Sashe 24
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 6 min read
Allah ne, amma a dinga duba komai ya zama dai dai ruwa dai dai tsaki”. Daga nan sai ta fara sharben hawayen karya tana fadin “kuma ni idan kayi haka ni zaka jawa zagi, sai aga don bani na haifeta ba na tura ta inda zata wahala. Tun da kaga yaron dake neman Farisa babansa senator ne. su Sakina ka duba kaga irin mazan da suka aura. Kuma ita a aura mata mai tallan gwanjo”. “to ya kike son in yimata ba ita ta kawo shi tace shi ta ke so ba. Kin san yaran yanzu da kallafa rai a kan abu. Idan naki bata shi sai ki ga an zo ana samun matsala. Kuma idan shi an ki bashi aurenta, tana da wani manemin ne”. “manema kai Daddy. Kaga akwai kanin wata kawata. Au nama tuna ka san ta Maman Aziza. Ya dawo daga London ya samu aiki a chevron. Tun da yazo gidan nan ya ganta ya ke ta nacin in bashi ita. Idan har ka yadda a rushe maganar waccan yaron, sai a hada ta da shi. Ka tuna daddy hustling din nan shi ma ba dadi gareshi ba”. Allaha ya sani ba wai son Zainab ne ba yayi ba, haushinta kawai yake ji na yadda taki ta zama kamar sauran yaransa a zatonsa, tun da shi bai san ya akayi karatunta ya gurgunce ba. Amma yadda yaga yaran a tsaye da alamun akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu. Bayan sun gaisa ya shiga gida. Nan kuwa ya sanar da ita abin da ake ciki batun ganinsu da yayi yanzun nan. Take ita ma kuwa ta bashi shawarar yadda za a yada kwallon mangoro a huta da kuda. Su dai suna tsakiya da zancensu su uku cikin jin dadi da annashuwa sai ga Halim yazo ya ce suje dukkan su uku Daddy na neman su. Cike da tsoro suka bi shi zuwa falon Daddyn. Nan suka same shi zaune tare da hakimarsa. Cikin ladabi suka sake gaishe shi san nan ita ma suka mika mata tata gaisuwar. Daddy yayi gyaran murya. Ya kalli Zainab, yace “Zainab wan nan shine yaron da kika zaba ki ke son ya zama abokin rayuwarki?” Shiru ta kasa Magana. Sai Momi ta ce “ki buda baki kiyi Magana mana. Duk kanmu nan akwai wani bakonki”. Cikin jin kunya ta daga kanta alamun eh. San nan ya juya ya maida hankalinsa inda su Al Bashir ke zaune duk murna ta cika musu ciki, na ganin nesa zata zo kusa. San nan ya sake cewa “mallam Balarabe ina son in sanar da kai na shirya aurar da Zainab nan da lokacin kankanni, saboda haka idan har da gaske kake yi ka turo da iyayenka nan da kwana goma. In aka wuce wanan lokacin zan bayar da ita ga wani”. Da sauri Mujib ya amsa da cewar “da iznin Allah ba zamu haura hakan ba, yanzu zamu je mu sanar da su sakon da kabamu”. Nan take Momi ta sake samo wata dabarar tace “kuma Dadi ina ga abin da za ayi a saukaka komai. Kaga dai idan ma kayan daki akayi mata, bai fi ya samo musu daki falle daya ba. Saboda haka kar ka karbi komai ya biya sadaki kawai idan yaso shi yayi mata kayan daki daidai da su shi da kansa. Kaga an sauke msa wahalar lefe. Tun da kuma sana’ar gwanjo kake na san ka san inda zaka samo furniture second hand”. Ba su san sanda suka hada ido tsakanin Mujib da Al Bashir ba, na ganin yanayin cin mutuncin da Momi ta dauko yi musu. Al Bashir ya sake kai idonsa inda Zainab ke tsugunne. Yana kallon yadda take kokarin sharen hawayen da suka zubo daga idonta. Shi ma Mujib ya hango yanayin da take ciki.Take ya mai da hankalinsa wajen daddy yace “ba komai Allah Raini. Akwai abokin mu daya kafinta ne. idan muka sayi kayan aiki na san zai mana kayan gadon da sauki. Sai a gaya mana sadakin yadda idan munje gida sai mu sanar su taho da shi gaba daya”. “Dubu dari biyar” suka ji muryar Momi ta furta. Da su da Zainab din duk ba su san sanda suka dago suka kalleta a firgice ba. Zainab ta maida kanta kasa kawai taci gaba da kuka. Shi kam kukan nata yafi komai daga masa hankali. Ji yake kamar ya tashi ya naushe bakin Momi da ta sanya rabin ransa kuka. Mujib ne yayi saving situation din yana neman a dan rage musu, saboda su masu karamin karfin ne. “Ashe da ma ba auren kuke so ba wasa kawai kuka zo yi da hankalin ‘yata. Ni dai iya abin da muka ga zamu bukata na sadakin ta ke nan. Idan zaku iya biya BisMillah. Idan kuma kun ga ya fi karfin ku to ku tafi Allah hada kowa da rabonsa”. Momi ta sake fada. Daga haka kuwa ta mike shima Dady ya mike suka shiga gida. Suna barin falon Zainab ta saki wani kuka mai shessheka, wanda ke nuna alamun rike shi tayi. Tashi yayi ya koma kusa da ita. San nan cikin muryar rarrashi yace “Putri Salju dago ki kalle ni”. Ta dago ta kalle shi. Yana ganin yadda fusakrat ta koma shi ma ya shiga tashin hankali. A lokacin yayi niyyar tonawa kansa asiri ya juya ya kalli Mujib yace “lets quit this game”. “Not now is like there is a hidden agenda behind it. Roll the dice to the end”. Mujib yace da Zainab “kin ga mufa wan nan ba wani abin daga hanakali ne a wajenmu ba. Zamuje mu ga yadda za’a yi”. “Amma ya Mujib 500. Ta ina zamu samo su”. Sai kawai ta sake sakin wani kukan mainuna alamun karaya. Hannunta yaja ya rike cikin nasa, yace “kin ga Putri daina damun kanki. Ga mashin dina na san idan na sashi a kasuwa zan samu dubu hamsin. Ina da dashin da na shiga na dubu goma. Kuma an bani. Ni na dauki na karshe na dauki dubu sittin. Idan an juya zan samu na farko kin ga ai an samu dari da saba’in. na kuma san Abbana zai tallafa min da ko yayane”. Yana fadar haka ta mike da sauri tace “ina zuwa”. Tana fita kuwa bata jima ba ta dawo, hannunta dauke da bakar leda. Ta mika masa. Sai da ya sa hannu ya warware kullin ya ga ashe kudi ne a ciki. Suka kirga suka ga dubu saba’ain da biyar. Yace “me za yi da su”? “ka hada ka kawo sadakin da Momi ta tambaya”. Sai da yaji kamar zaiyi kwalla saboda tausayin ta. Tabbasa tana son sa bilhakki da gaskiya, saboda duk kokarinta na kar araba su ne. ya karba yace “ko dai in hada da wadan can da kikabani a yi miki kayan dakin”. “ni dai ban ce ba. Kayan daki ba su zasu bani farin cikiba. Sadaki nake so ka kawo shine kawai muradina”. Shi kansa Mujib sai da ta burgeshi da kuma tausaya mata da yayi na ganin yadda ta mato akan kaunar abokinsa. Nan take yace “kar kuji komai. Nima ina da dan tanadi na, na san kuma ba zasu gaza dubu dari ba. Idan muka hada na san zamu samu wani abu substantial”. Momi bata basu damar ci gaba da Magana ba ta aiko Hanif ya kirata akan tazo ta dafawa Daddy tea kuma ta dora abincin dare. Mikewa tayi yayin da suma suka mike Mujib yace “dan Allah kar ki sawa kanki damuwa. Mu dai goyon bayanki kawai muke bukata. Idan muka samu wan nan to mu kuwa mun yi niyyar tunkarar ko wane kalubale ne ya fuskanto mu’. Nan dai suka yi sallama. Ta shiga gida su kuma suka tafi