← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 43

Sashe 12

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 2 min read

computer. Ya karya hula da tayi matching da kayan ya kuma bude jikinsa da turaren cool water. Idan ka ganshi sai ka dauka sabon ango ne ba mai shirin zuwa nema ba. A motar ma Sulaiman ne mai tuki shi kuwa marriage candidate sai dada gyara hula yake yi yana dada duba kansa a madubi ya tabbatar kwalliyar sa tayi. A kofar gidan Dr Abdullahi suka yi parking bayan sun yi horn maigadi ya bude musu gate. A wajen parking suka yi parking. Momi na zaune a falo ta ji shigowarsu. Nan suka yi shawara akan shi Sulaiman tunda kusan dan gida ne ya shiga yayi masa iso. Shi ma kuwa Sulaiman ganin ya zabowa Zainab zakaran gwajin dafi ya dage wajen karantawa momi uban gidan nasa. Tun da ya fara bata labarin AlAbashir zuciyar Momi take tafasa. A zuciyarta take ayyana irin azabar da zata gana mata saboda bakin ciki. Sai da ya gama tacee "to kai Sulaiman ga kanwarka a gidan ga kuma su Farida amma duk bai gansu ba sai wan nan kucakar yarinya"? "Su ma ai kin san halinsu Momi. Gaisuwar arziki bai samu daga wajensu ba suna zuba dan banzan girman kai. Ita ma ai ladabinta ne ya jahankalinsa da kuma ...,.." "To kaga ya isa haka. Duk wani bayaninka ba zai yi tasiriba. Ka koma ka sanar da shi Zainab an mata miji. Idan har a gidan nan yake son aure yazo ga Farida nan ko Farisa duk wacce yake so zan bashi. A bakin gate ya samu AlBashir suna hira da Mallam mai gadi. Saboda kowa ya san shi dabi'arsa ce sakewa da kana nan ma'aikata na gidansu da kuma na office. To a haka ya same shi da Mallam suna 'yar hira yau da kullum. Saboda rashin sanin halin da zai shiga idan yaji batun da ya zo da shi a nan ya fara kora masa bayanin da Momi ta zayyana masa a kan Zainab. Nan take kuwa ya shiga rudani. Amma sai ya daure yayi ajiyar zuciya yace "allah yasa haka shi yafi alkhairi". [8/6, 23:21] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI👨‍❤‍👨👨‍❤‍👨 Page 14 BY HANNE ADO ABDULLAHI
Chapter 12 · 0% Book details