Sashe 4
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
isa ka taba jarumi irin sa. Ka tambaya a kauyen nan kowa ya san irin jarumtarsa." Ita dai Innar su Khadija sai faman jan ta take tana bata hakuri yayin da shi kuma ya juya yafice daga cikin gidan cike da takaicin abin da mahaifiyarsa tayi masa. Kuma har sai da ya kai kofar gida bai daina jin zafafan kalaman da ta raka shi da su ba. Fadi take "yarinyace ka gaji ka sakota. Kace ba ka so. Wani kuma ya aura. Ka tsaya kanawa mutanen bakin hali. Ai duk wan nan zafin da ka daukan na san na takaicin rashin Khadijan ne". Ita kanta Khadija da Mallam Usman sai da suka dawo suna bata hakuri saboda ganin yadda ta dauki zafi. Ta kalli Malam Usman tace "kaga ai gaisuwa kazo min. Koma kofar gida ka zauna ka ci gaba da amsar gaisuwa idan yayi wani yunkuri ka daka min shi a wajen. Ke kuma shiga ki ci gaba da aikin abincin da kuke yi. Ban kuma yarda ki tafi ba sai sanda kuka saba tafiya idan kunzo". Innar Khadija tace "don Allah ki yi hakuri ki bar zancen nan haka. Da wanne zamu ji da rasuwa ko kuma da shirmen yara"? "Shi da ya dago fitinar ai bai tuna kanwarsa ce ta jini ta rasu ba. Tun da shi duk abin da matarsa ta dora shi a kai hawa yake ya zauna daram". Ai kuwa takaicin abin da aka yi masa shi a Kera tsaf akan Zainab ya sauke shi. Ita bata da masaniya ma na abin da yafaru. Yana cikin mayarwa da Rumaisa irin wulakanci da Khadija ta jawo aka yi masa ita kuwa ta shigo da saurinta tana fadin "Abba kaga da muka je Kera Abba Mallam ya ban....." Ba ta kai karshen zancenta ba ya kuwa yi mata dukan da Mercy da Ronaldo sukewa Ball. Yarinyar nan sai da ta dangana da bango ta tsaya. Duk da haka bai hakura ba dukanta ya shiga yi kamar Allah ya aiko shi. Sai da Mummy ta tabbatar ta daku san nan ta tashi ta rike shi tana ba shi hakuri. [8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👨👧IN FIKI A MIJI 💑 PAGE 4 BY HANNE ADO ABDULLAHI Kwanan Zainab uku tana jinyar dukan da mahaifinta yayi mata. Wanda ba komai ne ya hassala shi yayi mata dukan kawo wuka irin haka ba, sai kyawun da ya ga Khadija tayi. Ta yi shar da ita kamar ba matar kauye ba. Shi ko zaman su da ita a kasar waje bai ga tayi wan nan kyan da kuma kuruciyaba. Tafi masa kama da budurwa 'yar shekara ashirin ba uku zuwa da hudu amma ba wai matar malamin makaranta kuma uwar 'ya'ya biyar ba. Ya dade kwarai bai hadu da ita ba. A tsammani sa tun da talaka take aure zai ganta yarkace yarkace. Amma sai ya ganta tsaf da ita. Ga kuma kalaman mahaifiyarsa da ta dinga fadin "mata ce an bashi yace baya so ya sako ta. Wani kuma ya aura shi ne zai zo yana nuna wa mutanen bakin hali". Ba karamin tunzura yayi da kalaman mahaifiyar ta sa ba. Yadda ta kwana uku tana jinyar jiki, haka ya debi wannan lokaci yana jinyar zuciyarsa. A wan nan ma dare sambatunsa ne ya tayar da momi ta jiyoshi yana fadin "sai na wulakanta Khadija. Ita har ta kai matsayin da zan fadi magana ta mayar min da martani". Momi ta kamo shi ta zaunar da shi a bakin gadon dakin. San nan ta nufi fridge ta debo masa ruwa a kofi ta bashi ya sha. Sai da ta ga ya dan natsu san nan ta tambaye shi abin da ke damunsa. Take kuwa ya gaya mata niyyarsa ta daukar fansa akan tshuwar matarsa. Dariyar jin dadi tayi saboda itama tana da burin ta tsawwalawa wa rayuwar Khadija. Saboda a nata tunanin son da dangin Daddy su Farida suke mata ne ya hana ita din su sota a matsayin ta na matar mai kudin dangin. Ta ki fahimtar cewar su wadan nan fulani da ta ke gani bamasu zalama bane. Kudin ta dana mijinta ba zai sa su dauki raini da wulakancin ta da kuma na 'ya'yanta ba. Hakan ne ya sa suka ja baya da ita. Ita ma kuwa tayi niyyar ramawa. Take tayi murmushi tace "kana director a finance. Kira na Education kawai ka sa a sallami mijin nata daga aiki. Ai dai dama karyarta ta sa ce. To datse samun nasa muga tsiya". Jikinsa har kyarma yake saboda jin dadin wan nan gurguwar shawara da matarsa ta ba shi. Takwas na safe kuwa a gidan Murtala tayi masa. Ya kuwa nemi abokinsa ya kuma nuna masa abin da yake son ayi kuma yama kara da son abata takardunsa kar ya samu damar neman aiki. Summary dismissal yake son abashi. To shi ma na education din akwai voucher cuwa cuwa da ya ke son ya tura finance din ayi masa approving kuma shine mai sa hannu. Take suka yi trade by bater. Voucher a nan office din aka sa masa hannu ba tare da an sha wahalar kaita ba. Yayin da shi kuma yakira education secretary na zone din ya bada dokar a sallami mijin Khadija daga aiki. Kafin sha daya na safe kuwa takardar sallamar ta isa ofishin principal din Garko science. Har kuma da sharrin dalilin korar tasa saboda kama shi da akayi yana soyayya da daliba a makarantar. Shi dai principal na Garko ya samu bakuncin ES na zone din su da kuma bakar takarda korar karen da aka yi wa Mallam Usman. Ya tambayi dalili ES yace masa "kafar manya ya taka." "To kuwa ko zan tozarta kowa banda Mallam Usman. Saboda haka ina mai shawartar ka da ka canza lafazin cikin wasikar ka. Kora kuke so to ku sauke shi ba dalili amma banda kazafi". Principal din ya fada. ES ya tashi zai masa jan ido shi kuwa ya hado masa gangamin sauran malaman . Take kuwa 'yar karamar zanga zanga ta fara faruwa a makarantar. Shi kuwa Mallam Usman baima san abin da ke faruwa ba saboda ya fita da wasu dalibai kai ziyara kafin ciri dam. Ya dawo ya tarar da hatsaniyar da ake a cikin makarantar Inda sauran malamai suka dage in dai aka kori Mallam Usman to suma kuwa sai dai su ajiye aiki. Shi kuma ES YA DAGE IN DAI principal bai sa hannu a takardar sallamar nan ba to kuwa sai dai duk su rasa aikinsu. Vice ne ya daure ya fahimtar da Mallam Usman abin da ake ciki. Ba shiri kuwa ya gano fada da tsohon mijin matarsa shi ya haddasa masa rasa aikinsa kuma har yana neman ya zamo sanadin da abokan aikinsa zasu rasa nasu. Ba tare da doguwar shawara ba ya dau takarda ya rubuta shaidar ajiye aiki ya kuma tilasta principal ya sa hannu. Principal ya karba amma yayi masa alkawarin taya shi neman wani aikin ya kuma umarce shi da ya kawo takardun matarsa su dauke ta temporary tun da shi yana da hurumin daukar irin wadan nan ma'aikatan. Da wan nan mummunan labari ya isa wajen matarsa. Ya dai shaida mata cewar yana cikin malaman da gwamnati ta rage. Amma ya nuna mata ta kawo nata takardun za a taimaka masa ita a samo mata aiki. Ya kuma samu ta yarda da maganarsa. Har kuma ta yarda zata ba da takardun. Kwana biyu a tsakani ta kaiwa matar principal ziyara saboda ta yi mata barkar matar kaninta da ta haihu. Anan ta samu labarin abin da ya faru. Da tsananin bacin rai ta dawo gida. Nan kuwa ta tarar da mijinta. Ba ta bata lokaci yi masa bayani ba tace da shi "abban hafsa aramin wayarka". Ba tare da tunanin komai ba ya mika mata wayar. Shi dai yaga tayi kira sai kuma yaji ta sake cewa " yi hakuri zamu gaisa an juma. Yanzu nambar yayanki zaki tura min". Bai ji me akace daga daya bangaren ba amma yaji ta ci gaba da fadin "zan miki bayani ba wani abu bane". Daga haka ta kashe wayar. Shigowar sako da kuma kiran data dora shi ya sanyi shi fahimtar me take yi. Cikin kakkausaurya yaji tana fadin "sannu shugaban ma'aikatan duniya. Zauna ka dawwama aikin gwamnati. Amma ka sani ko ba retire akwai mutuwa. Kuma kai din nan kayi kadan ka iya kuntatawa rayuwarmu. Aiki an bar maka shi. In har kana ji ka isa ka hana mu shakar numfashi san nan zan san ka cika sunanka Abdullahi dan Zubairu. Amma ka sani ......." wuf taji an fixge wayar daga hannunta. Ta juya takalli mijinta wanda shi ma alamun bacin rai sun bayyana karara a fuskarsa. "Ashe baki da kunya ban sani ba. Ashe ko ba komai ba zai ci arzikin da ya kasance yaya a wajenki ko kuma ki duba darajar Zainab ba . Amma kika rufe ido kina gaya masa duk abin da ranki ya ayyana miki. Kin je kawai kin jiyo tsegumi a waje kika hau kai kika zauna." "Ke nan akwai abin da ya faru ka boye min". "Ni ban san komai ya faru ba. Aiki ne Allah ya kaddara abincina ya kare a kai sai kuma me". Shiru tayi ta kasa bashi amsa. Maganganu ne dankare a ranta amma ta kasa gaya masa. Tarbiya yayi mata ta mutuntuwa bata fadi in fada ba. Saboda haka ta kasa mayar masa da martani ko kuma ta ci gaba da yi masa musu. Sai kawai hawaye da kezuba a fuskarta na takaicin abin da daddy Zainab yayiwa mijinta. Ganin tana kuka sai kuma ya sassauta muryarsa ya kamo hannunta. Cikin muryar rarrashi yace da ita "kin ga Khadija ki yi shiru mu zauna mu tattauna yadda zamu shawo kan lamarin. Kuma kin ga principal yayi min alkawarin zai taimaka miki ke ki samu aikin a makarantar". Haka ya dinga rarrashinta sai da yaga tayi murmushi kuwa san nan shima ya murmusa yace "haba kin bi kin daga min hankali. Sanadin 'ya'yanki su dawo su tarar da ke cikin yanayi na bacin rai su dauka nine ba su san baban su director ne ya jawo ba". Ranar kuwa kwana tayi tana shawara wadda zata fisshesu