← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 43

Sashe 10

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

[8/6, 23:14] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨‍👧👨‍👧👨‍👧👨‍👧 IN FIKI A MIJI💑💑💑💑 Page 11 BY HANNE ADO ABDULLAHI A gajiye tikis Zainab ta iso gidansu saboda ga gajiyar aiki ga kuma ta hanya da ta sharo ta a kan takalminta. Amma ganin motar Sakina a gidan ya sanya taji gajiyar tata ta wartsake. Ta kofar baya ta zaga tana kokarin sulalewa ta gudu dakinsu saboda bata san abin da ya kawo Sakinan gidan ba. Tana kokarin hawa benen karaf Farisa ta hango ta. "Momi ga munafuka ta dawo. Na kamata tana kokarin gudu ta buya". Farisa ta fada cikin daga murya. Kafin ta gama hada da kuma fassara maganar Farisa sai kawai taji Momi ta rufe ta da duka tana cewa "shegiya tsinanniyar karuwa. Idan tambadewa kike sha'awar yi ba sai kin je kin nemi mijin Sakina ba ki shiga kasuwa da gaske har da kudi zaki samu". Ranar ta sha duka da zagi. Sabo da daga kafar bene Momi ta jata har falon gidan inda suka zauna ita da 'ya'yanta suka kare mata cin mutunci bana wasa ba. Ita dai in ban da kuka ba abinda take yi. Shigowar Halim da baby Amra 'yar wajen Sakinan shi ya katse taratsin masifar da ke saukarwa Zainab. Sai kuka yarinyar take tsandarawa kamar za a cire mata ido. "Kai Halim ina ka dauko Amra"?momi ta tambaye shi. "Uncle KB ne ya kawota yanzun nan yana waje ". Momi tabayar da umarni a shigo da shi. Daidai zai shigo Sakina ta dada narkewa ita als dole an cuce ta a bi mata hakkinta. Cikin gatsali ya gai da momin san nan ya juya wajen matarsa yace "ke kuma da kika fito ki ka barta yaya kike son in yi da ita". Itama cikin tsiwatace "ai na dauka ka samu inda zaka kaita". Dariya yayi san nan yace "aiwai ke nan yaji kika yo. Wan nan kuma ya rage nake. Dama alfarma zan yi miki saboda korafin da kike min na yawo amma tun da kin fi son haka sai mu ci gaba". Momi ta katse shi da fadin "yanzu Kabiru a gabana kake fadin irin wadan nan maganganun"? "Ah to Momi ni meye laifina. Idan dai macen bata kai ta rikeni ba ai ni kuwa zan nemawa kaina mafita. Na ga wanda zata iya rikeni tace ba haka ba sai kuwa tayi hakuri da yadda ta sameni". Kafin Momi ta gama hadiye mamakinta ya mike yana fadin idan kin sauko kya iya karasawa gida idan kuma kin san ba zaki koma yau ba nima in nemi wajen kwana". Daga nan bai kara cewa komai ba ya mike yayi tafiyarsa. Da farko Sakina taso itama ta dan ja ajinta amma Momin ta nuna mata shi wan nan gabon mijin nata sai dai su bi shi a hankali. Saboda ko ba komai akwai shi da sakin hannu. Mutunci ne kawai ba shi da shi. Haka ta dauki borin kunyarta ta koma. Wan nan abu da ya faru bai kuma sa ta ragewa Zainab duk wata hidima tata ba. Sai dai fa akwai close marking. Duk yadda zata hana Zainab haduwa da Kabiru tana kokarin yi. Ita ma kuma Zainab din ba son haduwa da shi take ba. Saboda indai zai ganta sai ya yaba wani abu a jikinta. Ga shi dai a lullube take amma hakan bai hana shi rike memory da ya gani ba. Ana haka Farida ta samu tafiya Sudan ita da Farisa. Ita Farida ta samu medicine yayin da aka bawa Farisa computer scince. Ita kuwa jakar gidan tana nan. Shekarar farko da zasuyi sauka zaman gidan Sakinna ya hanata. Bayan wata shida aka sake yaye wasu daliban da suka fadi screening na farko aka basu damar sake maimatawa aka saka da ita shi kuma daddy ya hana ta kudin sauka a dalilin Momi ta ce masa yasayyadin ne saurayinta shi yasa ya saka sunanta amma ba abin data sani. Haka tana ji tana gani ta sake maimaita wata shekarar. Ga kawarta Fatu ita har ta samu shiga Legal ita kuwa tana nan tana fama da hidimar Momi da ta su Sakina. Raguwar 'yan gidan ya dan rage mata aiki balle da su Halim ma sun girma suma ba sa tasowa sai biyar na yamma. Hakan ya sa Momi ta dada habaka sana'arta ta snacks. Shekarar su Farida daya a sudan, Momi ta debe duk yarsn gidan suka kai musu ziyara daga nan ta dauke suka karasa Saudiyya suka yi Ummara san nan suka je Turkey da England yawo. Saboda Momi ta kwashe wajen wata bata gida sai hakan ya bawa Zainab dama shiga wajen Mama Hajjo watau mahaifiyar kawarta Fatima. A nan ta dada karuwa da darussan rayuwa. Saboda Mama Hajjo macece mai hikima cikin wasa da dariya take nusar da su abin da ya dace da rayuwarsu kamar irin su mu'amala da iyaye da kuma dangin miji da shi kansa saurayin idan an same shi har kuma ya zuwa lokacin da zai zama miji. Ha ka zalika nan ta sake kwarewa da gyara irin su lalle da halawa da dilka. Ita kanta ba ta san ta tana da talent na zane ba sai da ta zanawa Fatu lallen rasma idan kagani sai ka dauka a saudiyya aka zani shi. Haka nan ta ci gaba da kasancewa lokaco lokaci Momi zata debi sauran yaranta har su Bilki dake gidajen mazajensu su kaiwa 'yan sudan ziyara daga nan su wuce yawo kasashen duniya, amma banda Zainab. Saboda idan ta tafi da ita harkar cinikinta zata tsaya. Kuma yadda ake cinikin snacks tana nan haka ake yinsa ma in bata nan. Kusan in bata nan ma kudi sun fi taruwa saboda babu mai ci sabanin idan yaran gidan suna nan. Sai da su Farida suka dauki tsawon shekara uku a Sudan san nan suka zo hutu saboda IT da za suyi a kasar nan. Biliki ce ta sake haihuwa ta biyu ke nan. Dukkan su suna gidan. Yan boko na kwance a kujerun falon suna ta latse latsen wayoyinsu yayin da ita kuma take ta kai da kawowa na ganin tsaftar gidan da kuma abincin da za a ci ya kammalu. Uncle Sulaiman ne ya fito daga dakinsa da hanzari rike da waya yana amsawa a dan firgice yana fadin "gani nan zuwa yallabai". Sai da ya kashe wayar san nan ya ya juya wajen Bilki yace mata "mai gida na ne ya zo mana barka". San nan ya fice da hanzarinsa ya shigo da shi. Yadda suke kwance a kujera ko zaman su ba su gyara ba. Haka zalika rawar jikin da Sulaiman yakeyi ta kokarin martabar bakon bai shalle su ba. A yangace kowacce ta dago kai ta kallashi. San nan aka yi masa gaisuwar ya kake. Shi ma da lafiya kawai ya amsa musu san nan ya mai da hankalinsa wajen gaisuwar ban girman da Bilki da Sulaiman suke masa. Ita Bilkin ce ta sake mikewa ta shiga kitchen Farida da Farisa su na nan a yadda suke. Sai faman latse latsen waya suke ta faman yi. Ba ta fi minti biyu da shiga ba Zainab ta shigo falon dauke da dan madaidaici tray wanda ta dora jug da kananan kofuna guda biyu da kuma robar ruwan swan. Sai daga gefe dan side plate ne data rufe da foil paper. Kamar ko da yaushe sanye cikin dogon hijabinta wanda ya kusa rufe idon sawunta. Cike da natsuwa ta karasa kusa da shi ta jawo side table ta dora tray a kai san nan ta russuna daga gefensa tace "barka da yamma". Sautin muryarta kawai ya sanya yaji duk wata jijiya ta jikinsa ta amsa. Take adduar da yake korawa baby Musty ta makale a bakinsa. Da kyar ya daure ya amsa mata da cewa "barka kadai". Bata lura da yanayinsa ba ta jawo tray gabansa ta zuba masa ruwa a kofi daya dayan kuma ta zuba masa matsattsen lemon zaki san nan ta dan kware gefen side plate din da ta rufe da foil samosa da meat pie suka bayyana. Wai tas Mallam Al bashir ya manta da azumin litinin da alhamis da yake yi ya kaiwa abincin nan attack saboda kawai ya manta da komai in ban da kyakkyawar fuskar Zainab. Yatsun hannuta zara zara su suka dada mantar da shi komai sai kokarin shan lemu da ta zuba da su. Ba tare da ta lura da yanayinsa ba ta mike ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta. Sai da ya cinye meatpie biyu da samosa uku ya kuma sha lemu kofi biyu san nan ya tuna yau ya dau azumi. Yaran nan suna kallo tunda bakon nan ya shigo maigidan yake mazari a gabansa amma hakan bai san sun gane darajar da bakon yake da ita ba. Shi dai Albashir yayi musu barka. Amma fa rabin hankalinsa na ga son sake ganin baiwar Allah nan da ta shayar da shi lemon da bai taba jin mai dadinsa ba a rayuwarsa. A lokacin da ya shigo masu gidan basu dade da yin lunch ba saboda lokaci ya nuna wajen karfe biyu da rabi. Zainab tana shiga kitchen tayi sauri ta dora nama da busasshen kifi da stock fish a pressure pot. Ta dauko kazar gidan gona guda daya ta wanke ta mutssuke ta da kayan kamshi da su maggi ta dora mai ta hau suya ba tare data tafasa ta ba. Da ta gama da jar suyar ta kwashe ta zuba a food flask. Zuwa lokacin abin da ta dora a pressure pot ta san ya nuna ta bude ta zuba jajjagen attarugu kadan da tumaturin leda sai da ta bari ya dan bararraka san nan ta wsnke ganye ugu da bitter leaf kadan ta zuba a kai ta kuma watsa agushi a ciki ta rufe tukunyar. Ta dauko guntuwar doya. Miya na sauka doya ta dahu ta buga masa sakwara. Duka duka bata fi 40 minutes a kitchen ba sai gata da wani tray din da su plate da serving spoon ta dora kan dining. San nan cikin san yin murya ta juya wajen Bilki tace "Anti na gama". Nan dai maigidan ya ja bakonsa dinning. Shi kuwa bakon yayi wa abincin nan ci mara algus. Da kyar bayan la'asar shi ma don kar masu
Chapter 10 · 0% Book details