Sashe 5
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 2 min read
ita da mijinta. Bayan shawarar da zuciyarta ta yanke mata ta dora da nafila domin neman sa'a a wajen Ubangiji. Washe gare ta nemi izninsa domin zuwa gida. Da mahaifanta ta tattauna abin da ta ke son yi. Take kuwa suka goya mata baya. Ta dawo kuwa baifi da awa uku ba sai ga mahaifinta yayi sallama da kudi har dubu dari uku da saba'in. Kun san mutan kauye ba kamar na birni ba da bamu da abin saya sai kaya da dinki. Su kuwa baka raba su da dan tari. To haka itama Khadija. Garkenta na manyan shanu biyar bajimai da kuma sanuwa uku da 'yan marakai bakwai ta sa babanta ya kai kasuwa. Kuma a wan nan lokacin kudin da aka sayar da su makudai ne saboda darajar kudin. Mallam Usman bai san da duk wan nan shiri nata ba sai bayan da daddare yara duk sun yi barci san nan ta fito da kudin nan ta tura gabansa. Cike da mamaki yace "wan nan fa "? "Na yi tunani ne shine naga idan mutum yana tare da azzalumai gwanda ya fita harkarsu kawai. Saboda haka batun ni in kawo kwali na a bani aiki bai taso ba. Aikin gwamnati mu barwa masu takama da gwamnatin mu kuma mu kama Allah mu dogara da kanmu". "Anya Khadi ba za ki bar zan cen nan ba. Kowa ma ai da Allah ya dogara". "Na dai ji mu bar wan nan zancen mu koma kan wanda ya dame mu. Noma da kiwo zamu koma. Baffa yace in gaya maka ya baka fadamarsa ta kauyen gurjiya ka kuma san shinkafa ake a wajen. Saboda haka tun da Allah ya hore maka ilmin noman zamani sai ka yi amfanin da ilmin da Allah ya baka ka habaka noman ka. Ni kuma bayan gidan awaki zan zuba. Baffa yace zai hada mu da wadanda suke saye zuwa kudu. Zan kuma ci gaba da saka ta yadda na saba saboda kunji kunjin tsakar gida. Amma aikin daga ni har kai ba mai yinsa". Shi ma kuwa yayi na'am da wan nan shawara ta ta. Haka suka tsara rayuwarsu suka dukufa noma da kiwo da kuma 'yan sana'oin da za su rufa musu asiri. Kuma Alhamdu Lillah asirin nasu ya rufu.