← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 43

Sashe 27

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fatu tayi sallama. Sai da suka amasa san nan ta shiga tana fadin “ai na gaya maka lakanin da malamin nan ya bani kamar yankan wuka yake. Amma ba yanzu zan karbi ladan aiki na ba sai nan gaba, da kuma tarar kin sanar da mu sunanka na asali har kana sakamu suma”. Hararar wasa ta sakar mata. Ita kuma ta ci gaba da fadin “ai yanzu ka gano matsayin da kake mitar an ki a nuna maka. Tun da yau dai ka tabbatar in ba kai ba sai kabari. Tun da rijiya ma idan an shiga a iya fito da mutum da rai”. “Ni dai bani da abin cewa sai godiya”. “za dai kazo godiyar amma ba yanzu ba. Ku zo daddy ya aiko a kira ku”. Hijabin ta ta mika mata suka fito suka nufi gidan su Zainab cike da farin ciki. Anan kuma suka tarad da iyayensu da kuma Alhaji Bashir da Alhaji Usman, wadanda sakon kiran uban amarya ya same su lokacin da suka fita za su raka his excellency, wanda zai wuce wajen dayan daurin aren wanda shine ya fito da su dukkansu. Sai da motarsa ta tashi san nan suka koma cikin falon, inda suka samu hajiya Rumaisa tana ta gursheken kuka da ikirin dole a raba wan nan aure. Baffan Nene ji yake kamar ya tashi ya rufe ta da duka. Shi Alhaji Bashir ne yace a bata damar ta fadi dalilin ta na son raba auren Tace ba zata fada ba sai an kira Al Bashir yazo. Ana wan nan takaddama shine aka tura kiransu. Suka shigo cikin farin ciki wanda ya gaza boyuwa a fusakarsu duk su biyun. Alhaji Usman ne yace “hajiya gasu sunzo fada mana dalilin da kike son sai an raba su”. A razane duk suka dago idonsu su ka kalleta watau ango da amaryar da ba su san kiran na meye ba. Allah ya sa tare suka shigo shi da Mujib. Kamar daga sama yaji muryar Momi na fadin “saboda ya yaudari ‘yata, shi yasa nake son a rabasu”. “Wacce yaudara yayi mata”? nan kuma Baffan Nene ne ya fada cikin bacin rai. “Ya san shi ba namiji bane ya yaudareta ya aureta”. Dukkan su na falon haka suka ji saukar zancen Momi kamar dukan guduma [8/8, 21:57] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 26 BY HANNE ADO ABDULLAHI Dakin ya dauki shiru na dan wani lokaci. An rasa mai abin cewa. Shi kuwa Al Bashir sai kwankwasar daben kasa yake yi da knuckles din shi. Mujib da ya san shi tun suna yara, ya san alamun kurewar bacin ransa ke nan. A hankali ya dora hannayensa a kan nasa ya dan matsa. Ya dago ya kalle shi idanuwansa jawur kamar an zuba masa gauta a ciki. Girgiza masa kai yayi alamar yayi hakuri. Ga wani uban gumi da ya wanke shi sharkaf duk da sanyin falon. Ita kuwa amarya dago kanta tayi ta kai kallonta zuwa angon, tana mamakin furucin Momi. Tunani ta ke a zuciyarta “to in ba namiji ne ba shi menene? Mutum ga saje ga kira irin ta maza murya irin ta maza sutura irin ta maza kuma ace ba namiji bane”? Wan nan shine tunanin da zuciyarta ke wassafa mata. Bata san sanda wata karamar dariya ta subuce mata ba, saboda sakarcin Momi da take gani. Tayi saurin kunshe dariyarta kar iyayenta da kakanninta su jiyo ta. Amma tabbas bata ga ta inda za a ce ya balarabenta ba namiji bane. Dogo mai kyakkyawar kira ta mazan kwarai, kuma momi ta kalle shi tace ba namiji bane. Shine abin da zuciyarta ta ci gaba da wassafa mata. Tana cikin wan nan tunani taji muryar Baffan nene yana cewa “Rumaisa kiji tsoron Allah. Ta yaya kika san wan nan maganar”? “Baffa tsoron Allah ne yasa na furta wan nan maganar a gabanku sabo da bana son cutar da Zainab”. Muryar Al Bashir can kasa yace “na nawa kuma”? Mujib ne ya yi saurin sakin gyaran murya wadda ta dakushe kalaman Al Bashir ba wanda yaji mai yace sai shi kadai. Hanakalinsa bai dada tashi ba sai da yaji muryar mahaifin sa yana fadin “Balarabe kaji tsoron Allah. Idan har ka san ba ka da lafiyar sauke hakkin auren yarinyar nan ka shaida mana tun da wuri kar ka cuce ta”? Dago idonsa yayi ya sauke su akan mahaifinsa, wanda shima ya hango tsananin bacin ran da ke tare da shi, amma ba ya son ya zama mai son kai a tsakanin ma’auratan yafi son kowa a bashi hakkinsa. Baffa ne ya sake cewa “Rumaisa ke muke jira muji dalilin ki na cewa shi din ba namiji bane” “Mh ai Baffa zancen ya zaga garin nan, tun da ba wanda ya taba ganinsa da wata yarinya ya nuna yana sonta, shi ne nima na samu labari”. “ita ke nan iya hujjar da kika dogara da ita”? “ka ga baffa bari muji daga bakin yaron, kar a cuci yarinya” Alhaji Usman ya dada fada. “Haba Alhaji saboda kawai yaro ya kame kansa baya shiririta sai a dau kazafi a lankaya masa. Kai AlBashir ka kare kanka mana. Tun da ita bataji kunyar zargin ka ba, kai ma kar kaji kunyar maida mata martini”. Ya dago kansa ya galla mata harara kamar zai tashi ya rufe ta da duka saboda tsabar takaici. San nan murya can kasa yace “Baffa ni bani da abin cewa sai dai a bani lokaci shi zai tabbatar da gaskiyata ko karyata”. “Wan nan hakane” in ji Baffan Khadija. “ai kuwa wallahi ba zai yiwu ba. Ba zan zauna ina gani a cuci yarinya ba. Dole ne ya sake ta”. Ta fada cikin muryar kukan da ban san ko na karya bane kona gaskiya. Baffa Nene ne ya sake harzuka ya mike tare da fadin “Allah ya sa kin gane ba wanda ya isa sakin auren sai mai shi da kansa ba. Bani ba. Ba ke ba, ba kuma shi kansa mahaifin yarinyar da ya zuba miki ido kina ciwa mutane mutunci ba”. “Don Allah Baffa kayi hakuri. Duk maganar bata bacin rai bace kayi hakuri”. Alhaji usman ya fada. Take ya juya harshe cikin fulatanci yake fadin “kin so nakasa yarinya Allah ya kareta shine kika bullo ta nan”. Ya juya inda AlBashir ke tsugunne yace da shi “kai mike kadauki matarka ku bar gidan nan. Aure ni na baka shi, ba kuma wanda ya isa ya karbe shi daga wajenka. Wuce ku tafi”. Yana fadin haka ya nufi hanyar fita. Har ya kai kofa ya dawo inda Zainab ke tsugunne ya daga ta ya fita da ita ya dago hannuta ya hada dana Al Bashir yace ban yarda ka tafi ka barta a nan gidan ba. Yanzu ku kama hanya. Kaje duk inda Allah ya hore maka ka ajiye matarka”. Aikuiwa yana mika ta, caraf ya sa hannu ya damke nata. Shi kuwa yayi ficewarsa daga falon yana fadin “ina Mallam Usmanu yazo ya mayar dani in rabu da ganin wanan bakin cikin”. A tare duk suka fice daga falon, suna jiyo muryar Momi tana tashin hankali. Su dai suka fita suka barta da mijinta wanda tun da aka fara Magana bai ce komai ba, saboda tsoron kar Baffansa ya tsinka shi idan har ya goyi bayan matarsa. Shi ma kuma wannan lokacin ba zai goyi bayan nata ba. Saboda ko banza His Excellency ne madaurin aure. Wanda hakan ya sa zai dada samun kusanci da shi. Shi wannan aure na Zainab ai an taki sa’a. wadan nan dalilai suka sa shi yaki siding da kowa. Shi ma a nan ya tafi ya bar Momi tana ta hargowarta. AlBashir rike da hannun Zainab cikin rakiyar Mujib suka nufi motarsa Mercedes benz G63. Sai da ya zaunar da ita a kujerar baya san nan ya zaga daya gefen ya zauna, yayin da Mujib ya shiga mazaunin direba. Ba wanda yace da kowa komai a cikin motar sai sauke zazzafar ajiyar zuciya da Al Bashir yake yi. Zainab ta saci kallonsa sai kawai zuciyarta ta raya mata wai gashi nan daure da dankwali da zani da riga irin na mata. Picture in her mind is so funny saboda haka ba ta san sanda dariya ta kwace mata ba. Sai a san na shi ma ya saki ransa ya shako wuyan ta cikin wasa yana fada “dariyar me kike min”? Muryarta can kasa cike da dariya take fadin kayi hakuri, hotonka na hasko da gwaggwaro da high heel shine dariya ta kamani”. Tare suka dago ido suka kalli juna shi da Mujib sai a nan suka fahimce Zainab ba ma ta san accusation da Momi tayi masa ba. Ita kallon physical halittarsa kawai ta ke and not something else. Dariya suka bushe da ita a tare. Mujib yace “yaya ina zan kaiku for your honey moon ko mayi saurin proving Momi wrong”. Kafin ya bashi amsa, wayarsa tayi ringing sai da ya daga wayar san nan ya tuna da appointment din da yake da shi da wanda ya kira. Ya na dagawa yace “yi hakuri ranka dade. Shaf na manta I was coming to see you, wani lamari ne ya sha kai na”. Ya dan yi jim alamar sauraro san nan ya sake cewa “a’a gani nan zuwa yanzun ma kuwa”. Ya kashe wayar ya maida cikin aljihunsa. Yana murza hannun Zainab dake rike a hannunsa ya ce da Mujib “please lets go to immigration office I need to get a passport done” “Amma na dauka yau public holiday they wont be around”? “no suna nan because of hajj operation they work round the clock”. Mujib zai sake Magana ya hango Al Bashir ta cikin madubi yana rada wa matar sa wata Magana wadda ta sata dariya, sai kawai ya fara waka yana kida, da steering motar. Yana fadin “ranar muke jira yau 'nima da tamburana gani na zo’ 'ango muke yiwa shi 'Muyo rawa da murna anyi aure’ Gaba daya dariya suke masa na ganin ya daddage ya na ta zuba waka. A haka suka isa farm center inda passport office yake. Duk da wajen a cike amma an kaisu VIP room dinsu. Ita dai biye take da su tana mamakin yanzu hoton passport kawai
Chapter 27 · 0% Book details