Sashe 42
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
fara masifar Zainab ta mallaketa mata da. Ya daina jin maganrta sai ta yarsa. Shi dai bai bi ta kanta ba ya yi tafiyarsa makaranta. Wan nan karon ma Dadi ya dan yi jinya, su baffa suka zo dubashi. Duk da dai yanzu shi dan gata ne a wajen Zainab. Hatta ruwan da zai sha za ta tabbatar ta ajiye masa. Amma yadda su Baffa suka ga gidan kamar kufai sai ba suji dadi ba. Suka tambayi Momi ya gaya musu ta koma Abuja da zama. Baffan Nene ne yace “to kai kuma haka zaka ci gaba da zama gida ba mace”? Shiru yayi bai bashi amsa ba. Shine ya sake cewa idan baza ka ga mun yi maka karanbani ba ai da mun baka mata”. “Wallahi Baffa ba wani karanbani. Idan zan samu hakan zan gode”. “ba damuwa kaje ka ganta ku gaisa. Safiya yarinyar kirkice duka duka shekarara ta talatin da biyu bata taba haihuwa ba. Mijin ne Allah ya yi masa rasuwa”. Da alamun jin kunya yace “Baffa ni ba ma sai na ganta ba. In dai kuna ganin ta dace da ni shi ke nan ayi komai. Momi dai bata da labarin komai saboda ba wanda ya ji zancen auren. Farida ce zata sanr da ita ita kuma ta koma karatu tana Ibadan. Halim da Hanif Zainab ta mai da su wata boarding school inda ake biya musu har karatun ‘Qur’ani mai girma. Saboda haka week end kawai tazo ta tarar da amarya a gida. Komai kuma ya canza. Dadi ango ya murmure duk furfuran nan ta tafi. Gida ko ina kal kal da shi. Tayi niyyar yin tijara da saukewa amarya Safiyya rashin mutunci, ita ma kuwa ta nuna mata ba kyalle bace. Da shirinta ta zo. Dadi yaga zata daga masa hankali ya sake ta saki daya. A ranar ta koma Abuja cike da bacin rai. Duk wan nan badakala da akeyi Zainab bata nan ta yi tafiya saboda tana kokarin hattama degree ta na uku a tafsir. Ita kam ai ilmin ta dangin mijinta ba karamin amfana suke da shi ba. Kaf yaran family a wajenta suke daukar karatu. Babbar islamiyya ta bude sadaka. Tun tana madina Dady ya sanar da ita zancen aurensa. Ta tashi dawowa kuwa ta hadowa ango da amrya lefen na garari. Ta shirya musu dan karamin honey moon inda ta yaudare su da cewar Dadi zai koma check up. Kafin su dawo kuwa ta sa akayi musu total renovation. Akayi musu sababbin furniture. A wan nan lokacin yaranta uku. Amma’yar shekaru takwas, sai Amir mai shekara biyar sai kuma Maama mai shekara daya. Sai koma babban bebinta da bata hada shi da kowa, watau first born dinta ke nan bala mai gwanjo. Goggo Safiya kuwa ta kama kowa ta rike a gidan. Su Halim idan sun zo hutu nata ne. Farida kuwa dama I don’t care attitude gareta. Ba ruwanta da harkar kowa. Aikin ta kawai ta sa a gaba. Albashir zaune a falonsa suna buga game da Amir a Xbox X dinsa Zainab tayi sallama ta shigo. Yana ganin yanayinta yace da yaron “game up. Sai gobe ma karasa”. Yayi musu sallama ya nufi dakinsu. Yaron na fita ya jawota jikinsa tare da fadin “me ya samu Putre Salju na? na ganta yau kamar akwai abin dake damunta”. “Farida ce ta bugo min waya tace wai EFCC sun kama Momi”. Sakinta yayi yaci gaba da buga game din shi kadai. “Ya Balarabe bakaji me nace maka bane”? “naji so what. Me kike so inyi miki”? “Kenan ba taimakon da zaka iya yi min. Shi ke nan na gode zan je in yi iyakar kokarina” ta mike irin ni nayi fushi din nan. Da sauri ya mike yana riko ya yana fadin “yi hakuri Putri na. idan kikayi min fushi ina zan sa kaina”. Da murmushi ta dawo wajensa ta zauna a gefensa. Shi kuma yace “yanzu gaya min me kike so inyi”? “wai da ka kirawo yallabai Sa’ad ba shine ogan Abuja ba ko da taiamkon da zai iya yi mana”. “an gama ranki shi dade”. Waya ya kira ya sanya ta a speaker. Muryar sa’ad taji yana cewa “kaga autan umma angon Zainab baban Amma. Yau ka tuna da ni ne ko zakka ka cire ka tuna da abokinka tsohon dan sanda”? “Ai ba wata zakka sai dai rigimar Putri da ta tashe ni yanzun nan”. “a kace amaryar bala mai gwanjo ta murda kambunta”. “ai ita dama kambunta kullum a murde yake. Gani kuma matsoraci ban iya yi mata musu ba”. Dariya ya tuntsire yace “yanzu me take so ayi mata mu taimaka mu dafa maka. Kasuwar gwanjo zamu koma, koko wata sana’ar ta samo mana”? “In bata samo sana’a ba ai ta dauko rigima. Ka tuna matar nan da ta so hana mu auren juna. Ita staff dinka suka kama”. “subahana Lillahi. Ai kuwa aiki baiyi kyau ba. Suruka guda a hannun surukinta. Bani details din case din. “ai ba wani details sunan ta Rumaisa a finace take aiki. Sai dai ban san nawa ta sata ba”. “kai jama’a. yanzu Ya Balarabe don zaka taimaka min sai ka ci min fuska”? Sa’ad ya jiyo muryarta ta speaker da Albashir ya danna. “Kin ga madam kyale shi. Bani nan da five minutes zan kiraku”. Minti biyar din ma bata karasa ba ya kira ya ke sanar dasu abin da ya faru. Kudi ne suka fitar ita da ogan ta har miliyan hamsin. Amma unfortunately five million kawai taci a cikin kudin saboda ogan ne ya karbe sauran. Sai dai kuma sa hannunta ne a voucher so ba ta inda zata fita. Sa’aad ya ci gaba da cewa “idan so samu ne a samu a yi refunding ko da ten ne daga cikin kudin sai a samo guarantor da zai sa hannu a sake ta. In yaso daga baya zan ga yadda za a yi ayi dropping all charges against her”. “kana maganar 10 mill. Ni ina ga kudin da zan biya”? Da mamaki ta juya tana kallonsa. Mutumin da don ya ginawa talaka gida ya bashi jari mai kauri ba wani abu bane a wajensa amma yana kukan bashi da as little as 10m. Tana cikin kuka ta duba balance din account dinta. Kudin ba su kai ba. Saboda bata dade auren Sajida da kuma Faruk kannenta ba. Duk da dai 90% Albashir ne yayi komai. Ga kuma Hafsa da ta itama auren nata ba hustling saboda kanin abokinsa Mujib shi ya aureta, amma dai duk da haka an dan ji jiki. Saboda har gida suka gina masa. Yinin ranar sam ta kasa sukuni. In ban da kuka ita da Farida ba abin da su ke yi. Ita farida tana da albashi mai dan tsoka, amma kaf hidimar anti Sakina da yaranta a wuyanta suke, saboda haka kafin wata dan abin da aka samu ya kare. Zainab tayi rokon tayi lallashin amma sam Albashir ya kekasa kasa yace shi ba abin da zai iya yi. Daddy kuwa ko guarantor ma yace ba zaiyi mata ba. Farisa tace ita kuwa she cant waste her money on Momi saboda ita ta jawa kanta. Albashir ya shiga wajen Umma take tambayarsa yinin yau gaba daya bata ga zainab ba, kuma bata kirata a waya ba. Kwanciyarsa yayi a kan doguwar kujera san nan yace “kyaleta umma rigima take ji shi yasa ma na fito na barmata gidan”. “haba dan uwana. Don tana ji rigima kuma ina ce ba rarrashinta zaka yi ba. Ita fa mace ba girma take da shagwaba a gaban mijinta ba”. “umman ba rarrashin take so ba. Wai fa matar gidansu taci kudin gwamnati shine ofis din su Sa’ad suka kamata. Kuma wai ni take so in taimaka in fito da ita”. Da mamaki Umman ta sake cewa “baka da abin da zaka fito da ita din ne ko kuwa tsiya kawai kake ji”? Shiru ya kasa baiwa umman amsa. “Anya dan uwana yaushe ka koyi riko haka”. “Allah Umma don dai baki san irin muguntar da ta dinga yiwa Zainab bane. So tayi kwata kwata rayuwarta ta lalace. Hatta makaranta kin ga sai da tayi mata sanadinta”. “Kuma da tayi mata sanadin nata sai me ya faru. Yanzu kai ilmin da Zainab take da shi ba daidaikun mata ne suka samu sa’ar yin sa ba. Ina ce ran nan kace min ERC sun nemi ta basu littafin data buga na easy fiqhu akan zasu saka shi a IRK syllabus na makarantu. Kuma duk wan nan daukakar har ace ana bakin ciki bata yi karatu ba. Ashe akwai abin da yafin ilmin addini dadi”. “umma ni kawai haushin matar nake ji”. “To ka daina saboda Maryam ta taba tambayarta dalilin da yasa take iya yiwa Momi alkhairi lokacin da ta kai Khalifa karatu Saudiyya. Amsar da ta bata ni kaina naji dadin ta. Tana budar baki tace idan har ta ci gaba da kullatar Momi to tabbas ba ta yi wa Allah godiya da ya hada ta zama da mu ba. Kaga kuwa idan ita tayi wan nan tunani kai ma irinsa nake so kayi. Saboda haka, kaje dan uwana in dai baifi karfinka ba, ka taimaka a fito da ita”. Suna falonta zaune ita da Farida sun yi jigum jigum, saboda ance idan ba a zo bailing Momi ba tsakanin yau da gobe tabbas jibi kotu za a tura ta. Shigowarsa yana waya inda suka ji yana neman ticket na mutum uku zuwa Abuja, ya sanya suka saki ransu. Sun sami jirgin karfe daya. Kafin uku suna ofis din Sa’ad. Albashir ne yayi komai, ya kuma tsaya a guarantor, amma fa yana yi yana mitar idan Momi ta gudu aka kama shi, ita ya shafa. Saboda umma da Abba suna da wasu ‘ya’yan ita kuwa shi kadai ne mijinta. Sa’ad yana dariya yake ce masa “kar ka damu ba inda zata je. Kuma ma ina ga zan yi closing din case din yau din nan. Nan da nan asarar 10m ta hau kan Albashir. Saboda ba shi yayi niyya ba ya sa mata suna asara. Mutumin da riba ke shiga account dinsa bayan kowacce awa daya. Ko sati zai iya hada ribar 10m din. Inda Allah ya takaita Farida bata tare dasu da ba