Sashe 36
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zainab din”? “Ita kuwa wallahi. Sam bata son karatu ba kuma ta son taimakawa a gidan. Kullum tana dakin a kwance”. Mallam Awwalun ne yace “ai mu kuma abin mamaki kusan tun kafuwar makarantar nan ba mu taba samun daliba mai kwazo da hazaka da kuma ladabin ta ba”. “Ahaf a makaranta take muku haka. Amam mu a gida ai wahalar ta muke sha. Kullum a cikin fada take da uwar goyonta. Ga bakin cikin kannenta da take yi. Allah dai ya sa ta samu mijin kwarai” Yasayyadi ya dan yi tsai san nan yace “Alhaji kayi hakuri da wata Magana da zan sanar da kai. Ka san kannena dukkansu biyu kawayen ta ne. haka zalika mahaifiyata tana shiga wajen hajiya. Amma labarin da ke fitowa daga gidan ka akan zainab ba mai dadin ji bane. Ka san su al’amarin mata akwai daure kai a ciki. Amma zan sanar da kai abin da na lura baka sani ba. Kaf aikin gidan ka har ma da sana’ar matarka Zainab ce mai yin su. Makaranta kuma ba kokari ne bata da shi ba. Amma hajiya da kanta, ta rantse sai ta lalata rayuwar Zainab saboda bakin cikin mahaifiyar ta da ta ke yi. Zainab na iya diban kawan uku na kowanne sati bata samu zuwa makaranta ba. Ko tana hidimar gidan ka ko kuma ta kannen matarka, wacce har gidajen su ake turata taje tayi musu boyi boyi. Ba aje makaranta ba ta yaya za a samu karatu ya tsaya. Ai rufar ka akayi. Abin da take yi wa Zainab shi ya hada su da mahaifiyata saboda tayi mata nasiha. Zani wan nan sai dai idan sauran ‘ya’yanka sun ga dama sun bata kwancen nasu. Shin ko ka san a gidan ka Alhaji, Zainab bata taba kwanciya a kan katifa ba. A kasa take kwana. Zainab ai ta sha wahala. Kuma ni Wallahi da na san bada sanin ka abubuwan nan suke faruwa ba da na yi karambani sanar da kai, saboda zagi dai kam ka sha shi a unguwar nan a kan Zainab”. Dr in ban da zufa ba abin da yake sharewa daga fuskarsa saboda bacin rai. Sai yanzu ya gano dalilin da ya sa tun da Zainab ta bar gidan komai ya daina tafiya daidai. Ashe dama ita ke aiwatar da komai. Shi yasa momi ta fito da dabarar yin kyauta idan kaci jarrabawa kawai, saboda ta san ta toshe duk wata hanya da zata sa Zainab ta samu wan nan kyautar. Yasayyadi ne ya katse masa tunanin da fadin “kayi hakuri Alhaji na san azarbabi na ya zarce misali. Amma a musulunci an fi son idan kaga dan uwanka na aikata kuskure to ka yi kokarin sanar da shi ya gyara, ba ka tafi kana gulmar sa ba. Ni ma kuma nayi ta neman sanadin da zan gaya maka naka kuskuren amma na rasa. Kasan yadda muke da hakki a kan ‘ya’yan mu haka suma suna da hakkki a kanmu”. “ba komai mallam Auwalu. Na gode da wan nan nasiha taka da kuma fahimtar dani da kuskure na da kayi. Na gode kwarai da gaske”. Ya fada yana mai mika masa hannu domin suyi sallama. A fusace ya shiga gidan sa nan kuma ya tarar da momi ta ci kwalliya za ta kamu. Dama kuma ita aladarta tana tsananin son buki. Saboda dinner ko ta waye sai ka gan ta a garin kano. Akawi randa ta kasa samun katin halartar wata dinner saboda jarabar son zuwa saboda ta hadu da haddaun mata, satar katin tayi ta kai sabon gari aka buga mata irinsa. A falo suka yi kicibis da shi tana fadin “dama kai nake jira ka shigo sauri nake yi fita zan yi”. “ba inda zaki je azzaluma macuciya mayaudariya”. “dr ni kake zagi? Ko dai ka sha wani abu ne”? “ba abin da na sha ido na ne ya bude daga nannauyan bacci da kika sakani. Ashe yarinyar nan zaluntar ta kika dinga yi ban sani ba”. “wai wacce yarinya kake magana akai ni ban ma gane me kake nufi ba”? “maganar Zainabu nake yi. Ashe ke kika cuce ta kika hana ta makaranta ban sani ba. Ashe baiwa kika mai da ita a gidan ubanta./ ashe kas kantar da ita kikayi a gaban ‘yan uwanta data girma. Amma ba komai ai kinga yadda Allah ya mai da ita”. “Oho sai yanzu na gano inda zamcen naka ya dosa. Kace dai yarinya ta auri mai kudi kaima zaka shiga ayi da kai. Shi yasa kake ta wan nan rara gefen. Yo kuma in ban da abinka kwantar da hanaklinka. Auren masu kudi ai yanzu aka fara shi a gidan nan. Farisa da zata auri dan senator ashe ita goya ta a baya zaka yi saboda nuna kauna da kuma soyay…….” Bai san sanda ya wanke ta da wani zazzafan mari ba wanda tun da take ba a taba yi mata irinsa ba. “Dr ni ka mara”? “An mare ki din idan kina da abin yi ki zo kiyi”. Har zata ci gab da zazzaga masa masifa, take sai tunanin ya shigar mata na cewar duk yadda akayi asirin karya tambaya data yi masa ya karye ke nan. Saboda malamin da yayi mata aikin ya tabbatar mata ba zai taba tantamar abin da ta gaya masa ko yayi shakku akan duk abin data fada. Tuna haka yasa tayi shiru kar zancen ya dada kwabe mata. Amma fa wata irin tsanar Zainab ce ta dada shiga cikin ranta. Shi kuwa bai ma kula da yanayin da take ciki ba, ya fita da sauri ya shiga motarsa. Har ya sanya ribas zai fita sai kuma ya fito ya tambayi mallam ko ya san gidan Zainab. Ya dai kwatanta masa. Kuma da yake ma ba boyayye bane mai gidan bai sha wahalar samun gidan ba. A baking gate suka yi kicibis da Al Bashir yana yiwa maigadi bayani wajen wacce yazo. Da hanzarinsa ya karasa wajensa. Har kasa cike da girmamawa ya tsugunna ya gaishe shi. Shi da kansa ya wangale masa gate ya karaso ciki da motar sa. Tun daga harabar gidan ya san cewa Allah yayiwa Zainab sakayyar kuntatawar da sukayi mata shi da matarsa. Da kyar ya daurewa kwallar dake barazanar zubo masa. Shi kuwa AlBashir kamar zai kwanta a kasa ya takashi saboda ladabin da ya ke a gabansa. Babban falonsa ya shiga da shi. Shi da kansa kuma ya bude fridge ya dauko ruwa da wani lemo na cucumber ya hada ya doro a jug. Ya kuma shiga kitchen da kansa ya debo danbun nama da kyar ma ya gano shi sai da shamsiya mai aikinta ta nuna masa inda yake. Yana jiyewa ya tuna da wani dabinon ajwa da basa rabuwa da shi. Ya sake zabura ya dauko ya dire masa. A gefen kafarsa ya zauna aka sake sabuwar gaisuwa. Sai sa masa alabarka ya ke yi yana amshewa. “dadi Bisimillah sha ruwa bari in kirawo zainab din”. Ya fada yana mai mikewa domin haurawa sama. ‘yar hutu kuwa tana zaune ta tsala ado da wani dan Karen leshi mai laushi da kuma tsadar gaske. Ita dai ta san sun yi sallama da shi akan zai fita sai kuma gashi ya shigo. Cak ya daga ta daga kishingidar da tayi ya mikar da ita tsaye. “Putri yau idan na baki wani albishir wanne goror zaki bani”? “sai da ta dan sumbance shi san nan tace “kai da ka mallakeni kuma ai komai nawa naka ne, sai dai in tayi maka salatin Annabi in yi tawassali da shi Allah ya yafe maka kura kuranka. “Godiya nake Putri. Muje innuna miki albishir din”? “Allah ya sa ba mota ka sake sayo min”? “Wan nan yafi duka wani kyalkyalin duniya da kika sani daraja”. Tare suka sauka saka. Hango Dadi da tayi ya sanya ta karasa sauka matattakalar benen da sauri cike da ihun “dadiiiii”. Sai dariya yake ya na fadin “yi a hankali Zainabu”. Sufa tayi a gabansa ta tsugunna tare da damke hannayensa duk biyu a cikin nata. “Dadi da gaske kaine”? Shi ma cike da dariyar murna ya fara tsokanarta yana fadin “ke kuma haka akeyi, saiki gudu sama ki bar mijinki da hidimar saukar baki”. Shi ne yayi saurin cafewa lokacin da ya zauna a gefenta yana fadin “Dadi ba laifin ta bane. Ka san akwai bakon da ya zarce saukar matar gida sai ta maigidan kansa”. Dariya suka saka dukkansu. Sai lokacin Zainab ta samu sukunin gaishe da mahaifin nata amma har a wan nan lokaci tana rike da hannunsa taki saki, kamar yace guduwa zai yi ya barta. Al bashir ne ya mike tare da fadin “let me see if Umma is around”. “da ka barta sai mu shiga”. Bai bata amsa ba ya mike yace da Daddy yana zuwa. Yana fita ya mai da hankalinsa kan Zainab. Muryarsa kamar zai yi kuka yace “ashe har turanci kina ji yanzu”. “gaskiya Dady ba laifi. Although it is not that fluent amma dai i can converse effectively”. Cike da murna yace “da kyau Zainab. Ga kuwa turancin nan radau”. Sai kuma ya dada marairaice fuska, yace “zainab”. Ta dago ta kale shi ba tare da ta amsa ba saboda jin seriousness din dake muryarshi. Tana sauraron kalaman da zasu fito daga bakinsa sai kawai taji muryarsa tana cewa “Zainab rokon gafarar ki na zo nayi akan irin wulakantanciyyar rayuwar da na barki ki ka yi a gidana. Ni da kaina na nakasa ki saboda haukan kishin mahaifiyarki da ya rufe mini do, da kuma wan nan munafakar uwar taku da ta ringa ingiza ni ina zaluntarki”. “Don Allah Daddi kar ka sake cewa in maka gafara. Bani da wata afuwa da zan maka illa kai ne ma zan dawwama neman yafiyarka ko na kuskure maka”. “sam Zainab baki taba bata min ba. Tun da nake dake ko musu baki taba yi dani ba komai gaskiyarki. Nine dai na dinga take hakkuwanki da suka wajaba a kaina”. “Don Allah Daddy kayi min afuwa ka daina maimaita Kalmar cuta da ka ke ganin kayi min. har abada bani da wani mahaifi sama da kai. Abubuwan da suka gifta na kuskure sun wuce har abada”. “Kin san Allah ba da sanina na dinga yi miki