Sashe 16
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi. “me kike yi har yanzu baki yi bacci ba”? aka tambaya daga daya bangaren. Sai da ta dago wayar daga inda take ajiye a kasa saboda ta ga waye mai kira da wan nan tsohon dare. Bata ga suna ba sai bakuwar lamba da ta gani. Ba shiri ta maida hankalinta kan wayar tace “yi hakuri wa kake nema ne”? “wacce nake nema na samu. Ko ba Zainab ce nake Magana da ita ba”? “itace ,amma don Allah kayi hakuri ban gane wa ke Magana ba”. “Allah ya sani Zainab zaki sa zuciyata ta buga, ina nan na kasa sukuni da tunaninki amma ke har kin manta da ni”. Ta dan yi ajiyar zuciya san nan tace “ka yi hakuri da gaske ban gano waye ba”. “na yarda Zainab. To bakon dazu ne Balarabe”. Murmushi tayi mai sauti wanda har sai da yaji sautin sa ta cikin waya, san nan tace “kayi hakuri ban dauki muryarka ba. Barka da war haka”. “barka kadai Zainab” shi ma ya fada cikin jin dadin yadda yaji alamun murna da jin sautin muryarsa. San nan ya ci gaba da cewa “mu dawo maganar mu ta dazu. Me ya hana ki bacci har wan nan lokaci”? Tabbas tayi murna da jinsa , saboda tsayuwarsu yau daya taji shi a cikin ranta. Ta kuma kasa daurewa har sai da ta sanar da baba laure bakon da ya zo mata da la’asar. Ita ma kuwa ta taya ta murna, ta kuma nuna mata cewar kar taji komai in dai har tana sonsa, saboda ta kan Mallam suka biyo. Ta fada mata haka saboda shi ma Mallam din iya abin da ya sanar da matarsa ke nan. Take kuwa ba ta san yadda akayi ba sai jin muryarta tayi tana cewa “idan na mayar da wan nan tambayar kanka zan samu amsa”? “Me kuwa zai hana Zainab”? “To na tambayi abin da ka tambaya’ Kai tsaye yace “tunanin santaleliyar yarinyar dana hadu da ita shi ya hanani bacci. Kin ji amsa ta ni ma kuma ina sauraron taki amsar”. “Ni labarai nake ji”. “kai Zainab. Ni nan na rasa sukuni saboda ke amma ke kin ma saka ni a kwandon shara. Kin ma manta da ni gaba daya”. Ba ta san san da ta dada kasa da sautin muryar ta ba, tace “kayi hakuri ba haka bane. Amma idan kaji ba dadi kayi hakuri. Ka san komai sai a hankali”. Kwarai ya yaba da hikimarta. Ga shi dai bata fito kiri kiri ta nuna tana ra’ayinsa ba. Amma kuma yaji dadin yadda ta karbe shi. Saboda haka yayi ‘yar karamar dariya yace “hakane Zainab. Na yarda da maganar ki. Amma yanzu duk da haka ki taimaka mini inji kwakkwarar bayani. Shin kin amince dani kokuwa. Ki taimaka min Zainab inji Magana daya daga bakinki”. Kunya ce ta kamata kamar yana ganin ta. Ya ji alamun haka saboda haka yace please Zainab ki taimaka min ko na samu kwanciyar hankali idan naji Magana mai dadi daga wajenki”. Cike da kunya tace “Allah ya tabbatar mana da Alkhairi”. Daga inda take tana jin alamun murna a sautin muryarsa in da ya ci gaba da cewa “na gode Zainab. Hakika yau kin faranta min raina yadda ba kya tsammani. Allah ya tabbatar mana da alkahiri”. Kwarai ta shagala da jin dadin hirar da suke yi shi da ita. Gaba daya taji nishadi na shigarta. Aiki take yi amma bata taba jin dadin aiki irin yau ba. Kafin kiransa a gajiye take matuka, saboda Allah Allah take ta karasa ta kwanta. Amma sam tun da ya bugo wayar ta gane wake Magana taji gajiya ta bar jikinta. Cike da nishadi taci gaba da danne meat pie din da ta zubawa nama. Tana yi tanajera shi a cikin kwalin da zata sanya a freezer kafin masu shi su zo dauka washegari. Cikin sassauta murya yace “bani labarin abin da kikaji a cikin radion”. Nan kuwa ta shiga bashi labarin duniya dalla dalla. Ya yaba da knowledge dinta a a current affairs. Ku san duk abin da yaji a tashar CNN da BBc world shi ta maimaita masa. Sai da ya nisa san nan yace “you are very current. Ina ga alamar jourrnalist zaki zama . sam bata gane me yake nufi ba saboda haka tayi shiru bata bashi amsa ba. Nan dai ya dinga janta da hira, har ta gama aikinta ta karasa gyaran kicin din. Ba shi ya daure yayi sallama da ita ba sai wajen sha biyu da rabi. Ya rabu da ita da alkawarin washe gari zai kawo mata ziyara. Momi na barin gida washegari tayi sauri ta shirya ta shiga gidan su Fatu da kokarin ta sameta kafin ta wuce makaranta. Ta kuwa sameta ranar bata da lecture sai bayan goma. Cike da zumudi ta zayyana mata labarin dan kyakkywan bakon da ya kawo mata ziyara jiya da kuma wayar da suka kwashe lokaci mai tsawo suna yi da shi. Feelings da ta ke ji a tare da ita bata taba jin makamancinsa ba. Ji take yi kamar ta janyo lokacin da yace zai sake zuwa wajenta. Ranar dai a anan ta lalace bata je islamiyyar safe ba haka nan bata bar Fatu taje tata makarantar ba. Domin suna ta tattauna batun Balarabe sai dubawa suka yi su kaga sha biyu tayi. Da sauri tayi wa mama hajjo sallama ta koma gida. Kamar yadda yayi alkawari. Ta na kokarin karasa hada abincin dare bayan sallar isha Mallam da kansa ya zagayo inda take a kicin tana aiki ya shaida mata cewar Balarabe ya zo. Da sauri ta karasa abin da ta keyi. Ta canza hijabin jikinta san nan ta nufi wajensa. Sai da ta dauki jug ta zuba matsattsen lemon zaki a ciki, san nan ta nufi bakin gate wajensa. Yau shi kadai ne. tun kan ta karaso daddaan kamshin turarensa ya bigi hancinta. Ba tare da saninta ba ta ja numfashi ta shaki kamshinsa sosai. Tun da ya hangota fitilar gidan ta haske ta ya kura mata ido. Bai taba ganin macen da ta iya taku irin na Zainab ba. Ga shi dai da dan hanzari take tafiya, amma sai ka rantse rawa take. Sai da ta iso gabansa san nan ya saki ajiyar zuciya. Shi ya sa hannun ya karbi jug din yana fadin “barka da fitowa gimbiya”. A kunyace ta dago ido suka hada nata da nashi. Dan duster da ta riko ta cikin hijabinta, ta saka ta goge bakin verander tace “Bissimmillah zauna”. “ni in zauna ke kina tsaye, ai kuwa haka bazata yiwu ba”. Tana kokarin zama gefen verender da sauri yace “kai kai dakata”. Da dan firgice ta juya tana kokarin tambayarsa abin da ya faru. Kafin tayi Magana sai gani tayi ya sanya gefen shaddarsa wacce da ace ta san kudinta to ta haura dubu dari. Amma haka ya sanya bakin rigarsa ya goge mata gefen da ta goge masa.yace “kema zauna my putri”. Ba ta san me yace da ita ba amma dai ta fahimce wani suna ne na jin dadi ya kira ta da shi. A wajen da ya goge mata ta zauna. Shima ya zauna a dan nesa kadan da ita suka saka tray da ta zubo masa lemo a ciki a tsakiya. Ta dan rankwafa ta gaishe shi kamar yadda tayi masa farkon zuwanta, san nan ta zuba lemon a cup ta mika masa. Cike da jin dadin abin da ta yimasa ya dauki lemon nan. Ya sha rabi ya na kokarin ajiye sauran, kawai bata Ankara ba sai jin muryar Khalil tayi yana cewa “eyeh lallai. Zainab kin rika. Jug din da Momi ta ware wa bakinta shi kika dauko kika kawo wa Bala mai gwanjo saboda kin raina Momi. Yau kuwa zaki gane kurenki”. Gaba daya ji tayi wutar kanta ta dauke saboda takaicin wulakancin da Khalili ya yiwa bakonta da ita kanta. Amma ta san babban ganganci ne ta nuna masa hakan. Kafin ta yi Magana yace “kin ga save your breath. Momi ce ta ce ki zo ki hadawa bakinta abinci, saboda su Farida da Farisa are very tired kin san su ba NFAs bane sun dawo daga IT sun gaji. A jiya Zainab tsakannin shabiyun rana zuwa na dare sai da ta dana samosa 500, spring rolls ma haka, da kuma meatpie shi ma same quantity, hakan kuma bai sanya ta ragi aikin gidan da take da komai ba, amma wai masu zuwa IT ten na safe su dawo 1 na rana sune suka fita gajiya. Khalili kuwa sauri yake yaje ya gayawa Momi labarin jug din data dauko, saboda haka ya na gama fadin haka ya yi gaba abinsa. Ganin haka ya sa ita ma ta mike da sauri ta ce da Al Bashir “yi hakuri ina zuwa”. Kafin ma ya amsa mata ta bi Khalil da sauri. Shi dai mamakin wan nan yaro yake. Ji yake kamar ya tashi ya rufe shi da duka, saboda wannan ne second time yana wulakanta masa Zainab dinsa. Tana jiyo sautin muryarshi yana sanarwa Momi labarin jug dinta na acrylic da ta kaiwa bakonta waje. Tana kuwa kokarin hada musu abinci Momi na caccakar ta tana masifar jug din da aka kaiwa bako ruwa a ciki. Bata tanka mata ba ita dai kokarin hada abincin take yi a dinning. Sai da ta gama komai su kuma suka zauna suka fara ci wanda ta dauki minti ashirin, san nan ta koma a tunaninta ma zata tarar ya tafi, amma ga mamakinta tarar da shi tayi zaune suna hira da Mallam. Ta zauna sun dan fara hira bai fi da minti goma ba, sai ga Farida ta iso wajensu. Ita kam sun yi gaisuwar mutunci don har ta yi introducing kanta a matsayin kanwar Zainab. Ya dan ji dadin ganin yadda ta mutunta ta. Amma shi ma abin takaice ta kalleshi tace “sorry to intrupt you. Amma Momi tace kizo ki kwashe plates a dining ki gyara kitchen”. Tana fadar haka tayi masa sallama ta koma ciki. Daga ido tayi tana kallonsa, kafin ma tace komai yace “kar ki damu Putri jeki zan kira ki anjima”. Tayi masa sallama ta dauki jug dinta ta shiga gida. Tana bada baya, AlBashir yace “mallam haka Zainab take fama