Sashe 29
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
[8/8, 21:58] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKIN A MIJI💏💏 PAGE 27 BY HANNE ADO ABDULLAHI Zainab na ganin Fatu da mama Hajjo ta taso ta rungume su cike da murna. Sun tsaya zasu fara kaudi Hafsa ta shigo da sakon Al Bashir yana son ganin Zainab. A babban falon Abbansu ta same shi, ya zuba kwalliya sai tashin kamshin yake. Da sallama ta shiga, yana jin sallamarta ya dago suka kalli juna. Bai sani ba ko idanunsa ke masa gizo amma sai yaga ta kara wani kyau na fitar hankali ga kuma wa ni irin serenity in her face da ba zai iya describing ko na meye ba. But to him she look more at peace. Abin da bai sani ba, kwanciyar hankali yanzun nan take bayyana a yanayin mutum kamar yadda tashin hankali yake bayyana. Duk da kunya ta dan fari dake tsakanin Khadija da Zainab, amma tabbas sun ji dadin dan kankanin lokacin da suka samu sakewa da juna. Ajiyar zuciya ya saki, san nan ya mika mata hannunsa alamun suyi masabiha yana fadin “assalamu alaikum”. Ita ma nata hannu ta mika masa alamun amsar musabihar tasa tare kuma da amsar sallamar da yayi mata. Yana damkar hannunta ya jawo ta jikinsa ya rungumeta tsan tsan a kirjinsa. Duk da dai Zainab na da tsayi dai dai misali, amma tsayuwar su tare sai ya mai da ita wata gajera a gabansa. Ta fara kokarin zare jikinta daga gare shi ya kara rike ta tsam, yadda ba za ta iya kwacewa ba. Yace “haba amaryar Bala Mai gwanjo, ina zaki gudu ki bar Balanki”? Ita ma muryarta can kasa kamar mai rada kuma cike da jin kunya tace “wan nan ba Ya Balarabe na be. Ni nawa kawaici gareshi da kunya”. Dada rungumeta yayi yana dariya, san nan yace “ahaf manta da shi shi a lokacin ba a halasta masa yin hakan bane shi yasa ki ka ga yana wani kamewa wai shi ala dole ga mai kiyayen hududullah”. “amma ai dai ya tsaya inda aka umarce shi din ko”? “ni kuma ina ne iyakata”? ya tambaya tare da tsare ta da idanun bayan ya dan sassauta rikon da yayi mata. Shiru ta kasa ba shi amsa. “ba ki da amsar hakan to ni ina da ita”. Ya sa dan yatsansa dan ali ya shafo tun daga goshinta zuwa hancinta ya dangane da bakinta zuwa habarta wadda ya dago ta da yatsansa ta kalle shi sosai ciki idonsa. Sai da ya dan yi kissing bakinta, san nan yace “Putri Salju Al Bashir da aka aura miki bashi da iyaka a kan ki”. Kunya ce ta kamata sai kawai ta boye kanta a cikin kirjinsa. “a’a kar muyi haka mana, daga na kawoki garin Fulani sai kuma ki kama al’adarsu”. Ta samu ta dan zame kadan san nan tace “dama nima tawa ce ala’adar”. Tafi yayi mata yace “eyeh Putri saya. That’s more like it. Na fi son duk maganar da nayi ki bani amsa”. Take ta canza topic tace “yaya gajiyar bikin da kuke yi”? “gajiya tabi lafiya zamuje mu kai amarya Kaduna an jima kadan. Na dai bar su Sa’ad sun dauko wani choreographer wai ya koyar da su rawar Fulani, saboda sun rantse biki zasu yi da gaske a Kera”. Dariya ta saka a hankali tace “haba wasa dai suke yi. Ina su ina bikin kauye:? “ashe kuwa zaki sha mamaki. Baki san friends dina da son challenge ba. Already har sun yi oder costume da zasu yi amfani da shi. So gwanda ma ki sanar da su Fatu they should get ready for a duel”. Nan dai ya zauna har kusan azahar suna ta hirarsu cikin annashuwa da jin dadi. Kuma duk abin nan da ake hannunta na cikin nasa bai saki ba. Ita kanta yanayin da ta ji na wani nishadin da bata taba jin irinsa ba, sai ya sanya ta daina kokarin kwace hannu ta bar shi yana wasa da shi. Da kyar ya iya mikewa bayan 12.30 shi ma sabo da nacin wayar su sa’ad ne da su Mujib ya hakura. Har bakin mota ta raka shi, anan ne kuma wata wayar ta sake shigowa. Ganin angon ne da kansa ya sa a speaker. Daga can banagaren aka ce “wai kana ina ne. ka san so muke by 1.30 latest mu bar garin nan, amma kai an neme ka an rasa”? “kai jiya da aka neme ka aka rasa waye ya dame ka da cigiya? Ba kyale ka aka yi ba. I beg give my space. You know the feelings that iam experiencing so why are whining like a wounded cat”. “yi hakuri mutumina. Da zaka yi dabara ma kawai ka dauko abin da ke saka feelings din mu wuce tare kawai da ya fi sauki”. Kallonta yayi yace “kina jin su wai in dauke ki ki raka ni. Taimake ni muje amaryar Bala Mai gwanjo”. “Bala mai gwanjo ai ka kasa shi wan nan dai ta Ya Al Bashir ce. Kuma ma …..”dariya suka ji ansaki daga cikin waya ta mutane da dama wadda ke nuna alamar can ma a speaker suka saka shi. Muryar Mujib taji yana cewa “taimaka ki sake shi ya taho ko ki biyo shi ku taho tare Allah I promise ba zan gaya wa kowa ba, kin san hanyar kaduna idan dare yayi ba kyau gareta ba”. Dariya kawai tayi ba ta ce komai ba. Da kyar dai ta samu ta lallaba shi ya bar garin. Tun da ya tafi kuwa yake waya da ita har ya isa Kano. A Kaduna suka kwana saboda dinner da aka yi a can, amma washegari karfe 8.30 a garko tayi masa. Nan fa Hafsa da Fatu suka shiga hidima da shi. Aka ajiye masa kayan breakfast, amma shiru bai ga wacce yazo wajenta ba. Can dai hakurinsa ya kare yace “wai ke Hafsa ina kika boye min mata ne”? “ai matar ka sai dai hakuri. Mama Hajjo ta fara mata gyaran jiki ta ce kai da sake ganinta sai an kawo ta gidanka”. A firgice ya dago yace “you must be kidding me”? “Sorry I am not” ta amsa masa. Ya juya wajen Fatu da ke masa dariya saboda firgicewar da yayi. Yace. “Fatu wai da gaske ne? amma in ki ka ka yi min haka kin kayuta ke nan, har da ke za a hada baki a hana ni ganin rabin raina”? “Kayi hakuri ba hadin baki bane. Sun dai ce wai idan ana biki ba a cika son ango yaga amarya ba, wai hakan na kara dankon soyayya a tsakaninsu”. “And whose theory is this”? Hafsa ce ta ce “absent makes the heart fonder”. “Kin ganki nan ba za a iya kada ki a magana ba. Zan hadu dake ne. akwai ran da zan rama”. Haka dai suka taya shi hira suka samu ya karya, saboda from all indicationsa asubanci ya yiwo daga Kaduna. Amma sai yai wa Mama Hajjo ta dan Zamani. Bata hana shi ganin amarya ba, sai ya fara engaging dinta a video call. Kusan kullum zasu dauki sama da awa uku sun hira, ido da ido ta cikin waya. Ranar laraba aka sa amarya a lalle, a nan garin kera. Kanwar Kakar Zainab ce ta kama amarya da kwaryar nono sabuwar tatsa. Kuma kaf yayyen Albashir da kuma da yawa daga cikin danginsa sun samu halarta. Momi Rumaisa ma da ‘yar tata gayyar taje saboda fadan da mijinta ya yi. A wannan lokaci ya samu nasarar nuna mata bacin ransa na abin da tayi. Ranar jumma kuwa tun da safe sai ga wasu mutane da tantuna da kujeru cikin motocin daukar kaya guda biyu. Baffa da ya san da zuwansu ya sa an share makeken filin da ke kofar gidansa wanda ke daura dana amininsa kuma kakan Zainab na wajen uwa. Suka jere kujerun nan gwanin ban sha’awa, a karkashin tantin nan. Suka yi traditional decoration da zai nuna maka Fulani heritage. Aka tanadi guri na musamman domin zaman ango da amarya. Kafin magariba kuwa motoci suka dinga shigowa garin dauke da ‘yan biki kamar masu zuwa hajji saboda yawansu. Nan fa aka shiga fito da gasassun raguna da danyar madara da soyayyun zabbi, ana kawo wa baki. Haka suma matan da aka sauke su a cikin gida. Sai bayan an yi sallar isha, san nan aka fito zuwa harabar da aka tanada domin wan nan sha’ani. Filin yayi tar da haske saboda fitulun da aka kakkafa. Aka yi wa mutanen kauyen da suka zo kallo wurinsu daban na baki daban. Mai kida kuwa sai dukan kayan kidan sa yake yana busa sarewa tare da waka mai dadin gaske da fillanci, saboda speeker da aka saka masa kana jiyo sautin kidan nasa da ga nesa. Can ana tsaka sai ga amarya ta shigo cikin shudin saki buba da zani da kuma dankwali san nan aka yafa mata wani a kanta, amma ba lullubi ba. A kan kawai aka yafa shi aka barshi ya sauka ta bayan wuyanta. Ga wani kyakkywan murjani da ke rataye a wuyanta. Tayi kyau bana wasa ba. Kwalliyar so simple but classy and elegant. Shi ma angon yana gefenta sanye da nasa sakin shudi kamar nata, wan da shi kuma riga da wando ya dinka, san nan ya dora babbar riga ta shadda light blue a kai. Abokan nan ango kuwa idan ka gansu zaka rantse ba su taba shiga birni ba. Sun sha kwalliya da riga da ake kira lauje waje, wando kafi shanun wuya da kuma hula habar kada. Suka shigo cikin wata rawar Fulani mai birgewa kowa rataye da sanda a wuyansa. Haba kan kace meye wan nan filin ya kacame, sai ruwan kudi ake yi musu. Suka yi da’iar suka saka ango da amarya a tsakiyarsu. Su dai basa rawa da tsalle yadda abokan suke yi, amma suna dan rausayawa. Gaskiya lilisco Choreogrpher da suka dauko yayi kokari, domin kuwa ko samarin kauyen ba za su iya irin rawar da suka diba ba. Kuma wani abin birgewa sun daga rawar tasu to another level. Innovation din da suka yi shi ya kara mata armashi. Can ana tsalle rawar Fulani da kafa daya sai kaga gaba dayansu sun tsuguna sun debo shoki,