Sashe 38
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karen tsada. Don ma Zainab ta tsaya akan magani da kuma abincin da zai ci. Yanzu auren zainab da albashir ya doshi kimanin wata takwas. Tana kuma da ciki dan wata biyu wanda daga ita har shi ba wanda ya san da shi. Kyau ne dai tayi shi har ta gaji. Ni kaina idan na ganta mamakin irin kyan da kullum ke karuwa a tare da ita nake. Ga sana’ar da take yi ta catering services wanda bata hulda da kananan mutane sai manyan yara. Saboda fiye da rabin customers din nata daga sashin dangin mijinta ne. balance din account din ta kuwa sai hawa kawai yake amma baya sauka. Saboda ko da wutsiyar ido ta kalli abu da sunan ya burgeta to kuwa Albashir zai tabbatar ya zama rabonta. Nauyin danginta kuwa wani lokacin sai dai idan sun zo godiya ta samu labarin alkhairin da mijinta ya aiwatar. Saboda haka sai ta mai da hankalinta kan tallafawa ‘yan uwanta masu karamin karfi. Amma inda kasan bata daukar ko kwabo haka balance din account dinta yake. Monthly allowance dinta wanda ko goro da kudin kitso bata saya da shi 300k ne. A kwai ranar da suka je saloon ita da Meena. Duk saurinta kar ya dawo bai same ta a gida ba sai da hakan ya gagara. Saboda shidai ita ke nan dokarsa. Duk inda zata ya amince mata, amma fa ta tabbatar ta riga shi dawowa. Ya tsani ya shigo gidan nan bai yi tozali da ita ba. Amma ranar akwai mutane a saloon din hakan ya sa bata gama da wuri ba. Ta main house suka bi. A falon umma ta tarar da shi. Yana ganin su ya rufe Meena da fadan da ba ita ta cancanta ba. A dan fusace yace “ke meena ina kukaje tun azahar sai yanzu kusan magariba kuke dawowa gida”. “uncle AL B salon muka je aka gyara mana gashi”. “a salon din ne kuka dade. Duk wanke kai yana haura minti uku ne? kun dai tsaya hira kawai”. Dariya Meenan ta saka tace “to ai gashin anti Zee shi yafi bada wahala saboda tsayinsa. Tana sama da awa daya acikin dryer bai bushe ba”. Ita dai bata kula su ba saboda ta san fadan nata ne ganin Umma ya sa shi ya wayance da yiwa Meena fadan. Sai kawai ta sulale ta shiga kitchen din Umman. Nan kuwa ta tsaya ta hada musu dinner. Bata shiga gida ba sai bayan isha. Ta riga da tayi wayon da duk randa ta san ta yi masa laifi to kuwa ranar kwalliyar ta, ta daban ce. Haka zalika kwarkwasa da tarairaiyar da za ayi masa daban ce. Kwalliya ta rangada da kananan kaya, wanda suka dada fito da tsarin halittar ta. Tana jin alamun yana kokarin shigowa tayi saurin sakkowa daga sama. Da ya kalleta sai da ya kusan shidewa. Sai kuma ya tuna ya kamata ya dan nuna fushinsa, sai ya dan dake. Murmushi kawai ta yi saboda both the first and the second reaction ta gansu. “sannu da shigowa” kawai tace da shi. Shi ma a dan dake ya amsa da yawwa. San nan ya nemi kujera a falon ya zauna. Kitchen ta shiga saboda ta lura kamar bai ci abincin sosai ba, ga kuma dare bata son ta bashi abinci mai nauyi. Saboda haka pepper soup na ragon ruwa ta shigo da shi cikin bowl. Center table ta jawo ta dora akai. A kan kafarsa ta zauna, sai da ta marabce shi da kyau na kusan minti uku san nan ta janye bakinta daga nasa. Ajiyar zuciya ya saki yace “kawai don kin san bana iya fushi dake shi yasa kike min abin da kiga dama”. “Allah ya huci zuciyar ya Bala na. da iznin Allah ba za a sake maka wan nan laifin ba”. “ke don baki san yadda nake ji bane idan na tura kofar gidan nan ban ganki kin zo tarba ta ba. Sai in ga gidan ya yi min baki”. “in dai haka ne daga wan nan an daina zuwa salon dinma tun da ran yaya na baci yake. Ko kuma ayi wa kan kwas kwas saboda yana neman shiga tsakani na da rabin raina”. Sai da ya saki murmushin mai nuna alamun fushi dai kam ta sauke shi, san nan ya kai hannunsa ya dada shafo gashin yana fadin “a bar min abina, saboda kallonsa yana sakani annashuwa. Idan na shafa shi kuwa har cikin zuciyarta nake samun natsuwa. Amma dai ki taimaka min in daina shigowa gida ban same ki ba”. “in Sha Allahu an wuce wajen”. “yawwa Putri na. yanzu me kika kawo min”? Bata bashi amsa ba, sai dai spoon feeding din shi data shiga yi. Bayan ya gama ta dakko gwanda data yanyanka kanana tana bashi. Washegari kuwa ta sakko ta tarar ana gyaran dan wani daki a gefen dakin masu aikinta wanda dama dakuna biyu ne. ita dai bata san me ake yi ba. Ta dai ga plumber da electrician suna aiki. Akaja ruwa aka sa Ac aka fenta dakin. A week later cargo ya iso gidan, sai kawai gani tayi ana installing su hair dryer da su steamer kayan pedicure da dai sauran kayan da akan samu a hadadden salon. Ana gamawa ya leka yace Putri ga salon nan bana son kina sharing items da wasu”. Sai ya zamana har su yaya Ai nan suke zuwa su da yaransu. Every weekend zasu daukko mai salon da suke zuwa ta yini a gidan sai ta gama da su dukkansu. Bayan wan nan ya nemar mata online karatu a university ta Madina. Zata dinga daukar karatun ta online sai kuma karshen kowacce semester ta je ta rubuta exams ta dawo. An gama da wan nan sai ga su farida sun zo hutu, wanda ita farisa ma ta gama. Ita Faridan ce, ke da sauran shekara daya. Tana dira kuwa washegari a gidan yayarta ta wuni. Tayi murna matuka da yanayin da ta samu ‘yar uwar tata a ciki. Sabanin Farisa da ke kallon komai a wulakance kamar ta ga kashi. Suna cikin hira ta ce “anya yaya Zee ba komai a tare da ke kuwa”? Tareda mamaki tace “ban gane ba komai a tare da ni ba. me kika gani”? “eh to ni dai to me you look pregnant. When was the last time ya had your period”? Ta daga kai sama tayi shiru alamar tunani. “kar dai kice min you cant remember”? “gaskiya na manta. Ko two ko three months back”? Cikin dariyar tsokana tace “gaskiya you are having good times da yayan nawa. Tun da har lissafi ya bata”. Dukan wasa ta kai mata tace kin rainani”. Da ya dawo kuwa ba tare da ta sanar da shi suspicion din kanwarta ba ta sa shi ya kaita asibiti nan kuwa labari mai dadi ya same su. Sai kuma ya nuna da dai ta hakura da karatun tun da ga wan nan ya gifta. Rigima har gaban Umma, inda ta sasanta su da fadin yayi hakuri idan anga tana shan wahala sai ta tsaya da karatun. Haka ta soma daukar lectures dinta on line, in da zata samu degree a Islamic philosophy. Wanda kuma saboda zurfin karatun data samu a sanawiyyar da tayi, shekara biyu kawai zata dauka ta hattama karatun nata. Farisa dai ta samo Salim ahmadu Salim. Babban yaro dan gidan senator Ahmad salim mai shunku. Ba shine babba ba. Amma shine babba a wajen amaryar da shi senator yafi so. Matarsa ta fari ‘ya’yanta takwas duk mata ne saboda haka Sharifa na zuwa ta fara da haihuwar maza, wanda sai da ta haifi hudu cif sai ta karbe gida. Ita kuwa hajiya Bilki tuni ya mayarda ita bola ita da ‘ya’yanta. Ba ruwan sa da su. Dan teaching din da take yi shi ke rike da ita. Ita dai tana zaune a bangare guda na gidansa. Ita ba matar aure ba ita kuma ba sakakkiya ba. Sashen nata ma idan ka gani zaka dauka na masu aiki ne. ta rungumi kaddararrta ta barshi da halinsa shi da matarsa. Tun da Salim ya tashi dan gata ne lamba daya irin gatan nan mai illah. He is very arrogant. Ba wanda ya isa ya sashi ba wanda ya isa ya hana shi. Ita kan ta Farisa Allah ne yayi wan nan auren nasu. Yayi yawon karatu kasashe kafin daga karshe ya hakura da zama a Sudan saboda ya taba dukan wata budurwa har ya kusan kasheta aka yi masa denying visa into Europe gaba daya. Asia kuma an kama shi da drugs a Thailand da kyar baban ya fito da shi suma suka bata passport din shi. Da kyar aka samu ya tafi Sudan din, inda kuma a nan suka hadu da Farisa. Suma relationship din nasu kamar ba zai kai labari ba. Saboda haka zasu kwashi adashin tsiya ya kamata ya lakada mata duka. Ayi baram baram. Amma kwana biyu sai kuma ka gansu sun dinke kamar ba su ba. Tarbiya dai kam babu ita a tare da shi. Abin da duk yake so shi yake yi saboda uwar da uban sun jika shi fiye da zaton mai karatu. Basa taba ganin laifinsa. A Thailanda da aka kama shi da cocaine, Allah ya sa bata kai commercial quantity ba, amma duk da haka uban ya kashe sama da dala dubu hamsin kafin ya samu aka sako shi. To wan nan shine mijin da Farisa ta samu. Ita kuwa Farida ba wanda ya taba zuwa da sunan ya gan ta yana so, ko da samarin makaranta. Har aka sa rana Zainab bata da masaniya, balle da ke dadi ya ce ba ruwansa duk abin da ya faru Momi ita zatayi kuka da kanta. Bincike kawai ya nuna yana son yi akan yaron ta harzuka tana gaya masa maganganu har tana cewa bakin ciki yakewa ‘yarta saboda baya son kowa ya kamo Zainab, tun da yanzu itace a gaban goshinsa. Saboda haka a kyale mata yarinyarta itama ta auri mai arziki. Hakan kuwa akayi. Nan kuwa ta fantsama shirin biki. Da aka tashi aka basu wani makeken gida sai da kuwa ta cika falika uku da dakuna shida da kaya. Kaya kuwa na alfarma. Ga kuma hidimar biki da aka tsunduma. Zainab