Sashe 8
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
da zaki yi"? Tana zaginta tana duka a lokaci daya. Farisa da Khalil kuwa sai dariya suke. Sai da tayi mata lilis san nan ta tsallake ta ta barta a wajen. Khalili ya kalle ta ya mata gwalo yana cewa "gobe ma ki kara tabani sai na sa Momi ta yi miki duka banza boyi boyin gidanmu". Tun daga wan nan lokaci ta dada janye jikinta daga garesu. Saboda kome suke so idan taki yi musu yanzu zaka ji suna fadin "ko yi ta girma da arziki ko yanzu musa kuka . Kin kuma san idan mun digar da hawaye digo daya ko na karya ne sai kin zubar da cikin jug na gaske". Sai ya zamana bata da wani da take mu'amala daxshi a cikin gidan idan ba baba Laure ba. Ita ma din kuma Mallam mai gadin su ne ya dora mata nauyin kula da Zainab. Saboda ya lura da taken taken matar gidan so take ta watsa rayuwar yarinyar nan gaba daya. Ba abin da ya dameta da tarbiyarta. Za ta iya aikenta shago siyo abu komai dare ba abin da ya dameta. Kasuwa kuwa ko wacce iri ce turata takeyi kuma da kashedin lalle ta samo araha. Mallam sai ya fassara hakan da taken taken lalata rayuwarta. Shi ma kuma sai ya dauki aniyar tsaya wa a kan lamuranta. Shi ya hana ta fita da daddare. Idan an aiketa ya ja mata kunne kar ya kara ganinta taje shago shi ta ba shi ya sayo mata. Lokuta da dama kuma da uwar take tura ta kasuwa sai ya tabbatar da matarsa suka tafi. Balle da suka yi sa'a ba yini suke a gida ba. Haka zalika ya dorawa matarsa larurar kula da tarbiyyar yarinyar tare da nusar da ita harkokin da suka danganci tarbiyarta. First period dinta ita ta nuna mata yadda zata kula da kanta. A wata rana mallam yazo wucewa sai ya ganta ta kawowa direban gidan abinci. Shi kuma ya rike hannu ta yana mata wasa. Yana cewa "zo nan matata. Zo ki bani a baki in koya miki wasan masoya. Kin san Momi ta ce ni zaki aura". Dama kullum haka Momin take gaya mata cewar tun da ta ki karatu sai dai ta auri Sale direban gidan. Kuma inda zaka san da gaske take. Ita ta dora mata dokar duk sanda ta gama abinci ta kai masa dakinsa. A wan nan ranar da Mallam yaji kalamansa ba karamin tashin hankali ya shiga ba. Da fushinsa ya karasa wajensa yace "sakar mata hannu karamin shakiyyi". Ba shiri ya saki hannunta cikin tsoro. Ko ba komai yana shayin mallam mai gadi saboda yana kallon mai gidan ma ko bukatarsa ta tashi a wajen aiki wajen Mallam yake zuwa ya taimaka masa da addu'a. Gashi kullum ka ganshi da Qur'ani a hannunsa yana karatu ko kuma wani littafin addini. Hakan yasa yake masa kwarjini. Mallam ya juya ya kalleta ya daka mata tsawa yace "me ya kawoki dakinsa"? Cikin tsoro da rawar murya tace "momi ce tace in kawo masa abinci". Ya dan sassauta muryarsa cikin tausayin yarinyar yace "daga yau ki dinga ajiye masa a bakin baranda kar ki sake zuwa dakinsa". "ToMallam "ta fada da saurinta. San nan ta juya ta wuce cikin gida. Sai da yaga ta shige san nan ya juya wajen Sale yace "kai kuma naga take taken ka. Ta ka saurareni da kyau. Na rantse da girman Ubangiji idan ka kara taba yarinyar nan ni kuma na maka alkawarin kai da mace a duniya har abada. Network naka zan dauke gaba daya. Idan kana ganin karya nake ka gwada ka gani". Kwarai Sale ya tsorata da barazanar Mallam. Saboda haka ya kashe wan nan boss din. Ita kuma Baba Laure ta shiga nusar da ita duk abin da ya kamata diya mace ta sani a rayuwarta. Allah ya basu hahihuwar yara biyu duk maza. Basu samu mace ba, sai suka mai da ita kamar 'yarsu. Ita ma kuma haka ta mai da su makwafin da iyayen da Momi ta hanata ba don Allah ya raba ta da su ba. Kawarta daya a islamiyya Fatima. A nan bayan layinsu take. Su ba masu sukuni bane domin babanta masinja ne a kotu yayin da babarta take awara. Amma ita take taimaka mata. Ita take bata abincin break. Ba tare data sanar da ita komai ba ta fahimci halin kuncin da ta ke ciki a gidansu. Ba ta cika zuwan gidan ba sai ta tabbatar momi da ahalinta ba sa nan. A haka rayuwarta ta ci gaba har suka fara zama 'yanmata ita da sauran kannenta. [8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧IN FIKI A MIJI💑 Page 9 BY HANNE ADO ABDULLAHI A haka Zainab ta dinga cukurkudar rayuwarta. Ta koma baiwa a gidan ubanta. Ta samawa kanta lafiya ta zama mai hakurin dole. Idan an sakata tayi. Idan ance tayi laifi ta bada hakuri komai gaskiyarta. Tayi developing wani robotic attitude a rayuwarta. Bata da ra'ayi sai na 'yan gidan. Abin da duk suke so haka take biye musu. Amma duk da haka bata tsira daga masifa da kuma kyarar Momi ba. Abin da bata sani ba Momi hassada take yi da baiwar kyau da Allah yayi mata. A yanzu ne ma ta daina aske mata gashin ta. Da bini bini zata dauki almakashi ta mai da mata shi saisaye a sunan wai taga kwarkwata aciki. Amma gashin nan da yake ba shi da zuciya bashi sati uku zuwa hudu zaka sake ganinsa kwance lamban a gadon bayanta. Gashi baki mailaushi gaske. A haka kuma ba gyara ya ke samu ba. Da kyar take iya shafa masa vaseline sau daya a wata. Shima Baba Laure ce ta sanya mata dokar duk sanda zata yi wankan tsarkin al'ada ta tabbatar ta tsefe shi ta wanke da sabulu. Suna fara zama 'yanmata kuwa surar jikinta ta nuna mai kyawu ce lamba daya. Fuskarta kuwa dama tun da ta taso kasan kyakkyawa ce. Ba abin da ya rabata da mahaifiyarta har hasken fatarsu iri daya ne. Wan nan kyau nata shi ke dada bata ran momi. Kar kuma ku dauka nata basu da kyan. Suma kyawawa ne bama ya Farisa da ta ke fara kal. Ita ma kuma Farida kamarsu daya sai dai haskenta bai karasa na Farisa ba. Zasuyi kala daya da Zainab. Sai dai ita kuma jikinta ne ba mai kyau ba saboda she is busty. Amma zamani na gayu. Da yake kuma ta iya parking din su da kyau sai suka zama abin sha'awa. Ita kuwa borar 'ya'ya ba ma wanda yake tunawa da saya mata undies. Jikin ne Allah ya sanya ya zama mai tsayawa da kansa. Sam bata bukatar sanya bra. Skirt ne da pant idan sun bata ta zubar ta zabi masu dan dama dama. Shi ma idan Farisa taso wulakanci tayi kararta wajen Momi akan ta satar mata undies. Hakan kuma ba zai sa Momin tayi tunanin sai mata ba sai da ta ci dan banzan duka Farisa kuma ta yi ta dariyar jin dadi. Tana da shekara sha bakwai Farida na sha shida Farisa kuma bata karasa sha biyar ba suka yi kandi. Anti sakina da anti Bilki kuwa kannen Momi lokacin suna BUK 300 level. A lokacin ne kuma suka tsayar da samarin da suke so. Anti Bilki ta samu Sulaiman mai aiki da wani attajiri da ke da kamfanin yin atamfofi a China. Yayin da Anti Sakina ta hadu da Kabir. Shi kuma ma'aikaci ne a DPR. Tun da kuwa suka samu samarin da suke so sai dawainiya ta karar wa Zainabu. Ga shi yanzu sun shiga ajin sauka a islamiyya. Saboda haka basa tasowa sai uku da rabi. Kuma ya zama dole bayan ta girka abincin dare ta bata lokacin wajen yi wa samarin aunties dinta better na musamman. Ta gyara falon baki inda suke zama. Bayan nan ta kashe lokaci wajen yi musu kwalliya da daurin dan kwali. Haduwarta da Fatima ya sanya ta koyi abubuwan gayu kamar su make up dauri da kums lalle. Har da gyaran jiki. Da wajen babar Fatiman suke zuwa lalle da gyaran jiki. Dan raka sun da take yi sai itama ta koya. Shi ke nan kuwa suka daina zuwa ko'ina. Ita ke musu komai. Amma fa ita bata da lokacin yiwa kanta. Hatta gyaran farce ita take zama tayi musu. Mahaifinta dai duk yadda Momi zata yi ta sa shi yaga bakin ta ta iya. Idan har yana gida zata saka Farida ko Farisa wani a cikinsu ya hada masa abincinsa a dining. Wacce ta girka daban amma mai serving ita ake nunawa uban ita ta girka. A hankali sai da ta sa yayi mata shaidar hatta aikin gida kiwa take masa. Bari Momi take bayan ta saka ta ta gyara dakinsa da su bandaki ta wanke. Sai an daidaici ya kusa shigowa sai a tura 'yan gata da turaren wuta su saka masa. Za kuma a tabbatar ya gansu saboda ya yarda su suke hidimarsa. Yayi ta jin dadi yana sa musu slbarka. Ita kuwa tsakaninsu sai dai zagi da fada. Kuma ko waye zai ji haushinta. Ke ba karatu ba kuma ke ba aikin gida ba ai dole uba yaji haushi. Baba Laure da Mallam sai kuma Mama Hajjo watau mahaifiyar Kawarta Fatima su ka dai ne a tsaye a lamarinta. Ko pad idan wani a cikinsu bai sayamata ba to kuwa sai dai tayi amfani da tsumma. Ana haka auren Sakina Da Bilki ya tashi. Daddy shi yayi musu komai na 'yan gata. Zainab ta samu an dinka ankon bikin da ita. Kwatsam sai ga kawar Farisa ta zo daga Lagos ziyarar gidan uncle dinta. Nan kuwa Momi ta karbe ankon Zainab aka bawa bakuwar Farisa. Kaf snacks din da aka ci a bikin nan da kuma wanda aka kaiwa amare gidansu ita tayi shi. Duk da bata da anko. Ranar dinner ta ci kwalliyarta da less din da Farida ta bata. A keken Mama Hajjo ta gyara rigar da skirt din suka dawo size dinta. Saboda tsabar karbar kunce kamar sai da takoyi gyara a dole. Ko ita Fatiman da keken dinkin ke gidansu bata iya dinki kamar Zainab ba. Ga dai babarta Mama Hajjo mai ciniki goma