← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 43

Sashe 39

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

tayi wa Abbanta waya yake sanar da ita zancen auren kanwarta. Taje gidan da niyyar taji me ake ciki, Momi ta zazzage ta ta koreta tana fadin bata son ganinta a harkar bikin ‘yarta. Har tana fadin “in don ganin wan nan dan kudin na mijinki ne ya sa kikewa mutane gani gani. Jira kiga inda ake harkar arziki. Shi iyayensa ban da kudi har mulki suna da shi”. Batayi la’akri da cewar shi kudin mahaifin sa bane, sabanin Albashir da yake da halastacciyar dukiya ta halal. [8/9, 14:16] +234 814 948 5104: FINI A UBA👪👪 IN FIKI A MIJI💏💏 PAGE 33 BY HANNE ADO ABDULLAHI Duk abin da ake yi na shirin biki, Zainab bata da masaniya. Shi kansa dadi bai san komai ba. Ya dai san ranar daurin aure da kuma wanda zata aura. Amma ban da haka bai san duk wani shiri da ake ciki ba. Tayi niyyar gudonmowa Momi ta nuna bata da ra’ayi bata son komai nata. Duk da haka ta bawa mahaifinta kudi naira miliyan biyu da sunan ya rage hidima. Yaya A’I ce, ta kawo katin gayyatar na bikin Salim da kuma Farisa wanda dinner ce ta gidan maza. Tare suka yi makaranta da mahaifiyar yaron, amma sanin yadda take gudanar da lamuranta ya sanya bata mua’mala da ita. Amma ganin sune manyan garin ya sanya uwar angon nacewa sai ta gayyace ta, saboda duk uwar darin ce ita da uwar amaryar. Professional class strugglers ne. ana fito da kati, Zainab taga sunan kanwarta ajiki. Ita kuwa yaya A’I tana mitar ba zuwa zatayi ba, saboda bata son halin mamin Salim. Umma ce tace “Maama baki da kirki yarinyar nan tana sonki tun kuna yara amma ke kin kita”. “Umman ba son ta ne bana yi ba. Gaskiya ba zan iya hulda da ita ba. Kina ga yadda son abin duniya ya zarme mata tayi destroying gidan mijinta gabadaya. Kwata kwata ya daina kula uwar ‘ya’yansa sai ita da yaranta kawai. Ba yadda za ayi ki ga sauran yaran ki dauka wai uban su daya da su Salim. Su kullum suna yawon kasar waje amma ita kuwa tana faman yadda zata biya kudin karatun yaranta anan Nigeria. Amma ba komai kanta ta yiwa. Gata dai nata sun samu amma tarbiyya ita kuma waccan din nata sun yi zarra. Ta dai samu duniyar, amma ni tausayin yariyar da zata auri salim din nake. Yaron kwata kwata ba shi da dadi”. Zainab ce tace “maama kin san su da kyau ne”? “Tun secondary muke tare da ita”. Sai da tayi ajiyar zuciya san nan tace “Maama kanwata zai aura”. Cike da mamaki suka maida kallonsu gareta. Umman ce tace “yanzu ke da gidanku bikin a gidanku kuma jibi za a fara amma baki sanar da mu ba”. “umma kiyi hakuri nima ban san an kusa bikin ba. Farida dai ta sanar da ni an kusa auren amma ban san komai ake ciki ba”. “Allah ya kyauta” inji Umma. San na ta juya wajen Yaya A’I tace zaki iya samo mata katin zuwa saboda bai kamata ace bata je ba”. “ai ko kati dari na nema zan samu, saboda hadaddun mata take so a wajen bikin”. Take kuwa ta buga mata waya akan tana bukatar more cards for her family. Tana nan gidan kuwa sai ga driver ya zo ya kawo mata about twenty cards, amma fa dangi an hana su saboda ‘yan gayu ake so a bikin. Umman kuma ta sanya ta ta aikawa har mamanta da kanwarta da kuma wasu friends dinta. Gayya dai suka saka tayi sosai. Bayn nan Yaya A’I ta nemi wata kawarta dake Lagos, tace mata hadaddaiyar souvenier take so kuma nan da two days take sonta. Ta aika mata details din amarya da ango da kuma sunan presenter. Ranar Thursday za a gabatar da dinner ta gidan maza, saboda haka Zainab da tawagar ta, ta kusan mutum ashirin ta isa venue din. Da gani kasan bikin na manya ne. kuma ita dai yaya A’in ta bawa MC sunan Zainab. Har announcing arrival dinta akayi. Su kuma su ka biyo ta cikin rausaya na kidan da mc ya saka musu. Ga kwalliyarta tadaukar hankali, kamar itace amaryar don kuwa tama fi amaryar kyau, saboda ita farisa iyayi yayiwa a kwalliyar tata yawa sai taki yin kyau. Da kyar momi ta danni zuciyarta saboda bakin cikin yadda taga Zainab tayi stealing show din bikin. Ga kuma VIP seat da aka ware musu ita da jama’arta. San nan ga kuma dinbin souvenier mai dan Karen tsada da kyau data raba. Wani set ne na kayan wanka da ya kunshi bath robe da towel na fuska da na jiki da kuma nakai an nade su da kyau aka saka acikin wata jaka mai daukar hankali. Duk kuwa wanda yazo fita daga gidan bikin nan sai da aka mika masa tsarabar nan. Biki dai yayi biki. Mata kuma an sha shagali. Saboda tsabar duniyanci, uwar amarya da ango suka taka rawa tare. Ga barin kudi da aka dinga yi kamar ba gobe. Su dai Zainab da convoy dinta da suka yi gracing occasion sukayi sallam suka tafi. Washe gari ma ranar wuni umma ta sake tilasta ta akan sai taje. Tunda ta ga take taken Momi taje ta gyara dakin boysquaters inda baba Laure ta tashi. Nan ta shirya ajiye dangin mijinta. Kafin ta taho kuwa, sai da ta bada sallahun yaran da suke kamata aikin catering dinta suka hada mata variety na abinci mai yawa, saboda har da mutan kera tayi saboda suma ta san ba lalle Momi ta mutunta su ba. To cikin hukuncin ubangiji abinci nata shi ya rufawa Momi asiri saboda wadanda taba wa aikin nata abincin sun yi disappointing dinta. Amma kusan ba laifin su bane ita ta bada dokar kar a kawo mata abinci da wuri saboda ta fi son sai mutan kauye da kuma locals sun tafi san nan ta fito da better for her special guest. Hakan kuwa akayi. Su kuwa dangi Zainab ta ciyar da su, sanna ta bawa kowa kyautar atamfa irin ta kamfanin mijinta, san nan tayi oder hummer masu kyau domin su mai da ‘yan uwanta gida. Sai goshin magariba kuwa aka dinga shigo da variety, amma Momi tayi rashin sa’a saboda da yawa daga mutanen da take expecting basu samu zuwa ba, saboda a ranar kuma bikin ya hade da na wata ‘yar perm sec. Saboda haka can akayiwa rubdugu. Kunsan harkar bariki ko zumunci is for the highest bidder. Nan dai taro ya waste ya barta da tulin abinci da sai dai a zubar ko a bawa alamajirai. Washegari kuwa dinner Momi ce itama kuma an kashe mata makudan kudi. Ga guri yayi kyau. Ga abincin an hada shi kamar ba gobe. Amma fa amarya da uwarta basu zoba sai bayan tara na dare. Albashir dai da ya kawo Zainab ya tokare jikin kofar da take zaune ya hana ta fitowa. Fatu tana tsaye tana musu dariya na wan nan kankagewa da yake mata. Shi kuwa fadi yake yi “mh mh barni Fatu. Kinajin sanyin da ake a garin nan in barta ta fito wan nan filin. Ina ba zan iya ba”. Bayan dai dogon zama da aka bar mutane suan jira, sai ga Momi ta shigo cikin rakiyar kawayenta ta sun sha kwalliya sun gaji, sai ya zamana kamar ma sune amaren. Da rawa suka shiga, amma basu fi minti biyar da fara rakashewaba, sai ga wata iska ta taso. Kafin minti biyar wuri ya harzuke. Decoration sai fadowa kan mata yake. Ban Ankara ba sai na hango gwaggwarayen kan mata yana tashi a fili. Wuta ta dauke. Bakajin komai sai hayaniya. Du iskar nan bata fi minti hudu ba, amma ta’adin da ta yi saika dauka ‘yan daba ne suka kai farmaki filin. Abinci cike da chaffing dishes duk ya bude da kura. Shi dai Albashir ya maida kofar motarsa ya rufe ya sa su Fatu suka shiga domin ya ajiye su a gida. Tun da suka dau hanya yake tintsira dariya. Har Zainab ta gaji ta ce “wai dariyar me ka keyi ne kai kadai”? Sai da ya sake sakin wata dariyar yace “dariyar hadaddadiyar dinner da ban taba halarta irinta ba nake. Fatu baki hango Momi ba kafin a dauke wuta ta dafe dankwali tana kukan na ganin yadda akayi fata fata da hidimar da ta hada”. Dukan wasa ta kai mishi. San nan tace “Momin tawa kake wa dariyar mugunta”? “ni na isa in yiwa surukata dariya, murna kawai nake taya ta. Ni na isa in yiwa Momi dariya. Ai tana da value a wajena sosai. Ki tuna fa har mai gwanjo na zama saboda kawai in bi dokar ta ai kuwa kinga ina mutunta ko”? ya fadi tare da sakin wata dariyar. Haka bayan ya sauke su fatu nan ma ya daddage wajen bawa Umma labarin crises da ya faru a gidan party. Yana dariya kuwa har da sukewa ita ma Umman na taya shi. “kai Umman har da ke a tsokanar Momi”. Cikin dariya tace “yi hakuri matar dan uwana. Ai duk wanda yace tukunyar dan uwansa ba zata tafasa ba, Allah ba zai sa, tasa tayi ko dumi ba. Ta dauka haka zata share kalau. Ai da saura ma”. A can kuma cikin motar amarya da ango, masifa yake zuba mata kamar zai daketa a wajen yan fadin data fito da wuri bata tsaya bata lokaci ba ai da duk haka bata faru ba. Ita dai Farisa kukan abu biyu take. Ga na bakin ciki biki ya baci ga kuma na bakin cikin masifar da Salim yake mata. Ya ma mai da ita gida a kawo ta washegari kamar yadda aka tsara, yace in har bata bishi sun wuce ba a lokacin to kuwa sai dai auren ya rabu. Haka ta hakura ya wuce da ita gidan sa yana duddura mata ashar kamar ba sabuwar amarya ba. Washegari kuwa Abban su Albashir ya aiko da sakon kayan gara komai goma goma gidan su Zainab. Suma dai wan nan din ne ya rufa mata asiri, saboda duk abin data karba ta narkar da shi a ganin ta yi haddaden biki, har kuwa da kudin garar. Tayi haka da tunanin zata samu gudummowa saboda
Chapter 39 · 0% Book details