Sashe 23
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kuma Sakina da yaranta guda biyu. Ba zata suka yi mata saboda Momi ta so kamata da laifi, amma batayi sa’ar yin haka ba. Saboda ita dai yadda ta saba haka taci gaba da kula da gidan. Bai dameta ba da aka zo ana rabon tsaraba ita ba a bata komai ba, saboda ta saba da haka ranta bai baci ba. Ita kuwa yanzu ba abin da ke damunta in dai zata samu damar ganin rabin ranta to kuwa ba abin da zai bata ranta. Kusan duk abin da Momi ta nunawa Dadi da sunan zainab ta sayawa, ashe karya take ‘yan gidansu ta rabarwa. Ba abin da ta bata. Da suka zauna da Dadi tace masa “waini Zaunab tazo tayi maka godiyar tsarabar da aka kawo mata”? “Ni bata zo tace min komai”. “kai ni na rasa bakin halin irin na wan nan yarinya. Yanzu duk abin da aka saya mata amma bata yi appreciating ba saboda kawai ba ayi tafiya da ita ba”. A dan hasale Daddy ya amsa wa Momi da cewar "tafiya ba ita jawo wa kanta ba. Itama da ta yi karatu ai da da ita za a dinga zuwa ko ina. Amma tunda haka ta zaba, sai ta zauna tayi ta sakarcinta. Ai tun da ma ta samu mai sonta, gwara kawai a aurar da ita”. Yana fadar haka Momi taji faduwar gaba, saboda kuwa ba ta tsammaci jin haka daga gun daddy ba. Idan ta tafi wa zai ci gaba da yi mata bautar da Zainab ke mata. Ai kuwa zata san yadda zata lalata zancen auren nan. [8/7, 21:39] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 23 BY HANNE ADO ABDULLAHI Tun da mutan gidan nan suka dawo, Zainab bata huta ba. Allah ya taimake ta ko ina na gidan a share yake kal kal da shi. Da farko suna shigowa aka bawa driver kudi yaje ya sayo kayan abinci. Ba ita kuwa ta samu ta gama sorting din su out ba sai bayan isha. Ta sa food stuff a store a cikin robobin da suke arranging kayan abinci. San nan ta dawo kan perishables ta wanke condiments ta barsu suka tsane san nan ta bi ta duddura su a cikin zip lock, yanda zasuyi saukin dauka idan za ayi amafani da su. Ta saka su a freezer su wacce take daban data nama. Sannan ta dawo kan nama da su kaza da kifi da dai sauran su irin su kayan ciki da su ganda. Suma haka kowanne ta wanke shi ta barshi ya tsane, san nan shima ta duddura tasa a zip lock din. Suma ta zuba a tasu freezer. Hatta fruits da vegetables sai da ta gyara. Su kuma kowanne da fridge dinsa. Ta debo ruwa da drinks masu yawa ta zuba a fridge din wajen dinning inda nan ne ya kasance nasu wurin zaman. Sauran kuma tayi arranging din su a kantar store din gidan. Hatta su tuna da su salad cream sai da ta zuba su a pantry cupboard dake kitchen san nan ta dawo dora abincin dare. Ana tamabayar me za adora Anti Sakina da bata wuce gidan ta ba tukunna tace sakwara. Su Halim sukace wake da shinkafa. Ita Momi tace ferfesun kayan ciki da soyayyen dankalin hausa take sha’awa. Haka ta zage ta bata lokaci wajen sallamar kowa. Ba dai ita ta samu kwanciya ba sai bayan sha biyu na dare saboda sai da ta jira suka gama san nan ta gyara ko’ina. Ga shi kuma an bata dokar da safe tayi doya da kwai da ferfesun naman kai. Daddy kuma ayi masa kosai. A kuma dama kunun gyada. Saboda haka tanayin sallar asuba ta dora daga inda ta tsaya jiya. Misalin tara na safe taji wayar Balanta yana kira, alamar yazo ke nan. Baba Laure ta bawa sako ta kai masa. Doyar data soya ta zuba a foil paper ta kuma hada masa da dahuwar da tayi ta zuba a ‘dan wani karamin flask da ta sayo musamman domin haka, tace ta mika masa zata kirashi a waya. Tayi hakane gudun abu biyu. Ta san da taje zai shagaltar da ita har su Momi su tashi ba ta kammala abin da ta sa ta ba. Ko kuma a fito a same shi a gidan da safe bata san yadda zasu dauki al’amarin ba. Mallam mijinta ta bawa ya mika masa sakon. Yana jin abin da ta fada ya kalle shi yace “hala mutan gidan sun dawo”. Shirun Mallam din shi ya dada tabbatar masa da cewa sun dawo. Ya sake cewa Mallam “kar ka damu In sha Allahu komai ya kusa zuwa karshe”. San nan yayi masa sallama ya nufi mashin dinsa da abin Karin da masoyiyarsa ta bashi. To ita fa tana wan nan kujiba kujiba ne kuma Momi ta kai saranta wajen mahaifinta na kinyi masa godiyar tsarabar da tayi karyar ta bata. Duk suna zaune kuwa a dinning suna karyawa ya kira ta. Ta tsugunna da ga gefe kamar yadda ta saba. Nan kuwa ya rufe ta da fadan da ba ta san dalilinsa ba. Fadi yake yi “ni kin raina ni kin dau bakin cikin ‘yan uwanki da sukaci gaba kin dorawa ranki. Kuma na fada miki in dai ni kina son mu shirya dake karatu na so kiyi kika yi. Saboda haka banga dalilin da dan anyi musu abu saboda kwazon su za ki dinga bakin ciki akai ba”. Nan dai ya dinga fada. Ya dauki kusan miti ashirin yana tsattsagar Zainab a wajen.ita dai in ban da sharar hawaye ba abin da ta ke yi. Sai da yayi iya yinsa, san nan ya sallameta ta tafi. Sai da ta gama hidimar abincin rana wajen karfe uku ta shiga daki domin ta kimtsa ta tafi islamiyya, san nan taga miss call din Bala guda goma sha hudu, sai a lokacin ta tuna tayi alkawarin kiransa. Kafin wayar tayi ringing ya dauka. Irin daukan nan in flashing ka so yi sai an ci katinka. Ta yi sallama ya amsa mata muryarsa can kasa alamun rauni. “yaya na ke jin kamar baka da lafiya”? “Ina zan yi lafiya Putri Salju? Kwata kwata yau ban ganki ba banji muryarki ba”? “Subahana Lillahi. Me yayi zafi haka? Kai dai kawai ragwanta ke damunka” “A kan soyayyarki Zainab ni rago ne na karshe ma kuwa. Kina ganin na shigo wajen aiki na kasa komai. Ga Mujib nan ya sakani a gaba sai tsokanata yake yi. Please Zainab kiyi min izni in zo in ganki ko na ji dadi da sanyi a cikin raina”. “kayi hakuri aiki ne ya dan sha kaina har na sha’afa da kiran ka da nace zan yi. Wayar kuma na sata a caji a daki saboda haka ban ji tana ringing ba. Yanzu kaci abinci”? “Ina na kasa shan ko ruwa ne tunda banji muryarki ba”? Ta yi kasa da muryarata alamar rarrashi, san na tace “yi hakuri Ya Balarabe daure ka tashi kaci abinci. Ka samu ko paracetamol ne ka sha. Duk da dai sauran kwana goma bikin saukar mu, amma yau zan ki zuwa makaranta in jira zuwan ka, in har zaka iya zuwa”. “Invitiation din da kika bani ya sanya naji na wartsake gaba daya. Nan da la’asar zaki ganni”. “yawwa jarumi na. ai na san kai jajirtaccen mutum ne. Ina ya Mujib din bashi mu gaisa”. Yana karabar wayar yace “ranki dade yau kin kada ‘yan maza har kasa warwas”. “ ni kuma ba zan amsa gaisuwar kaba, saboda naga kamar kana sakaci da amanar da na baka. Kana kusa zaka bari har yaya na ya wuni bai ci komai ba”. Dariya ya yi, san na yce “gaskiya kin so dora min laifi ne kwai. Amma ina ce ko ciwo ne ya kamaka ai akwai liktan kowanne irin ciwo. Shi nasa ciwon ke kadai ce maganinsa”. Murmushi tayi san na ta ce “Yanzu dai na baka aiki ka tabbatar ya ci abinci sosai ya sha magani. Nan da awa daya da zaku zo in ganshi garas. In ba haka ba, tarar da zan dora maka bankin duniya ma ba zai iya biya maka ba”. “tuba nake gimbiyar Balarabe. Yanzu za ki ga aiki da cikawa”. Ya ajiye wayar ya juya wajen sa ya ga yadda ya takarkare yana cin doyar data zuba masa tun safe. Dauke kwanon yayi yana fadin yanzu saboda Allah dama akwai wan nan better dish din in this office kana jina ina ta kirarin yunwa nake ji, amma kayi min shiru”. Shi ma ya fisgo flask din yana fadin “let go ka jira yanzu zan tura gidan yaya A’I a aiko mana da abinci this is for me alone”. La’asar kuwa a masallacin layin su Zainab suka yi sallah. Tun da suka hau mashin nan zuwa gidan Mujib yake mitar shi fa ya gaji da hawa mashin, saboda haka yau idan sun je su nemi turo iyaye saboda ayi mai kankat. Kafin isowarsu ta salla wanka ta feshe jikinta da turaren Tommy hilfigre da kuma splash dinta na Victoria secret garden. Ta sa atamfar ta mai dan kyau daga cikin kayan da Farida ke bata. Ta dakko dogon hijabinta da yayi matching da kayan ta saka. Tana gama azkar kiran wayarsa na shigowa. Ta kofar baya ta bude ta nufi wajensa a inda suka saba haduwa. Yana ganita ya saki murmushi. Bayan sun gaisa kafin suce wani abu, aka turo kofar gate din. Daddy ne ya shigo ga dukkan alamu daga masallaci yake. Su duka su biyun suka karasa in da yake suka durkusa har kasa suka gai da shi. Shi kansa ya yaba da yadda ya gansu. Saboda da duk wanda ya gansu ya san ba mutanen banza bane. Amma kuma hudubar Momi ta yau da safen nan na yawo a kansa, in da tace masa “da gasken Dadin Farida aure zaka yiwa Zainab”? “to ba gwara ayi mata auren ba. Ita ba karatu take yi ba balle ace wani abu take jira. Yanzu fa idan zaki tuna shekararta ashirin”. Ya amsa mata. “Eh ni ban ce kar ayi mata aure ba. Amma ina fatan ba wan nan mai tallan gwanjon zaka dauki santaleliyar yarinya kamar Zainab kabashi ba. Ai an san arziki na