Sashe 3
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hijabinta ta janyo har sai da ya yage daga wuya tana fadin "zo ki tafi da wan nan tarkace da kika zo da shi. Ko kinga munyi miki kama da matsiyata irin mijinki da zaki dauko wasu kazaman kayanki ki shigo min da su gida. Idan ma wani asirin kika dibgo kika kawo mana to ni na ci dubu sai ceto." "Allah ya shirye ki". Shine kawai abin da ta fada ta fizge hijabinta ta nufi gate da niyyar fita. Bata ankara ba taji wani abu kakkaura kuma mai sanyi na zuba a jikinta. Tana dubawa taga nonon nan jarka guda Rumaisa ta juye mata a kanta. Sai a lokacin ta tuna ashe a freezer ta saka shi ya kwana saboda ya iso ga wadanda ta yiwa tsarabarsa ba tare da yayi tsami ba. Bata gama da wan nan ba taji daya daya jarkar ta doki dunduniyarta. Ashe wurgar ta tayi da ita. Itam kuwa daya jarkar take ta fashe nonon ya kwaranye a kasa ya kuma hade da jinin da ya zubo daga kafar Khadijan inda jarkar taji mata ciwo. Shi kansa maigadi yayi mamakin karfin da Rumaisa tayi amfani da shi ta fizge kwandor albasar tayi kokarin jifan Khadija da shi. Shi dai Allah ya bata sa'a ta kauce masa. Haka nan jakwane jakwane ta fita daga gidan cikin rakiyar zage zagen Rumaisa. Tana mamakin wan nan kiyayya da take mata. Gida ne ta fita ta bar mar ta. Abin da bata sani ba, tun ranar farko da aka kawo Rumaisa gidan nan ta yaye mayafi suka yi ido hudu da Khadija taji tsanar ta ta zargu a idonta. Kyawunta ba karamin razana ta yayi ba. Ga shi ita kuma mace ce mai kyayshin tsiya. Bata kaunar kowa ya fita da komai. Tafi son zama star a duk inda ta ratsa. Amma kyan Khadija ya tsorata ta. Mace kamar ita ta zabi duk wani bangare na jikinta. Tsayi daidai misali. Kirar jiki abar tinkaho. Kala abar alfahari. Gashi burin 'yanmata. Murya muradin mawaka. Sai kuma uwa uba hali irin na salihan bayi. Wadan nan qualities din su suka janyo tsanar da Rumaisa tayiwa Khadija. To kuma sai aka dada rashin sa'a. Duk wadan nan martabobi duk da Zainab karama ce, amma sun fara huda a jikinta. Ai da farko dawowarta gidan , aji daya aka saka su da kannenta. Gashi dai daga local government tazo , amma ba a yi wata guda ba ta zarce kowa a ajin har da kuwa Farida da kuma Farisa. Saboda tsiransu wata goma ne kawai ya saka aka saka su a makaranta tare. Kwazon ta shine abin da Mummy ta fara attacking ta hanyar tabbatar dabata samu damar zuwa makaranta a kowacce rana ba. Ko hana ta damar yin home work da dai sauransu. Duk da cin mutuncin da tayi wa Khadija bai ishe taba. Maigidan na shigowa ta tare shi da kukan ta tana rattaba masa wai Khadija tazo ta kare mata zagi da cin mutunci. Akan wai ance tana zaluntar Zainab. Sai da ta fyace majina san nan cikin muryar kuka tace "yanzu saboda Allah duk yadda nake kokari na akan yarinyar nan amma ba'a gani. Yadda nake tattalata har yafi yadda nake wa su Farida amma duk da haka yarinyar nan da bakinta ta kalle ni a gaban uwarta tace wai ina wahalar da ita. Kuma ni ba wan nan ne yafi bata min rai ba irin gaya mata da tayi wai kana banbanta, ta da sauran yaran gidan nan". Sai da ta fashe da wani kukan san nan ta sake marairaecewa tana fadin "yaushe aka yi. Me aka yi wa su Farida ba a yi mata ba. Wannan magana ta bata min rai. Amma ai ita Khadijan ta fi kowa data dauki maganar yarinya ba tare da ta binciki Komai ba". Tafasa yake ita kuwa tana dada tunzura shi. Habawa ai kuwa da ya tashi a fusace dakin yaran ya nufa. Zainab na kudundune a kasa tana kukan raba ta da mamanta da aka yi,"sai saukar bulala taji. Tayi ihu tayi magiya tayi afi amma bawan Allah nan bai san tana yi ba. Mummy da mugunta tana karasowa da gudu abu na farko da ta fara yi shine jawo kofar ta rufe ta kuma rike handle din tana fadin "don Allah Abban Farida ka bude kofar nan". Tabbas ba shi ya kulle kofar ba ita ta rufe amma bacin rai ba zai barshi ya tuna mai ya faru ba. Sai da yaga Zainab bata motsi san nan ya fice daga dakin yana fadin "don uwarki gobe ki kara. Sai na miki abin da ya fi haka". [8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👧 IN FIKI A MIJI💑 PAGE 4 BY HANNE ADO ABDULLAHI Khadija ta dade tsaye a bakin gate din gidan su Zainab ba tare da ta san abin da zata yi ba. Shi kansa maigadi shock din abin da matar gidan tayi ya hana shi magana. Ta daure ta bude jakarta ta daiko wayar ta nokia 3310 ta kira mijinta Mallam Usman tana mai sanar da shi cewar ya gayawa abokinsa da ya kawota ba zata tsaya jiran sa ba zata dawo on her own. Yayi kokarin tambayarta ko wani abu ya faru amma ta katse shi da fadin yayi hakuri sai ta dawo. Ya buga ya sanar da abokinsa Malam Buba mai golf abin da Khadijan ta fada. Take kuwa ya fasa lodi ya fita daga layin lodin da ya hau ya dawo gidan Dr Abdullahi Zubairu. A halin da ya ga Khadija shi kansa hankalinsa ya tashi. Ta na ganinsa sai a lokacin kuka ya kwace mata. "Shiga mu tafi maman Hafsa" ya fada yana mai bude mata gidan baya. Shi kansa ya rasa kalmar da zai bata hakuri da ita. A kundila ya tsaya gidan wani abokinsa. Ta shiga tayi wanka matar gidan ta bata wasu kaya ta sa. Hankali tashe su ka tarar da Malam Usman yana dakon zuwansu. Sai a lokacin shi kansa Mallam Buba ya san abin da ya faru. Duk kan su sun yi bakin cikin jin wulakancin da aka yi mata saboda kawai ta kaiwa 'yarta ziyara. Ya bata hakuri wan nan ta wuce. Ba sai kuma ga tsohon miji sun hadu da sabon miji a gidan su Alhaji Abdullahi. Duk da aurensa da Khadija ya rabu hakan bai raunana zumunci tsakanin mahaifin Khadija da kuma na Abdullahin ba. Shine ma waliyyin ta a auren ta na biyu da shi Mallam Usman din. Kanwar Abdullahin ce ta rasu, Allah ya hada su a zaman makoki. Ya riga yaji famfon matarsa ga shi dama kuma yana kullace da shi kansa Usman din. A cikin gida suka hadu shi da Usman din ya shiga ciki gai da iyayen su mata. Bai ko lura ya hankalta da jama'ar dake dankare a tsakar gidan ba ko kuma ya na sane niyyar ci masa mutunci yayi oho. Mallam Usman na kokarin mika masa hannu domin su yi masabiha yaji kalaman Abdullahi mahaifin Zainab sun dake shi kamar bulala. Yana buda baki sai yace "dawa zan gaisa da kai?ai kai kanka ka san nafi karfin gaisawa da matsiyaci irinka". Kowa ya san Malam Usman, Usman din ne har a sanyi hali. Ga kuma kunyar gidan surukai dake dawainiya da shi. Domin yadda yake mutunta mahaifin Khadija haka yake yiwa tsohon surukinta. Saboda haka yana budar baki cikin sanyin murya yace "kaga Dr kayi hakuri koma menene mu tattauna cikin fahimtar juna. Ni da kai ai mun zama daya". "Dawa ka zama data ? Kaga Mallam dakata ka kalle ni da kyau ai ka san ni ba sa'anka bane." Ya na fadin haka ya cakumo wuyan rigarsa yana fadin cewa "kuma ka gayawa matarka ta kiyayi mata ta. Ranar da duk ta sake taka min gida sai na sa an wulakanta ta yadda bata tsamm........" "Sakarwa mijina rigarsa ko kuma infasa maka kai da tabarya". Yaji ihun muryar Khadija ta nufo su kuma dauke da tabaryar. Duk su biyu basu ankara da cewa hayaniyar su ta fito da Khadija da kuma mahaifiyar Dr da ma sauran mutanen da ke cikin dakin ba. Ta kuwa nufi shi dauke da tabaryar gadan gadan. Da hanzari mahaifiyarta watau kakar Zainab ta wajen uwa ta karbe tabaryar tana fadin "ke Dije baki da hankali ne". Yayin da shi ma cikin mamaki yace "Khadija ni ki ke son wulakantawa akan wan nam banzan talakan mijin naki"? "Ga ka nan banza wanda bai san ciwon kansa ba. Kuma ka zauna ka tace haram din da ke cikin kudin da kake ikirarin kana da shi ka gani ko bayan yin hakan halastacciyyar dukiyarka za ta kai tasa"? Inna mahaifiyarta ta ce " kar in sake jin bakin ki a nan". "Amma inna kina jin zagin da yake min bayan wulakanci da matarsa tayi min". "Ke Khadija wuce ki tafi gida. Kar in sake jin kince wani abu". Mallam Usman yace da ita. Ta yi tsai na dan lokaci ta kalli mijin nata sai taji ba za ta iya yi masa musu ba. Takaicin ya hana ta gayawa Abdullahi bakaken maganganu da ta tanada sai kawai hawaye ya fara zuba a idonta. Kallon baban Zainab kawai tayi ta saki wani dogon tsaki. Takaici ya kama shi ya daga hannu da niyyar kai mata mari wani irin riko aka yi wa hannun nasa wanda bai taba jin irin sa ba. Ya juya ya kalli Mallam usman wanda ya rike masa hannu yana fadin "sake ni in koyawa yarinyan nan hankali". Shi dai bai bashi amsa ba amma kuma bai saki hannun nasa ba. Innar Khadijan ce ta sake cewa "baban Hafsa kuzo ku wuce gida kai da Dije ba na son rigima". "Su wuce ina"? Mahaifiyar shi Abdullahin ta fada watau kakar Zainab ke nan ta wajen uba. Taci gaba da cewa "ita kuwa Dije ai nan gidan ubanta ne ba kuwa wanda ya isa ya sa ta fice daga cikinsa. Shi dai da yake jin rashin mutunci ya iya ficewa. Shi kuwa baban Hafsa gidan surukansa yazo. Kuma tunanin haka ya sanya ka kuma ci darajar hakan har ka iya shake masa riga bai nuna maka banbancin karfin tuwon dawa da na samanbita ba. In bai cin haka har kai ka