← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 43

Sashe 7

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

ashirin. Kuma ko ya kai sha tara ta sosa to sauran sun zube. Haka ya dinga zabgar ta kamar ya samu jaki. Yana cikinn ta sha takwas sai ga Farida ta shigo a guje tana fadin "Daddy tsaya gashi na tsinto shi a kit din Anti Sakina ashe dama bata da duba da kyau ba". Momi sai ta shiga salati da tafa hannu tana cewa "yanzu Farida munafuncin da zaki koya ke nan. Ina ce ni da kaina na je na duba kit din ban gan shi ba". "Mommy kema baki duba da kyau ba. Tun da ni dana je na daga kasan kit na gan shi ya fada ciki". Bata jira cewar kowa a falon ba ta daga yayarta ta jata zuwa daki. Tsabar azabar dukan da ta sha da kyar ta ke iya daga kafa. Tayi jinyar ta ta warke. An yi haka da wadansu kwanaki tana baya tana aikin abincin dare. Kar ku dauka ta wani manyanta. A'a duka duka a lokacin shekararta goma sha uku ne kawai. Kubewa take gurzawa ta miyar daren. Saboda a hankali daga juya min miya zuwa bare min magi ta koma daura kaza ki sauke a gidan. Su kuwa sauran in ban da karatu ba abin da Momi take barinsu suyi. Shigarta islamiyyar unguwarsu ne ya sanya ta ke kokarin kamo su a na Islama. Amma boko kam ya bi ruwa. Ko wasikar kirki da kyar zata iya rubuta maka da hausa balle English da sai dai idan tana aiki a falo ta ji a nayi a TV ko kuma sauran mutan gidan idan suna yi a tsakaninsu. Babu wanda zai ga yanayinta ya dauka ubansu daya da su Farida. A wan nan ranar ta kusa gama wa ke nan sai ga Farisa ta shawo kwana a guje da kekenta. Ta kasa tsayawa sai kan kwanon kubewar nan. Da ita da keken da kuma mai gugar kubewar gaba daya suka fadi. Farisa tana daga hannunta sai taga wajen ya dauje. Da gudu ta harba cikin dadi a lokaci guda kuma ta na tsandara ihun kuka kamar wadda aka cirewa ido. Ita kuwa boyiboyin gidan ba ta ankara da nata ciwon ba. Hankalinta yayi kan kubewar da ta zube. Tana kokarin kwashe ta daga kan sumuntin data kife taji muryar babanta da karfi yana kwalla mata kira. Gaba daya jikinta ya dauki bari. Shi ke nan ta san yau sai ta sake shan wata bulalar. A firgece ta saki kwanon data kwashe kubewar ta nufi falonsa a guje. Tana zuwa bata yi wata wata ba sai kawai ta zube flat a gabansa ta mikar da hannayenta gaba ta rike su a cikin na juna. Jira kawai take taji saukar bulala. Tun da ta san kira biyu ne a tsakaninta da Momi da kuma Daddy. Ita momi ko zata sata aiki ko zatayi mata fada. Shi kuma Daddy ko zaimata fada ko kuma zai zane ta. To yau kuwa tunda ta hado su da shalelen gidan Allah ne zai kwace ta a hannunsa. Shi kansa yadda yaga ta zo ta zube a gabansa tana sauraren duka daga gareshi sai da tausayin ta ya ka mashi. A hankali ya ce da ita "ta shi Zainabu ba dukanki zan yi ba. Samo ruwan dumi da gishiri ki gogewa Farisa inda taji ciwo". Gaba daya jikknta bai dai nabari ba. A haka tayi abin da aka sata. Ga wata sara da Momin ta dora Daddy a kai. Iya cin jarrabawarka iya kyautar da zaka samu kuma ciki har da dinkin sallah. Saboda haka kusan ko wacce sallah sai dai Farida ta bata kwancen kayanta da ta saka. Gashi ta fita garin jiki haka zata zumbula su wuyan riga na zamewa ko skirt buhubuhu a jikknta yana jan kasa. A wan nan sallah Daddinsu ya hada su gaba daya suka je kera domin su gai da 'yan uwa da kuma kakanninsu. Gaba daya yadda kakannin suka ga Zainab bai musu dadi ba Ta zama wata 'yar tsurut da ita. Gata kamar ko yaushe a firgice take. Tun da suka je kakarsu na hankalce da su. Ko kaya zasu saka ita zata fitowa da kowa nasa ta jera musu. Ta kwashe wanda suka cire ta wanke ta shanya . Halem da Hanif kuwa har abada daya na goye a bayanta. Gasu da wata irin kiba kamar mai tallan michelin. Amma haka nan tutur take fama da su. Ita ba me aure ba amma tafi matar aure hidimar gida da kuma wahalar yara. Kwana hudu kawai suka yi Momi da Daddy suka zo daukarsu. Suna falon mahaifiyarsa suna gaisawa inda a anan baban Daddy ya shigo ya iske su. Mahaifiyarsa ta kalleshi tace "Dacta ina son ka lura da wani abu idan ita Rumaisa ba ita ta haifi Zainabu ba kai kai ne mahaifinta. Amma ka kasa yi mata riko irin wanda kake yiwa sauran 'ya'yanka". "Hajiya wani abu tace an yi mata"? "Yo wan nan yarinya sai tace an mata. Ai duk mai hankali idan ya dubi yanayinta zai san a kuntace take rayuwa". Nan Momi ta shiga matse hawaye tana fadin "ni dai Allah ne shaidata yadda nake rike su Farida haka na ke rike da ita". "Wayyo Rumaisa share hawayenki ba yan zu ne lokacin yin sa ba. Ki dai tuna zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. Nawa aka yi kafin wan nan kuma duk munga inda suka bulle. Yarinya gaba daya bayanta a zane kamar jikin alfadari, amma kuce wai ba abin da kuke mata. To wallahi kaji na rantse maka idan ka sake kai hannu da sunan dukan Zainabu ban yafe maka ba". Daga nan kuwa bata sake magana ba ta shige uwar daki. Nan dai baban Dr watau Baffan Nene ya saka su a gaba duk su biyun da nasiha. Ita dai Momi har a wan nan lokaci tana ikirarin ba abin da take mata. Tun da suka dawo kuwa ta dora Daddy akan hana su zuwa kauye saboda a nan ake son lalata masa zaman gidansa a cewarta. Zainab dai bata samu karatun ta ya hau turba ba sai da Halim da Hanif suka shiga makaranta. Suma kuma ba sa tasowa sai biyar saboda har islamiyya a makarantar suke. Sai schedule dinta yayi mata daidai. Da safe ta yi breakfast ta shirya 'yan makaranta. Bayan sun fita ta gyara gida. Idan ta taso sha biyu ta wanke kananan kayansu da ta jika ta kuma yi manyan ayyuka. Abincin rana an soke yinsa a gidan. Saboda iyayen ma'aikata ne suma sai wajen shida suke dawowa. Daga baya Momi ta tura ta wajen wata kawarta ta koyo yin snacks. Shi ke nan ita momi ta fara sana'ar yin na sayarwa. Saboda haka tun bayan sallar azahar yarin yar nan zata fara tumurmusar flour. Ko ta na dani samaosa da spring rolls ko tana murjin meatpie ko kuma tana kwabin cake. Ga shi Alhamdu Lillah Momi na samun kasuwa ita kuwa Zainab tana ji a jikinta. Ita zata je kasuwa ta sayo kayan aiki ta murza ta soya ko ta kwaba ta gasa ita kuwa uwar dakin sai dai ta caski kudi. Amma duk da haka ko ladan aiki bata samu. Saboda ko da sallah ko irin Allah ya isa tallana ba zata samu a dinka mata ba. Sai dai kannenta su bata kwancen nasu. [8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨‍👧IN FIKI A MIJI💑 page 8 BY HANNE ADO ABDULLAHI Haka nan rayuwar Zainab ta ci gaba da kasancewa. Momi ta rabata da uwarta ta cusa rashin jituwa tsakanin ta da mahaifinta ta kuma raba ta da sauran dangi. Bata shaku da kowa ba sai dai aikinta da kuma baba Laure matar Mallam mai gadinsu. Dakuna shida ne a gidan kowanne da bandakinsa ga kuma falo uku. Amma kullum sai ta share na sharewa ta kuma wanke na wankewa. San nan ta bi ko ina ta goge. Idan Farida ta nuna kokarin taimaka mata yanzu uwar zata kora ta akan maza ta koma kan karatunta. Saboda haka daga 'yanmatan gidan anti Sakina da anti Bilki zuwa kannenta Farida, Farisa, Khalil, Halim da Hanif ba wanda zai iya rayuwa idan bata taimaka masa ba. Ko kayan sawarsu ba su iya tsarawa ba sai ta hada musu. Kusan ko yaushe ka ganta a cikin wata hidima take. Kullum ita ke karshen kwanciya misalin sha dayan dare kuma dole ta tashi hudu. Jikinta ya saba da wahala. To ita da haka suka kyale ta ma ba kyara da hantara da kuma cin mutunci da ta ji dadi. Inda kawai take samun sauki wajen Farida da kuma Anti Bilki. Amma sauran sai dai wahala. Su din ma suna sata ayyuka amma ba cin mutunci da wulakanci. Kuma sukan yi hirar arziki da ita. Inda ta dada tantance matsayinta a gidan wata rana ne tana kwashe tuwon semo. Khalil yana zuwa ya sa cokali ya debo tuwon nan ya bude rigarta ya sakar mata shi a ciki. Habawa! Ba ta san sanda ta mike cikin jin zafi ba tana ta rawar radadin zafin tuwon da ke kona ta a gadon bayanta. Haka ta dinga rawa da tsalle saboda zafin da take ji. Su kuwa sauran yaran sai dariya suke ta tintsira mata. Bayan nan ya dade yayi ja, abinka da farin mutum. Nan aka mai da abin wasa. Kuma har da Momi a wajen. Itama sai ta kulli aniyar ramawa tun da taga wasane. Sai ta sayo rayuwar ruwa a makarantarsu. Wasu animals ne da objects na roba. Idan ka siyo shi yana karami. Kana jika shi a ruwa sai ya yi ta shan ruwa yana kumbura. Ta san shi da tsoron kadangare sai ta sayo mai suffar kadangare ta jika shi wajen kwana uku. Yayi girma sosai kamar kadangaren gaske. Ta lallaba ta wurga masa cikin jakar makarantar sa. Yana zazzago litattafansa habawa yayi arba da katon jan gwala gwada ya fado. Tsalle ya daka da ihu a lokaci guda. Su Momi duk a ka yo kansa. Shi kuwa kamar zai shide sai nuna musu kadangare yake yi. Zainab tasa hannu ta dauke shi tana fadin "nima na rama" Wani irin barin makauniya Momi ta rufe ta da shi. Tana dukanta tana fadin "shegiya tsinanniya mayya. Kashe min
Chapter 7 · 0% Book details