Sashe 35
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai da gumu ta gumu aka gano cewa ashe Ibira ne. Yanzu haka bata san inda yake ba”. “Allah ya kyauta”. “Amin. Ai ke ta so da irin wan nan auren sai kuma Allah ya kare ki komai ya koma kanta”. Kiran sallar isha ya tashe su daga hirar. Tana idarwa kuwa, ta tarar da miss call sun kai goma na habibiy kamar yadda tayi saving number sa a wayarta. Tana kokarin kiransa taji wayar Fatu ta dau kara. Fatun na ganin shine ta danna speaker, tare da yin sallama. Sai da ya amsa san nan yace “saboda Allah Fatu kin yi min adalci ke nan. Da rana da ruwa da iska duk suka kare a kaina, a kasuwar gwanjo da kuma turin mashin, amma matata tazo ki tsare min ita ki hana ta dawo wa gida”. “Ni na isa in tsayar da matar bala Mai gwanjo. Wai yawo na raka ta gidan sauran kawayenmu su gaisa”. “Don Allah kiyi min rai. Matar tawa kika dauka zuwa yawo. Kice yau duk tsoffin samarinta sun gama kalle min ita”. “Ai sai dai suyi kallon amma ka sha gabansu. Ka tuna fa suma akayi saboda an dauka an rasa ka”. “Kuma fa da wan nan da wanan. Amma yanzu taimaka ki fito min da ita. A gajiye na dawo gida, amma rashin ganinta ya sa na kasa zama a gidan na biyo sawu”. “ai kuwa komawa zaka yi don sai ta kwana biyu zata dawo”. “ba matsala, ai dakin Baana ya na nan sai mu zauna a ciki”. Dariya suka tuntsere da ita dukkan su biyu. Fatu ce tayi masa iso ya shigo ya gaida Mama Hajjo. Da ya tashi fita kuwa ya ajiye mata dunkulen dubu dari a wajen. Ita kuma ta sakko da akwatin tsarabar su daga mota ta mika mata. Tun da Fatu ta rako su soron gidan yake makale da ita a hannunsa kamar zata gudu. A motarsa range Rover suka shiga domin komawa gida, shi kuma driver ya wuce da motar da ta zo da ita. Washe gari ma kuwa ta kaiwa Baba Laure ziyara a gidan da suka koma. Ta yaba kwarai da girman gidan, saboda bangare guda suka zuba kiwon kaji wajen dari biyar ga kuma wani kango da suka zuba tunaki a ciki. San nan ga wani sashe inda ‘ya’yan mallam maza guda biyu suka dawo da zama. Kowa da sashensa mai dauke da dakuna uku da falo da kici da bandaki biyu. Dama su ke nan yaransa maza. Nan ma dai ta dada jinjina samun tabarbarewar da gidan nasu ya dada yi. Nan baba Lauren ta sanar da ita sak abin da Mama Hajjo da Fatu suka gaya mata jiya. Ta kuma shaida mata cewar, sana’a ta tsaya cik. Tun tana karbowa ta jagwalgwala ta kasa yi har abin ya soma zama rigima da customers ta hakura. Baba laure ta ci gaba da fadin “ai ni ta so ta jibgawa wan na wahalar, ni kuwa Alhaji Yana bawa Mallam kyautar gidan nan na tattara na gudo. Ba irin masifar da bata yi ba ni kuwa na kekesa kasa na ki komawa. Ai ko shi mallam saboda Dadi yake zaune. Kin san yanzu lafiya ta yi masa karanci”. A dan firgice ta tamabayeta abin da ya samu Dadin. Ta amsa mata da cewa ciwon suga ne ke damunsa. Sai da ta gaya mata san nan ta tuna da ramar da taga ya dan yi. Ita ma dai nan ta bar mata tata tsarabar ta dawo gida. [8/9, 13:59] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 31 BY HANNE ADO ABDULLAHI Zainab dai ta zama ‘yar gata gaba da baya. Ba wurin miji ba, ba wurin yayyensa ba. Ga kuma dangin ta na wajen uwa da uba wadan da suka mai da ita kamr kwai domin laillaya. Ita kuwa Umman su Al Bashir yadda take ji da autanta haka take ji da matar sa. Kuma hausawa kance halin mutum jarinsa. Ko baki ta samu labarin Umman tayi gaisuwa ce kawai zata hada ta dasu. Tana fita kuwa ta shiga kitchen dinta ko na Umma sai dai kaga masu aiki na shigo da kabakan abinci kamar dama an san da zuwansu. Haka wata rana umman ta dan hadu da tsautsayi. Accidenta tayi amma bata ji ciwo sosai ba. Ta dai dan kukkuje. Kun san mutan garinmu da zurfin tunani da kuma son zumunci haka suka ciko bus biyu manya. Daya cike da mata sama da goma daya kuma maza. Babu kuma wanda ya san da zuwansu. Duk iya kokarin mutum ba zai iya wadata mutum sama da ashirin da abincin da bai san da zuwansu ba. Ita dai tana ganinsu ta zare jikinta ta koma gida. Industrial kitchen dinta ta shiga. Allah yasa tana da ajiyayyun snacks wanda tayi wa yaya A’I ba ta zo ta dauka ba. Shi aka fara soyawa aka gabarta musu da ruwan lemon kanakana. Ko ba komai ta san zai iya rike su kafin dai awa daya ta gama abinci. Kafin awar nan kuwa ta cika, ita da masu aikinta guda biyu sun sauke tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa wacce ta sha naman rago. Gefe guda kuma ga ferfesun kayan ciki da aka hada da shi. Ba su gama ba sai gata ta shigo da katon tray dauke da yankakkun kayan itatuwa. Nan ta zauna aka fara gaisawa. Caraf kuwa facalar Umman matar wan Abbansu ke nan mai suna baba kulu ta ce “hm sannu isasshiyya sai yanzu kika ga damar zuwa gai da mutane”? To dama kowa ya san ta da neman Magana da kuma sa ido. Umman ma sai da suka kwashi adashin tsiya taga ba abin da zata dauka a wajenta san nan ta samu lafiya. Ita dai ba tayi magana ba ta sunkuyar da kanta kawai. Bata hakura ba ta sake cewa da umman “dama haka surukar taki bata san darajar mutane ba aka ishe mu da matar auta mai hankali. Ina hanakalin yake iyayen mijinki suzo sama da awa biyu amma ki kasa shiga ki gaishe su”. Ta sake juyawa ta kalli Zainab ta ci gaba da cewa “ki bar ganin daga kauye muka zo, mune dai asalinsa”. Ita Zainab tun da tazo gidan ba wanda ya taba yi mata ko da kallon banza balle a kai ga fada. Rabonta da jin fada tun a gidan momi, sai kuma yau da wan nan azababbiyar baba Kulun ta dasa nata. Umman Al Bashir na kai kallonta wajen Zainab taga yadda take share hawaye. Mikewa tayi daga inda take zaune ta karasa wajenta. Ba ta ji kunyar kowa ba ta jawo ta jikinta tana goge mata hawaye tana fadin “yi shiru matar auta. Kar ki bari wani abu ya bata ranki har dan uwana ya shigo ya tarar da ke a yanayi na bacin rai. Kin san ko yaya ranki ya baci shi ma kasa sukuni yake”. San nan ta maida hankalinta wajen baba kulun tace “kin san mutane kowa da irin tunaninsa. To ita Zainab nata tunanai na in taga baki sun iso ta yi iya iyawarta ta wadata su da abin da su ci su sha, kafin ta zauna luguden lebe. Ai kema dan kin koshi ne da kabakin data kawo miki shi yasa har kika samu damar aibata ta”. “au Allah akan matar danki kike nema ki gayan min bakar Magana. In dai surukan zamani ne gaki ga su. Idan kin dawo kina kukan an janye miki da ke kika jawo wa kanki. Ko da yake naki ma sunan sa janyayye kamar yadda kika janye dan wata dole kema sai an janye naki”. Dariya Umman tayi saboda ta gane abin da take son fada Kenan. Ta ce “ai ni kowa a dangi ya shaida tsakanin na da surukuta mutuntuwa ce da kyautatawa. Kuma yadda ta rike ni haka kuwa zan rike wacce aka kawo min”. “aikin banza kamar ba mu san komai ba. Ba asiri kikayi musu ba ita da dan nata suke fifita ki sama da kowa”. “kash yaya Kulu kin sha fadar maganar nan na kuma ce ki shirya in raka ki wajen malamin da yayi min aiki a akansu ko kema kya samu yayi miki”. Wata ce a cikin matan dake zaune a wajen tace “Don Allah Hajiya kyaleta. Shi zaman duniya ai kowa da halinsa yake yinsa. A danbatta gaya min gidan da bakiyi fada da su ba. shi yayanmu ai don mai hakuri ne da kuma Dadan data hana shi sakinki shi yasa kike ganin kamar kin fi karfin kowa. Kin fi so yadda kike sa in sa da naki surukan itama ta dinga yi da tata”. Ita dai Zainab jiki a sanyaye ta miki daga wajen ta koma sama wajen Meena.Wan nan kuma shine abu na farko da ya taba mata rai a gidan mijinta daga shi kuma bata sake haduwa da wani ba. Yadda suke son Al Bashir kusan itama haka suke nuna mata. Amma fa gidan Dr Abdullahi Zubair ba haka abin yake ba. Saboda dai dadi ya gaji da kazantar da kuma kwaben abinci da ake yi a gidansa. Ashe itama Momin ko ta manta ne ko kuma dama can girkin da sauki oho. Amma ko ita da kanta tayi abinci ba dadi yake yi ba. Baki kuwa ya daina gayyato su, saboda idan ya kawo su kunya yake ji. Gida kaca kaca ba gyara. Ransa bai kara baci ba, sai ranar da ya fito daga masallaci suna gaisawa da malamin islamiyyar su Zainab, yake masa godiyar abin arzikin da mijin Zainab ya aika masa. Shima yana murna ya ke ce masa “ai mallam zainab kam abin na ta akwai albarka a ciki. Kaga dai da uwar ta so taki auren saboda wata jita jita da taji amma yanzu ga shi nan Alhamdu Lillah komai nata yana tafiya daidai”. Shi ma yasayyadin ya dora da fadin “biyayyar Zainab da kuma kwazonta ba zai tashi a banza ba”. “kayya mallam Auwwalu. Allah dai ya shiga cikin lamarin. Amma Zainab ai na sha wuya da ita a gidan nan. Kullum sai an kawo min kararta, ga kuma dakikanci da ta dorawa kanta. Ba yadda ban yi da ita ba tayi karatu amma sam yarinyar nan taki”. Da mamaki yasayyadi yace “ita