← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 43

Sashe 40

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka sai tayi almubazzaranci da kudin hannunta. Liki ma kawai ranar dinner gidan maza ta lika sama da 300k. Washe gari kuwa da za akai garar nan bata da ko dubu dari a tare da ita. Tana cikin wan nan tashin hankali ne sai ga sakon surukin Zainab ya iso. Momi ce ta sa Farida ta sanar da Zainab labarin wan nan sakon sai dai kuma babu kayan dangin ango. Tayi maula by stle. Da kuma an kawo tace bata so. Zainab bata yi fushi ba ta je ta sayo super goma Holland goma da shadda getzner guda goma. Albashir ne ya debo wasu shaddoji presidenta da ya sayo wa kansa suma goma yamika yace “gashi nan ba dan halinta ba kar azo ana yi wa 'yarta gori”. “kai Ya Al B. ni Kenan gori ka ke min na rashin zuwa da gara”? Sai da ya jawo ta jikinsa san nan yace “ai ni dake Putri bamu yi auren don abin duniya ba. Baki aure ni don kudi ba haka nima banyi neman aurenki da kudi ba. Soyayyace zalla da mutunta juna a tsakaninmu. Kuma ke baki san irinki, idan ma da bashi a kanta aka kawo wa miji da gudu zai karba, ya kuwa dage kodago don ya fanso ki. Don a lokacin dana ke nemanki ko faskare akace in yi saboda ke zan yi shi, balle sai da gwanjo mai sauki”. “To naji ya Bala mai gwanjo dan bani excuse inje kai garar nan”. Dada narkewa yayi a jikinta yana fadin “saboda Allah naje daurin aure kinje yini kinje dinner kin kuma zuwa wadda iska ta wargaza, amma duk da haka sai kin kuma fita yau”. Itama murya cike da shauki tace kayi hakuri. Nayi ma alkwarin da wuri zan dawo”. “Ni ba wan nan damuwata ba kar kije iska ta dauke min ke. Kin ga ba wani nauyi ne dake ba, san nan …….” Dukan wasa ta kai masa ya goce cikin dariya. To sun kai gara, amma fa sai da aka yaba musu bakar Magana, saboda sun yi lefe akwati ashirin suna expecting gara sama da haka. Momi dai aka dawo ana bata labara bakin ciki kamar tayi yaya. Duk yadda taso tsara bikin ba haka yazo mata ba. Ga shi anji jiki, kuma kususu ba riba, saboda ko kwatar abin da aka kashe ba a samu ba. Komawar yara makaranta ma sai da taci bashi suka koma, saboda Dadi yace ba zai kara ko kwabonsa ba, saboda ya bata kudin komai nasu ta narkar da su a bikin nan. Balle dama ya dada jin haushin labarin da ya samu a wajen Mallam ya dada bata masa rai. Shi ya shaida masa yadda akayi neman auren Zainab da kuma shawarar da ya ba wa Abashir na yayi basaja, da kuma irin yadda rayuwar Zainab ta so baci a sanadin rashin sa ido da aka ringa yi mata. Dadi yayi nadamar rashin sanya ido a harkar gidansa kwarai da gaske, wanda kuma shine major problem din mazan yanzu. Sun dauka in dai sun tafi nema shi ke nan hakkinsu ya tsaya daga nan. Sun dauka wadata iyali materially is all that is needed. Su bar mata suna son ransu. Allah yasa mu dace. [8/9, 14:19] +234 814 948 5104: FINI A UBA👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 34 BY HANNE ADO ABDULLAHI Haka dai Zainab taci gaba da yin rayuwarta cikin jin dadi da walawala. Ga tsananin kauna da mijin ke nuna mata. Ga kuma yadda mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwansa ke tattalinta. Ko da auren Fatu ya tashi wanda kuma shi ya hada auren nata da daya daga cikin abokansa, shi yayi mata komai na hidimar auren. Mama Hajjo saboda tsabar murna ta kasa yi masa godiya, sai dai da sun hada ido ta fara hawayen murna. Ga kuma gallalen mijin da ya hada ‘yarta tata da shi. Farisa kuwa tana zaune a gidan mijinta. Duk da dai zaman nasu ba wani dadi ne da shi ba. Yau fari gobe tsumma. Kusan duk waanda ya kamata ya sa baki ya gaji da shari’a a tsaakaninsu. Shi ba shi da hakuri ita kuma bata da kunya. Idan fadan su ya tashi haka zaka gansu kamar ‘yan daba har da fashe fashe. Duk kayan alatun da aka narka musu sun farfasa su. Haka nan idan ya. debi cakunsa zai zo kan dan abu kadan ya rufe ta da duka. Ga dai gidan hutun nan an samu an shiga, amma fa rai da jikin ba su huta din ba. Barinta uku na sanadin dukan da yake mata. Sai kuma daga baya ya dawo yana bata hakuri. Ita kuma tsabar sonsa haka zata hakura. Balle da ta gwada nuna wa Momi halin da take ji bata dau wani mataki ba ita dai burinta ta binne zancen kar Dadi da kuma sauran mutane suji suyi musu daraiya. A hakama kuwa gwanda ita da Sakina. Saboda ita auren ma ya gagara gabadaya. A yan shekarun nan auren ta hudu. Ga ta da saurin samun miji, amma fa bata dadewa auren ya ke karewa. Aurenta hudu.’ya’yanta hudu kowa da ubansa. Zaman gidan Momi ya gagareta saboda last auren da Dadi ya daura mata sharadin daya gindaya mata ke nan. In dai ta fito ba gidansa ba. Haka ta hakura ta koma birged gidan ubanta da zama. Nan kuma suka dasa da matar uba. Kullum cikin tashin hankali. Zainab kuwa bata da matsala. Karatun ta take cikin kwanciyar hanakali. Idan lokacin jarrabawa yazo mijinta ya saka ta a gaba suje ta gama jarrabawa su dawo tare. A haaka har ta gama degree dinta tana goyon ‘yarta mai sunan Ummansa suna kiranat da Amma. Dai dai ta gama degree ne kuma a lokacin bata dawo ba, Farida tayi zuwan hanzari daga Sudan. Haka ya faru ne sakamakon shayen shayen da khalil ya sanya kansa a ciki. A daure aka sako shi a jirgi a haka kuma ta shiga dashi gidan. Dadi yayi tsanannin bakin ciki da wan nan abu. Take kuwa jininsa ya hau ya yanke jiki ya fadi. Sanadin samun stroke dinsa ke nan. Momi saboda kawai bata son kowa yaji ta kaishi psychiatric ta sa aka kulle shi ta manta da shi a a wajen. Halinta ne ya sanya kusan duk matsalar ‘ya’yan wasu a bakinta zaka ji tare da kuma nuna sakacin iyayen na abin da ya samu dansu. Kullum ita ce kadai ta iya tarbiyar yara, to yanzu da abin ya zo kanta, sai ta ke kokarin boye tata wutar mai dan Karen hayaki. Abin da bata sani ba, ba ma acan ya koyi shaye shayen ba, tun a nan yana yi. kusan kuma duk wanda ke tare da ita ya sani itace bata sani ba. Saboda haka da wan nan ya faru sai take ganin ba wanda ya sani. Ba ta san tas asirin ta a bude yake ba. Inda ma kuwa ta dinga tallata na mutane haka itama aka dinga tallata nata. Amma wan nan yanzu ba shi ne damuwarta ba. Maitaining status dinta a society shi ya dameta, saboda ko ba komai yanzu Dadi aljihunsa yayi kasa. Ita kuma bata yi niyyar ritaya daga karyar da ta daukar wa kanta ba. Nan kuwa ta likewa wata kawarta da akayi mijin senator akan zai samo mata aiki a Abuja. Kullum tana zirzirga zuwa can. Har dai tayi sa’ar samun aikin. Ta kuwa tattara ta yi gaba abinta ta bar dadi da su Halim su kadai a gida. Sai kuma Khalil dake kulle a asibiti ko mai zuwa duba shi babu. Wan nan tafiyar da Zainab tayi ta dan dade bata nan. Kuma duk wayar da suke da Dadi bai taba sanar mata abin da ake ciki ba. Sai da ta dawo ta tarar da bakin ciki kala kala. Tayi bakin ciki matuka, na yadda ta samu Dadinta cikin rashin koshin lafiya.in ba don Mallam ba, ba ko maikula da shi. Halim da Hanif ba wani hankali ne da su ba. Duka duka shekararsu twelve ne a lokacin, ba abin da ya dame su sai dai susa video game agaba su yini wasa. Karatu duk ya tabarbare. Haka nan ta tarar da khalil a kulle yana hauka tuburan. Da Momi ta hadu da wata kawarta tayi mata jajen Khalifa. A nan ta san ashe mutane sun san case din danta. Yana kulle sama da wata hudu sai a lokacin ta kai masa ziyara. Dan saukin da ya samu ta dage sai an sako mata shi. Tare kuwa suka dawo gida. Mallam Usman da yaji shi ya bada shawarar a mayar da shi wajen wani malami mai horar da yara irinsu. Haka kuwa aka dauke shi aka mayar wajen mallam Gaga. Karatu Qur’ani sosai da sauran littafai yake biya maus. Kuma a hada da bayar da maganin shaye shayen. Tun da aka kaishi wajen nan ba wanda ya ke kai masa ziyara in ban da zainab. Ita Momi ta fake da tayi fushi saboda an dauke shi bada shawararta ba. Dadi kuma yace ba za a dawo da shi ba. Haka ne ya sanya tayi fushin karya. Nan kuwa fakewa ta yi da hakan domin kuwa bata da lokaci. Aikin da take nema a Abuja ya samu. Kuma ga shi basa zama kullum suna cikin fita aiki. Alkawarin da tayiwa Dadi da farko shine zata ringa zuwa kowanne sati, amma shi ma ya gagara. Daga baya ta fito da akidar sai dai shi ya bita su koma Abuja, yace ba inda za shi. Shi ba cikakkayar lafiya ba, tun da nasa aikin ma ya gagara yi. Dawowar Farida shi ya dan daidaita lamuran gidan. Amma itama bata iya tsawatarwa su Halim. Saboda haka yaran suka fara komawa ba arabi ba boko. Gashi itama tun da ta dawo aiki ya sha mata kai. Kusan kullum sai ta kwana a asibiti. Ga dai karatun ta samu masha Allah. Ga kuma babban aiki amma fa babu ko mashinshini. Abin dai bai kai ga damunta ba tukunna. Gida dai ya fashe ya zama kamar kufai. A wan nan rana da Zainab ta kai ziyara, abin ya bata mata rai matuka. Farida ta fara aikin kwana. Wan nan ya sa su Halim basu je makaranta ba. Mallam kuma yaje garinsu gaisuwa. Sallama take ba wanda ya
Chapter 40 · 0% Book details