ka sameta”?
“Kwarai zan iya”. Shi ma ya amsa masa.
“To zan gaya maka kadan daga cikin irin rayuwar da take yi a gidan. Idan har kana ganin zaka iya aurenta a haka to shi ke nan”.
“Mallam kaunar da na ke yiwa yarinyar nan ba karama bace. Saboda haka kar ka dauka wani batanci zai sa in ji son da nake mata ya ragu. Shi kan sa Sulaiman yayi kokarin nuna min matsayin mu ba daya ne da ita ba. Amma hakan bai girgiza ni ba. Abin da ya sani janyewa fada min da aka yi cewa an mata miji”.
“Idan nace ba ayi mata mijin ba zaka dawo ke nan”?
“Da gudu ma kuwa”?
“To kuwa akwai matsala. Saboda idan dai zaka je neman aurenta da duk wata baiwa da Allah yayi maka, matar ubanta ba zata taba yarda ta barta ta aureka ba. Amma da zan ka dan yi basaja ka ragewa kanka daraja da aji da kamar kasha casa’in da tara ka bar daya kawai daga darin da Allah ya baka, to ka iya nasara”.
Bakinsa har rawa yake yi. Yace “fada min me kake son inyi. Ko meye zan iya yinsa a kan Zainab”.
“Da kyau yanzu haka kafin in fito nayi Magana da mahaifinta kuma shi da kansa ya sanar da ni cewar ba wani miji da aka yi mata. Na kuma sanar da shi cewar wani yaro yana neman iznin aurenta. Amma fa nayi baranbarama. Domin ya tambayeni sana’ar ka nace gwanjo kake sayarwa a kofar Wambai. Idan kuma har kana son auren ta to kuwa a wan nan siga zaka je neman aure. Amma matsayinka na gota haka, ban ga yiwuwar matar uban zata bar ka, ka mallaketa ba”.
Yana fadar haka ya mike da niyyar tafiya. Shi da kansa ya rako shi yana kokarin debo kudi ya bashi, “yace masa Alhaji kar muyi haka da kai. Burina in ga Zainabu ta samu rayuwa mai kyau”. Bai jira yaji amsar sa ba ya buga mashin dinsa ya ja ya tafi.
Chapter 13 · 0% Book details