Sashe 34
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
[8/9, 13:58] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 30 BY HANNE ADO ABDULLAHI A motar ta Rav 4 yayin wan nan lokacin kalar maroon mai ruwan hanta, direbanta mai suna mallam Yunusa yana tukata, ta doshi gidan su. Horn ya danna, mallam ya leko ta ‘yar tagar da ke manne da dakinsa. Tayi saurin sauke gilashin gefenta, tace “mallam Barka da yamma” . Da murna ya wangale kofar gate din. Kusan tare da motar suka nufi wajen da za ta tsaya. Da kansa ya bude kofar bangarenta, yana fadin “barka da zuwa uwata. Yau ke ce a gidan nan”? “nice mallam”. San nan ta rusuna yadda ta saba gaishe shi. Bayan sun gaisa take tambayarsa baba Laure. “Ai Laure tana gida. Kin san bayan aurenki da sati guda Alhaji ya aiko wani mutum da sako, gida ne sukutum ya saya mana shi a nan unguwar badawa, baki ganshi ba kato da shi”. Cike da murna tace “kai amma madalla, an gode ni bai ma sanar da ni ba”. Nan dai suna ta dan tattaunawa, hango Halim da ta yi shi ya katse tattaunawar tasu. Da gudu yaron ya karaso ya rungumeta. Ko ba komai akwai shakuwa a tsakaninsu. Dukkan su su biyu suna kaunarta kwarai da gaske ko don wahalar kuruciya da ta sha dasu. Hannunsa rike a cikin nata ya jata suka shiga gidan. Ita kuwa hankalinta yafi karkarta kan yanayin da ta ga gidan. Sam ba haka ta tafi ta bar shi ba. Da gani kulawar da ya saba samu tayi karanci kwarai da gaske.. Harabar dai a share take ba laifi ko don dama Mallam ne ke gyara ta. Amma fa tun da suka fara shiga cikin gidan ranta ya baci matuka. Kai kace gidan ya dau shekara bai ga shara da mopin ba. A kofar baya kuwa tarin wanke wanke ta tarar da wata ‘yar mitisitisyar yarinya ta tasa su a gaba tana kuka.Ta kalli kayan tsibi guda ga kuma yarinyar duk ba ta fi shekara tara ba. Kayan nan kuwa sun fi kama da an ci abincin biki an waste. Shi kuwa bai kula da yanayin ta ba sai kaudi yake zuba mata yana bata labarin makaranta. A hanyar shiga falon suka yi kicibis da Hakim. Shima kamar dan uwanta haka ya rungumeta a haka suka shiga wajen Momi. Duk sun dafe mata kamar zasu ka da ita. Fadi suke “Momi ga Ya Zainab ta zo”. “kai da Allah can ka cika mana kunne da surutu sai kace wanda yaga bako daga gidan aljanna”. Tana daga ido taga ashe anti Sakina ce mai wan nan bala’in. a haka dai ta durkusa kusa da Momi cike da ladabi tace “momi barka da war haka”? A wulakance ta dago ta kalleta. Take kuma tsadaddar after dress din dake sake a jikinta ta tsone mata ido. Da gani kasan ba zata kasa dubu hamsin ba. Ga kuma awarwaro gwal guda hudu ma su dan karan kyau sanye a hannunta. Da ta dago kuwa wani daddadan kamshiun turaren ne ya daki hancinta wanda tassan tabbas bakuwar da ta shigo ita ta zo da tsarabarsa. A wulakance ta ce “sai yau ki ka ga damar zuwa ki gai da mutane? Ki dai yi a hankali shi gidan miji ba matabbata bace. Idan ta kubuce gidan dai da ake gudu nan za adawo”. Murmushi tayi saboda a yanzu kaunar da Al Bashir ke nuna mata ta bata wani irn confidence da ya sanya bata jin shakkar kowa da kuma komai a rayuwarta. “Momi kiyi hakuri ba na nan ne sai jiya na dawo”. “marar kunya ai ba sai kin sanar dani kinje yawon shakatawa da miji ba. Idan ba kya nan ko waya ba za ki iya yi ba”. “Momi kiyi hakuri a gida na bar wayata ban tafi da ita ba. Kuma ban rike number kowa ba a kaina. Shi yasa”. “ke dai kika sani.in dai auren zamani ne kiyi mu gani. Wadanda suka mutunta iyayensu ma, suka rabu dasu lafiya yaya suka kare, balle ke mai auren yaudara”. Ba ta bata amsa ba ta mai da hanakalinta wajen Anti sakina tace “Anti sakina barka da yamma”. Sai da ta maimaita sau biyu san nan ta yi firgigit daga kallon leshin da ya bullo ta gefen rigar zainab wanda ita bama ta san ya bullo din ba. Ba kunya kuwa ta kai hannunta ta taba domin ta tabbatar da original din ne ko kuwa barawon sane. Amma laushinsa ya sa ta gane dan dubu dari da hamsin din ne. Bata amsa mata gaisuwa ba sai ta bita da cewar, “saboda zaki zo gida yau kika yi wan nan kuren adakan saboda ki zo ki birge mu. Ta baki burge din ba”. Ta yi tsaki ta sake cewa “aikin banza ga riga ba mutum. Kayan ma sam basu hau jikin ki ba saboda rashin sabo. Sabon shiga arziki”. Har ranta ya dan so ya baci, amma da ta tuna sanda ta san kayan yadda meena ta dinga koda kyan da su kayi a jikinta, sai taji komai ya yaye. Shi kuwa uban gayyar sai da ya sata ta yi posing ya dau hotonta saboda tsabar kyawun da ta yi. Da kuma ta sake tuna kalaman umman AlBashir da tan kace matar dan uwana mai kyau da kyawun hali. Saboda duk jin kunya na Zainab, matar nan taki surukanta da ita. Jan ta ta ke yi a jiki kamar yadda zata ja sauran ‘ya’yanta a jiki. Muryar Dadi ce, ta katse mata tunanin da ta ke da tsaka da yi, wanda ya tarbe ta da murna yana fadin “a’a yau Zainab ce a gidan”? Da sauri ta mike ta nufi inda yake a tsaye, ta durkusa dai dai kafafunsa tace “Dadi barka da war haka”. “Barka kadai Zainabu” ya amsa mata cike da sakin fuska, wan da ba ta jin ta taba ganinsa ya yi mata Magana cikin fara’a irin ta yau. Amma idan bata manta ba babu wata mua’amla da ke hada su illa a kai karararta ya kira yayi mata fada. Amma yau irin fara’ar da ya tarbe ta da ita ta faranta mata nata ran matuka. Kujera ya samu ya zauna kusa da inda take tsugunne a gefensa. “yaushe kuka dawo ne”? “Jiya Dadi”? “Kai madalla. Allah yasa an samo hajj mabaruk”. “Amin Dadi. Na shiga wajen Anti Bilki ta na gai she ku da kyau”. “kai madalla muna amsawa”. Dai dai nan Momi ta kasa daurewa ta mike tare da buga wani uban tsaki ta yi shigewarta daki. Allah sarki Zainab, bata san dadi ya iya hira ba sai wan nan ranar. Shi yake mata tambayoyi tana bashi amsa yana kuma hadawa da comment. Zan cen nasu duk ya danganci wuraren da ta ziyarta. Inda kuma shi yayi ta encouraging dinta tana bashi labari. Ko ba a gaya maka zaka fahimce cewar yayi matukar farin cikin da yanayin ‘yar tasa. Sun kai kusan awa dawa suna hira, san nan shi da kansa yace “tashi ki koma gida kin san ba a son magariba ta ringa samun mutum musamman mace a waje”. Da kansa ya shiga dakinsa yayi dubi dubi ya rasa mai zai bata, sai kawai yasa hannu a aljihunsa ya damko kudi wanda bai san yawansu ba ya mika mata yace “ungo karbi ki sayi wani abu ki shiga gidan naku da shi”. Saboda murna ba ta san sanda hawayen dadi ya zubo mata ba. Wai ita Zainab Dadi yake mikawa kudi da hannunsa ba tare da ta tambaya ba. Ta sa hannun biyu ta karba cike da murna. Halim da hanif da suka raka ta mota su ta bawa tsarabar akwati biyu suka shigo da ita gidan. Bata bawa Mallam tsaraba ba sai dai ta tambayi kwatancen gidansa ya yi mata. Mallam Yunusa ya ce ya gane wajen. Nan suka rabu da alkawarin za ta kai musu ziyara. Daga nan kuwa bata yi birki a ko ina ba sai gidan aminiyarta watau Fatu. An sha murna da tsalle na jin dadi. Mama Hajjo sai dariya take yi musu. Da kyar ta samu ta sake ta suka gaisa da maman. A nan taci tuwon dare saboda magariba a nan ta same ta. Ita kanta sai kallon mamaki take binta da shi na ganin yadda ta canza ‘yan kwanakin kadan da basu hadu ba. Ba ta boye musu ba ta nuna damuwa da yadda taga gidansu duka ya kazance. Mama Hajjo da Fatu suka kalli juna suka tuntsire da dariya. Maman tace “ya kuwa ba zaki ga gida ya koma haka ba. Injin shara da wanke wanke da kuma goge bata nan. Ai watan tonon asirin Momin ku ya kama. A dan wata biyu nan tayi masu aiki sun kai ashirin. An dakko nufawa, an dau kabilun kaduna, ke har an dawo ana daukar na madobi. Kowa yazo ya zauna kwana biyu sai su gudu akan ba za su iya ba. Me kawo mata ‘yan aiki ta ce ta gaji da debo ;’ya’yan mutane tana kawowa ana wulakanta su. Ita Sakina ai Allah ne ya cece ta. Wata gansamemeiyar banufiya ta tashi yiwa rashin mutuncin data saba. Tana marinta, ita kuwa ta kai mata naushi. Allah ya taimaka ba ta samu idonta ba. Sai da tayi sati kusan biyu tana jinyar raunin da tayi mata”. Da mamaki tace “amma ita da take zuwa lokaci lokaci me zai hada ta fada da masu aiki, duk da dai nasan tana zuwa sosai”. Fatu ce tace “au baki da labari. Wan nan sokon mijin nata ta kama da mai aikinta a dakinta. Ta kama yarinyar da duka, ta turo ta waje tsirara, shi kuwa ya fizge zaninta ya lullube mai aikin da shi. Ya kuma rattaba mata saki uku a lokaci daya. Sai a makota aka bata aron zani ta daura. Tana isowa gida ya biyota da yaranta ya tattara ya nemi transfer ya bar garin”. Cike da mamamki tace “ba sai ta kaiwa ‘yan uwansa yaran ba”? “ta ina zata kai su bayan ba saninsu tayi ba. Sai da wan nan abun ya faru ashe ba su yi bincike a kan asalinsa ba. Suna gani dan canji a tare da shi suka bashi ‘ya. Waliyyin ma ashe limamin masallacin ofis din su ne.