Sashe 26
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma dan wani aminin Alhajin ne zai aureta. [8/8, 21:55] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 25BY HANNE ADO ABDULLAHI Zainab bata da masaniyar abin dake faruwa, saboda tana gidan su Fatu suna aikin snacks din da zasu yi sauka gobe. Tabbas Bala ya sanar da ita ko yau da safen nan akan cewa iyayensa zasu shigo washegari da yamma. Da kanta taje tana kokarin sanar da momi. A dakinta, ta same ta ce “Mh Momi dama Ya Bala ne yace…..” Bata barta ta karasa ba ta fara sauke mata bala’i. “ya Bala a gidan uban wa. Ke har kin isa ki aurar da kanki banyi niyyar kiyi aure ba. Shashashar banza marar hankali. Ta shi ki bani wuri ko in yi ball dake”. Hakanan ta mike tana mai zubar da hawayen takaici. Ta rasa me zata yi a duniyar nan Momi ta sota. Laddabi biyayya da kuma hidimar da take mata, ‘ya’yan da ta haifa a cikinta basa yi mata 2% dinta. Amma duk da haka ita ce a hantare ko da yaushe. Ita dai bata samu sanar da iyayenta zuwan iyayen Bala ba. Ta dai fawwala wa Allah lamuranta ta kuma yarda idan har mijinta ne shi ba wanda ya isa ya raba su. Shi ma dai Mallm Usman haka suka yi kundunbala su da kakannin Zaina na wajen uwa da kuma na uba. Da kuma kannen kakanin nata guda biyu. Shi ya tuko so zuwa gidan Dr Abdullahi, saboda information din da su Mujib suka bashi akan zuwan iyayensu yau. Su kuma daga bangaren iyayen Al Bashir sun shirya ke nan saiga gwamna jiha ya iso saboda halartar daurin auren da za ayi, wanda ya hada dangi da duk wasu abokan arziki. Shi ma Al Bashir kusan duk abokansa sun zo daurin auren cousin dinsa saboda angon abokinsu ne. Jiniyar gwamna ita ta tsaida su daga shiga mota domin zuwa wajen iyayen Zainab. Bayan sun gaisa suke shaida masa inda suke da niyyar zuwa, amma tun da yazo zasu fasa zuwa, su tsaya a daura auren da dama shi ya tara su. Allah ya sani His Excellency yana ganin mutuncin Alhaji Usman, watau shi mahaifin Al Bashir, saboda su suka tsaya masa ya hau kujerar da yake kai saboda sun ganshi a matsayin mutum mai gaskiya. Tashin farko ma da zai fara campaing. Naira million 500 ya bashi gudummowa. Kuma da aka ci zabe ya nuna san ya saka masa da alkhairin ya ki yarda, saboda ko kwangila yaki karab. Ya nuna masa saboda talakawa suka yi kuma talaka suke so ya ci moriyar dashin da suka zuba. Ai kuwa His Excellency najin auren Al Bashir za a je nema, yace da shi za aje. Nan kuwa suka runguda zuwa Hotoro NNDC inda gidan su Zainab yake. Dr bashi da masaniyar kommai sai gani yayi security sun zagaye gidansa. Kafin chief protocol officer ya gama yi masa bayani, baki sun iso. Bayan an gaggisa suka sanar da Dr Abdullahi uzirin da ya kawo su. Ka hango ta yadda zai yiwa governer musu yana matsayin COMMISIONER dinsa? Cike da murna ya karbi abin. Nan kuwa suka FITO da sadakin da aka yankawa dansu suka mika. Saboda tsabar rashin gata bai damu da ya tambayi Zainab ko ta na son sa ba ko bata so. Tun da ai yana sane da cewar Bala mai gwanjo ke neman aurenta ba Albashir Usman Ahmad Babba ba. Su dai su Baffa dasuka zo daga Kera sai mamakin wan an abu suke. Shi kuwa Mallam Usman bai yi mamki ba saboda ya san matsayin Al Bashir. Ana kokarin tashi sai Baffan Nene yace “to ni kam ranki shi dade da ayi aje a dawo, ga sadaki ga waliyyan ango gana amarya ga kuma liman na unguwar nan, a daura aure mana kawai shi ke nan”. “haka ne kuwa” da yawa daga falon suka amsa. Jin haka Alhaji Bashir kawun Al Bashir ya dau waya, ya bugawa babban dansa yace maza a yi diverting jama’ar da suka taru domin daurin auren ‘yarsa da kuma dan abokinsu shi da Alhaji Usman zuwa gidan su Zainab, ga wani daurin auren na gagawa ya taso. Kafin minti talatin kuwa muatane sun cika kofar gidan. Ba shiri mallam ya bude store da aka jibge tabarmi wadanda aka saya lokacin auren su sakina ya shiga baza su a haraba da kuma wajen gidan. Momi na daga cikin gida saboda kasancewar wannan jumma’ar ta kama public holiday ba su je aiki ba. Kafin ta Ankara kawai sai gani ta yi mutane na ta tududdowa cikin gidan. Baba laure ce, ke shaida mata ai wadanda suka kawo sadakin Zainab ne suka bukaci a daura aure yau din nan. Ta lailayo wata ashar da bazan iya rubuta muku ita ba, tace “uban waye mijin, saboda da dai na san ba wan nan dan iskan mai gwanjon bane’. Baba Laure dake mata dariya kasa kasa tace “na dai ji kamar ana ko dan gidan gwamna garin nan, don shi ma ya zo na dauka ma kin ji jiniyarsa”. “naji jiniya amma ban dauka nan gidan bane, na dauka wucewa su kayi”. “ai kuwa dai nan suka tsaya”. Kwasa tayi a guje ta shiga ciki, kamar tababbabiya. Ta buga wayar mijin hayaniyar falon nasa bata barshi yji ba. Jikinta gabadaya sai rawa yake yi. Ta ce "Yi sauri Hanif falon Daddy ku ka kira min shi kace masa na fadi bani da lafiya”. Da sauri kuwa ya nufi falon dadin nasu ya isar da sakon Momi ga Dr Abdullahi. Jin haka kuwa ya mike da hanzari yana fadin “ina zuwa wani abu ya faru a cikin gida”. Da sauri Baffan Nene ya riko shi yana fadin “kaga kar ka shiga ciki ko uziri maitsawo ne wakilta wani kawai ya dauran auren ai kaga ba a bar su mai girma .Gwmana suna jiraba”? Nan takewa kuwa ya wakilta mahaifin sa a kan ya daura auren Zainba, shi kuma ya shiga yaji uzurin da ya faru a ciki. Yanda ya ganta shi kansa hankalinsa ya tashi sai sambatu take tana fadin an munafunceta. “Kayi sauri ka tsaida auren nan. Ba zai yiwu ba”. Sune kalaman da ke fita daga bakinta. Kokari yake ya fahimci abin da yake nufi, amam duk ta rude sai Magana daya take maimaitawa. Kafin su Ankara sai jin sanarwa suka yi an daura auren Zainab Abdullahi Zubairu da kuma Alhaji AlBashir Usman akan sadakin naira dubu dari biyar, wanda Baffa Nene ya wakilci amarya His excellency ya zama wakilin ango. Da Momi da Zainab tare suka shide wacce itama sanarwar ta same ta ta sanadin wan Fatu da aka daura auren tare da shi.shi kansa Al Bashir bai zaci durin auren a haka ba, a bazata yazo masa. Zainab na jin an daura aurenta ba da Balrabe ba, ta kalli yayan Fatu watau Ya Baanaa cikin firgici da kuma tsoro. Tace “Ya Baana me kake nufi? Da wa aka daura aure na? na shiga uku”. Tana fadar haka tayi luu ta sume a wajen. Shi ma daga can kofar gida jin sanarwar daurin aurensa ya san yi shi luu din kamar zai fadi. Su mujib suka taro shi suna tsoknar sa. Allah ya taimake shi da zai je daurin aure babbar riga ya saka, ba don haka ba, da hoton daurin aurensa ya fito da karamar riga. Suna cikin farin ciki shi da abokan sa wadan da ba nashi dauri auren suka zo ba, na Sagir Inuwa suka zo wanda ya kasance shi ma abokinsu ne sai ga Ya Baana ya nufo su da sauri daga cikin gida yana neman taimako wai Zainab ta suma. A miliyan ya zumbuda yafada gidan su Fatu wanda yake bayan na su Zainab. A tsakar gida ya tarar da ita rungume jikin mama Haajjo tana kokarin shafa mata ruwa. Bai san sanda ya durkusa ya kamota jikin sa ya rungume ba, sai fadi yake “kar kiyi min haka Zainab. Don Allah ki tashi idan kika barni bansan yadda rayuwata zata kasance ba” Da kaga yanayin da yake Magana ka san a rude yake. Tana farkowa kuwa ta ganta manne a kirjinsa yana kuka. Ita ma ba shiri ta saki kuka tana fadin “wayyo Ya Balarabe Momi tayi nasarar raba mu. Na shiga uku dawa aka daura min aure da shi. Wallahi ban sonsa kai nake so. Jin kalamanta ya sanya shi dada rungumota jikinsa ya ma mata da wasu mutane a tsakar gidan. Mama Hajjo ce tasa Fatu ta shiga dasu dakin Ya Baana saboda idon mutane. Bai ji kunyar kowa ba haka ya daga ta cak ya shiga da ita dakin. Kan katifar dakin ya kwantar da ita, san nan ya tura kananan kitson da suka zubo har gadon bayanta wanda suka barbazu a fuskaarta lokacin da aka yaye mata hijabin da ke jikinta lokacin data suma. Tana kallonsa sai ta sake fashewa da wani sabon kukan. Ya sake rungomata jikinsa kanta na karkashin habarsa fadi yake “come on Putri is alright. Ki yi shiru ki daina kukan I will explain things to you”. “Ya Balarabe ba abin da za kayi min explaining. Ka barni kawai in karashe rayuwata cikin bakin nciki”. “in sha Allahu cikin Farin ciki mai tsawo da alkhairi da kuma yakana zaki kare raywarki”? “Ta ina? Kaine farin cikina, na kuma rasaka saboda haka bani da wani sauran farin ciki”. Ta sake fashewa da wani sabon kukan. A cikinn hannuwan sa ya saka fuskarta. San na yace “Putri look at me”. Ta dago ta kalle shi kamar yau ta fara ganinsa. “kin taba tambayata suna na na asali”? Gigiza kai tayi alamar a’a. “Putri nine Al Bashir da ni aka daura miki aure. Nine mijinki nine zan kasance farin cikin ki”. Take taji wata irin kunya ta kamata. Nan ta ringa tariyo boren da ta yi saboda a zaton ta ba shi ta aura ba. Hannu ta sanya ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Sake rungomata jikinsa yayi yana fadin “a’a kar muyi haka dake kunya kuma ta ina. Yanzu ki ka gama suma kina farfadowa akan ba abaki ni ba. Yanzu kuma kin samu sai kuma ki fara yiwa abin da kike so damage”. “Ta ina nayi maka damage”? Yana kokarin bata amsa