← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 43

Sashe 37

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

abin da nayi ba. Wan nan uwar taku ita ta ringa ingiza ni. Kuma na miki alakwarin sai na dau mummunan mataki akanta”. “Don Allah Daddy itama kayi mata afuwa. Duk duniya bani da ‘yan uwa da suka wauce su Farida. Tabbas kuma idan ka bata wa Momi zasu ji ba dadi. Ni kuma rashin jin nasu dadin zai saka ni nima inji ba dadi. Saboda haka afuwa ga kowa ita ta kamance mu”. “Madalla na gode da fahimtar ki Zainab. Makaranta kika koma ne ko yaya”? “A’a dadi ya Al Bashir ne yake koya min a gida. Nan kuwa ta takakrkare tana bashi labarin irin lesson din da take dauka a wajen maigidanta. Sun sake suna hira sai kawai jin sallama suka yi Al Bashir yaje ya tattago Abba da Umma domin su gaisa da mahaifin Zainab. Da sauri ya mike ya isa ga Abban domin suyi musabiha. Bayan sun gaisa suka zauna. Ita ma umma ta rusunu har kasa ta gai da shi. Hakan kuwa ba karamin dadi yayi masa ba. Shi yaushe ya isa Rumaisa ta gai da bakinsa a ladabce? Ai kawai kallon contenporaries take yi musu. Sai da suka gama gaisawa yace “kai kuma Albashir me yasa ka tattago su alhaji. Dama niyya ta daga nan ka kwatanta min gidansa in karasa mu gaisa”. “Ai Dadi main house din is adjacent to nan gidan “in ji Zainab. Umbola yayi musu da hannunsa yana fadin “kun ci gidanku daga ke har mijin naki. Kuma shine tun da na shigo ba zaku sanar da ni ba”. Dariya kawai suka yi. Ganin sun ware da hira ya sanya umma mikewa ta koma gida yayin da Zainab ta shiga kitchen. Bayan ya raka umma ya dawo kuwa a nan kitchen din ya sameta. Run gomota yayi jikinsa yace “yaya surprise din nawa how much is it going to be worth”? “hajj da Ummara” “Na riga naje na sake zuwa”? “sabuwar mota latest”. “not interested”. “a delicious meal”. “not good enough”. “to gaskiya ban san me zan baka ba” ta fada with disappointed look on her face. “Ni zan fadi me nake so. I just want a memorable and wonderful time with you tonight”. Ya na mai dada rungomata jikinsa. Itama sai da ta dan yi masa peck a kuncin sa, san nan tace “ka samu ka gama. Amma yanzu barni in samu in hadawa su abba dinner. Don naga yadda suka yi relaxing suna hirar siyasa ban ga lokacin tashin su ba”. Kamar kuwa yadda ta fada haka ce ta kasance. Ba su iya tashi ba sai da suka ji kiran sallar magariba. Dadi ya mike hade da yi musu sallama, akan daga masallaci zai wuce gida. Ba yadda basu yi ba ya dawo yayi dinner amma yaki. Al Bashir ya kalleta yace “implement plan ya Maryam”. Nan kuwa aka shiga neman makullin motar dadi ba a ganshi ba. Ganin zasu rasa jam’I ya sa suka hakura. Ko da suka dawo kuwa ta shirya musu abinci a tsakiyar falon su uku. Da mijinta da surukin ta da kuma mahaifin ta. An kuwa yi masa haka da sunan yaci abinci ita kuma zata ci gaba da duba makullin. Suna gamawa kuwa Al Bashir ya zaro key daga aljihunsa yana fadin “ashe Dadi kaga key din ni na saka a aljihuna na dauka nawa ne”. Dariya Abba yasa yace ‘ya’yanka sun yi tricking dinka”. “ai abba idan ba haka nayi masa ba zai zauna ba. Idan kuma yaki cin abincin gidan mu na san yau Zainab sai tayi kuka”. “ja’iri kai kuma da kukan nata gwara ka bata ran naka baban ko”? in ji Dadi. Yana sosa keya yace to ai dadi a hudubar da kuka yi min kunce a dinga kyautata yi musu. Kuma na dauka yin abin da zai hanasu kukan yana daga cikin kyautatawar”. “Ai kaga wan nan dan naka ba zaka kashe shi a Magana ba. Shi yasa customers dinsa kance in dai ya tsara ka ba yadda zaka yi sai ka sai kaya a wajensa”. Shima Abban ya fada. A nan dai har isha sai da yayi. San nan yayi musu sallama ya wuce. Ko da yaje gida kuwa bai tarar da momi ba tayi ficewarta gidan bikin da tayi niyya. Tun da dama a koshe yake dakinsa ya shiga ya kwanta. Mallam nema ya sanar da shi cewar ga kaya a bayan motarsa. Bayan ya shigo da su, yaga turarruka designer guda uku masu tsadar gaske da kuma variety package na shayin Tertly. Yana gani ya san aikin su Zainab ne. Da kuwa ya buga yai mata godiya ita bama ta san da wan nan sakon ba. Mika masa wayar tayi.yana fara godiya kuwa ya katse shi da fadin “dady kayi hakuri ka barni in samu cikakken ladan kyautatawa iyayena. Wan nan itace matsalar ka yi ta ingiza mutum just to destroy a relationship. Su kuma parties involve su zo daga baya su fahici juna su kuma yafewa juna because of strong bond da ke tsakaninsu, kai kuma ka kwana ciki da jin kunya ga kuma repercussion na ayyukan ka da kuma pay back da tabbasa sai ya zo maka. [8/9, 14:01] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 32 BY HANNE ADO ABDULLAHI Bayan DR Abdullahi, ya samu ya daidaita da Zainab abu na gaba da Dadi ya yi shine sasantawa da mahaifansa. Suma kuwa ya taka har kauyen yaje ya basu hakuri na irin abubuwan da suka dinga faruwa. Ya dauka da ya ke ganinsu a ‘yan lokutan da yake lekasu komai kalau ya dauka sakon da yakan bawa Rumaisa ne ke isa wajensu, sai a ranar suka sanar da shi su kan ba don mijin tsohuwar matarsa Khadija ba to da sun dade da mutuwa da yunwa. Tabbas sunje Hajji, amma ba kujerar da shi ya basu ba. Wadda abban su Hafsa ya bayar ce, wanda shi kuma bai taba raba hidimar da ya kan yiwa gidan mahaifan matarsa da kuma na aminin mahaifin nata ba. Mallam Usman kuwa na zaune a falonsa yana lissafin cinikin kayan gonarsa, kanin Hafsa faruk ya shigo ya fada masa ana sallama a waje. Yayi mamaki kwarai ganin mai sallamar. Duk da bai san da wacce ya zo ba, amma ya yi masa tarba ta mutunci, an sauke shi da karramawar da duk wani bakon arziki ya cancanta. Yanan sauraron yaji ta ina zai soma tashin hankali sai kuma ya ji sabanin haka. Hakuri ya dinga ba shi na yadda ya gudanar da al’amura tsakaninsu da farko. Shi ya nuna masa dama bai rike shi da komai ba. Bayan nan kuma ya dora da yi masa godiyar nauyinsa da ya taya shi dauka, saboda shi ya banzartar da shi. Da kansa ya shiga cikin gida ya kira yaran suka gaisa. Shi kansa yaran da’arsu ta birge shi, sai fadi yake “yanzu duk wadan nan nakane”. Ya sake nuna Hafsa yace “ita dai wan nan bata da maraba da Zainab. Ina ga kamar Khadija suka dauko”. A dakin Khadija kuwa sai da ya sha daga da ita kafin ta fito su gaisa da tsohon mijinta. Shima a dofane suka gaisa kamar mai daukar wuta. Bayan yayi masa sallama ya tafi, Mallam Usman ya koma cikin gida yana ganin yadda Khadija ke cika tana batsewa ita ala dole an yi mata laifi. “Wai fushin na meye”? Ya tambayeta. “Kawai tilastani da kawai zuwa gaida wan nan mutumin”. “Dijangala tawa. Da kin san irin dauriyar da na yi kafin in barki zuwa wajensa da kin sara min. saboda Zainab kawai na barki kuka gaisa, saboda na san idan taji yazo baku gaisa ba, ba zata ji dadi ba. Amma in bani ba bakauye wake hada tsoffin masoya a guri guda”? Da tsananin mamaki ta juya ta kalle shi tace “yanzu da wannan tsufan nawa har kake kishi”? “ke kike ganin kin tsufa. Amma ni har yanzu a dan dasheshiyar yarinya nake ganin ki a gabana, na ga dai sakacina da ban saki kin daura nikab ba”. Ita dariya ma abin ya bata. Tun daga wan nan lokaci kuwa zumunci ya kullu tsakaninsu. In dai zai shiga wajen iyayensa ya kan tsaya su gaisa, har kuma da tsarabar yara. Shi ma kuwa haka zai sa a loda masa kayan gona a motarsa. Dadi kuma yanzu ya mai da ziyarar kauyensu kusan duk karshen sati, sai yanzu ya dade gane illar da Rumaisa ta yi masa. Bata barshi ya kyautatawa kowa ba sai ita da ‘yan uwanta da kuma ‘ya’yanta kawai. Tun da kuwa ya dawo kan turbar arziki zaman lafiya yayi kaura a tsakaninsu. Ana ciki haka rashin lafiya ya sanya shi kwanciya a asibiti. Likita kuwa yayi bayani rashin cin abinci da kuma cin wanda ya dace da yanayin ciwonsa shi ya janyo masa wan nan larura. Zainab ta bashi kulawa matuka, saboda momi tafiya ma tayi wai tana da seminar. Nan kuwa karya take. Wata kawarta ce akayi wa mijin minister, shine suka tafi bikin taya su murna. Daga nan kuma ta tsaya hutuwa. Ita kuwa Zainab tun da taji haka ta daukarwa kanta, aika masa da abinci ofis mai rai da lafiya. Haka zalika ta roki Malam da ya bar Baba Laure ta dawo saboda kula da abincin mahaifinta kawai. Ya yadda amma ban da aikin kwana. Za dai tazo karfe goma na safe tayi dan abin da zata iya, saboda ita dai mai girki ce kawai ba ruwanta da shara da goge. Hakan ya mai da gidan kazamin gida. Da can saboda samun lafiyayyen abinci da kuma tsaftar muhalli kullum jama’un momi na gidan. Amma zuciyar gidan na tafiya sai suma suka daina zuwa. Haka zakaji gidan shiru kamar ba mutane a ciki. Shi Dadi baya shiga sabgarta kwata kwata, saboda jin haushin abubuwan da ta sanya shi yayi a baya. Ita kuwa hakan bai wani damunta. Balle dake an canza mata boss din office dinta, sai fantamawa suke a dukiyar gwamnati. Bata neman komai a wajensa bata ga kuwa dalilin da zata bata lokaci yi masa biyayya ba. Gaba daya dadi has lost control of his house. Ana cikin haka tenure sa as Commisioner ta kare. Ga kuma ciwo da ya sa shi a gaba. Ciwo kuma mai dan
Chapter 37 · 0% Book details