← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 43

Sashe 17

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ku a gidan nan”? “Ai kuwa haka take fama kullum”, ya amsa masa. Sallama suka yi ya karasa bakin mashin din Sule ya dauko leda mai dan girma ya mikawa Mallam yace “don Allah mallam kar ki karba. Kayi hakuri”. Sai bayan ya tafi Mallam ya bude yaga kykkyawan yadi mai laushin gaske da kuma turmin atamfa duk da bai san kudin su ba, amma tabbas ya san masu dan tsauri ne. [8/6, 23:25] +234 814 948 5104: FINI A UBA I👪👪 N FIKI A MIJI💏💏 PAGE 19 BY HANNE ADO ABDULLAHI kusan tun da suka rabu da Al Bashir cikin tunanin sa take. Da ta tuna wata Magana da suka yi shi da ita sai ta saki murmushi kamar wata sakarya. Ita Kanta bata san sanda murmushin yake kwace mata ba. Baba Laure na hankalce da ita, har ta kasa daurewa tace “uwata yau wane irin nishadi kike ciki ne. ni dai ina ga Balaraben nan ne sanadin wan nan farinciki naki”. Kunya taji matuka na yadda ta bari har baba Laure ta gano yanayin shaukin da ta ke ciki. Ba ta dai amasa mata ba. Amma fa duk da haka yanayin fuskarta bai canza ba. Yau bata da aikin snacks, amma Momi ta sanar da ita da safe da waina da ganda zasu karya a gidan. Kuma ta tabbatar sun dahu kafin bakwai da rabi na safe. Ganin ba pressure pot garesu ba, ya sanya ta hada gawayi a makubur din su, ta hada gandar ta dora ta barta tana dahuwa a hankali. Niyyarta data gama hada kullin masa, sai ta kwanta. In yaso ta samu bacci ko na awa hudu, san nan ta tashi tayi kokarin yin nafilar da ta saba, sai ta hau danin wainar. Kirrrrr karar waya ta katse mata tunani. Tsayawa tayi tana kallon fuskar wayar kamar fuskar mai kiran zata gani a ciki. Sai da tayi ringing uku san nan ta sa hannu ta latsa kiran. Sansanyar muryarta ce ta doki kunnensa wanda ta aika masa sallama da ita. Shima cikin shauki ya amsa mata. San nan cike da zolaya yace “ina fatan yau tunani nane ya hana ki bacci”. “idan yin hakan laifi ne ayi min afuwa, zan daina”. “haba putri salju. Abin da nake addu’a ya kasance sai kuma ince an yi min laifi. Ai fatana in shiga zuciyarki in yi kane kane, yadda ba wanda zai samu shiga, wanda yake cike kuma in hankido shi waje ya fada kwata”. Dariya kawai tayi san nan tace “kar ka wahalar da kanka. Barka da dare”. “barka kadai putri salju”. “sai dai ka san ban san ma’anar sunan da kake kira na da shi ba. Kar ko ce min kake zainab mai katon baki”. “Akwai madubi a tare da ke”? “a’a me kake so ayi da shi”? “So nake kije ki tsaya ki karewa kanki kallo. Ki gaya min meye bashi da kyau a fuskarki, kama daga goshinki mai kyalli kamar watan dan dare sha hudu. Wanda ya fito da kyawawan dara dara kuma fararen idanunwanki. Su kuma suka hadu suka kara fitar da kyakkyawa siririn hanci , wanda da ya taso bai tsaya a ko ina ba sai da ya iso inda kyakkyawa bakin ki mai dauke da siraran labba, wanda cikin sa yake cike da kanana, hakora farare tas da su. Af nayi mantuwa akwai wata siririyar wushirya da ta dada kawata su. Kamar yadda fuskarki ta kawatu da dimples. So ki duba a madubi kiga ina na kuskere ban fasalta ba. Ko kuma ina kike jin na fadi da daidai ba”. Murmushi kawai tayi ta kasa bashi amsa. Sai shine ya sake cewa putri salju yana nufin coolprincess, kuma wani yare ne na wani gari dana taba zaman ci rani”. Bata gane me cool proncess din ke nufi ba, amma dai ta daure bata nuna masa ba. Ya sake ci gaba da tambayarta. “mu dawo maganar dazu, me kike yi baki yi barci ba”? “waina nake kokarin hadawa. Ko zaka ci”? “idan an bani mai zai hana. Ko yanzu sai in biyo in karaba”. Sai da ta sake dariya mai cike da nishadi san nan tace “a’a ba zaka samu yanzu ba, sai dai da safe idan zaka iya zuwa”. “wanda yace zai zo da tsakar dare ta ina kika ga safiya zata wahalar da shi? Karfe nawa ki ke son in zo in karba”? “Idan zaka iya zuwa takwas zuwa tara zaka same ni. Idan ka wuce haka kuwa zaka daki gurbi”. “in sha Allahu kuwa zan zo. Ke dai tanadar min waina ta. Yau ba kya jin labarai ne, ko dai hira dani tafi labaran dadi”? “kai yaya b………” bata san yadda akayi ba taji ta kasa kiran sunansa. Nan dai hira ta barke a tsakaninsu, duk da shi ke fiye da rabin zancen. Amma ga mamakin ita kanta zainab din kusan shine bakon mutum na farko da ta ji tana iya sakewa da shi har tayi musayar Magana da shi din. Washe gari kuwa zainab tayi abin da bata taba yi ba. Tana sauke naman nan ta debi parts masu kyau guda hudu, ta samu dan karamin flask ta zuba a ciki. Kafin takwas da rabi ta gama gyara ko’ina. Al Bashir na ganin motar Momi data dadi sun fita daga gidan, ya karasa ya shiga ciki. Kamar ko yaushe mallam ne yayi sallama da ita. Sanye cikin shudin uniform wando da riga da kuma cream colour hijabi na yadin makarantarsu ta fito. Hannunta dauke da flasai guda biyu. Bayan sun gaisa ta gabatar masa da wainar da tayi masa alkawari. Lomar farko da ya kai bakinsa sai da ya lumshe idanuwansa saboda dadin abincin nan. Bai taba cin waina mai laushin ta ba, haka zalika shima dahuwar jelar san tayi dadi matuka. Ga kamshin kayan kanshi yana tashi wanda daka bude kwanon shi zai maka sallama. A wajen Mama Hajjo ta koyi dabarar sa spices sau biyu a girki. Ta zuba kadan domin fitar da karnin daga farko san nan idan girkin ya dauko dahuwa ta kara kadan saboda ya fitar da kamshi. Haka zalika bata daka spices ta ajiye. San da zata yi girki san nan take daka su, saboda sun fi kamshi a haka. Yana ci suna hira yake tambayarta wacce makaranta take zuwa. “umar bin Khattab, ta’alimul Qur’an” ta amsa masa. “iyeh ashe mutuniyar tawa ya sayyada ce. Yanzu izunku nawa”? “mun yi sauka da biye shekara uku da suka wuce. Yanzu kuma saura mana bai fi izu goma ma mu gama da hadda ba. Wanda muna san ran nan da wata uku zamu hattama, saboda kasa ne. kuma tun lokacin muna biye mun samu haddar sama da izu talatin ku san yanzu maimaitawa ake”. “ma sha Allah. Ni kawai kice in sayo allo ga malama har gida. Ba bulala ba kudin laraba”. Dariya kawai tayi bata bashi amsa ba. Sai da ya gama cin abincinsa wanda ya cinye tas duk da yawan sa, san nan yace “thank you putri salju for a wonderful meal. Na san abin da naci will carry me for most of the day”. Tana jin yana tsaro turanci taga ya kamata ta sanar da shi cewa ita ba ‘yar boko bace, saboda kar yazo ko mai jin turanci yake so ita kuma ta yaudare shi. Sai da ta dan saci kallonsa san nan cikin sanyin murya tace masa “kayi hakuri ni bana jin turanci”? Shima cikin sanyin murya yace “Me yasa ba kya jin turanci”? “Saboda bani da kokari aka cire ni a makarntar boko daga primary na tsaya. Sai aka mayar da ni islamiyya”. “shekararki nawa Zainab”? “ashirin’ ta amsa masa a sanyaye. “kar ki sake cewa kanki baki da kokari. Haddar Qur’ani tafi ko wane karatu wahala. Duk kuwa wanda ya same ta, to ba wani karatu da zai gagare shi a duniya. Turanci kuma ba lalle ne kowa sai ya iya shi ba. Idan kikaje kasashe da yawa musamman yankin Asia da Europe duk da yaransu suke karatu da gudanar da harkokinsu na yau da kullum. A nan kasar ne kawai idan baka iya turanci ba mutane suke ganin ka koma bayan al’umma”. “ai kuwa ba dadi kowa ya iya abu ya zamana kai kadai ne baka iya ba”. “fine and good. In dai turanci ne mastalarki ni kuwa nayi miki alkawarin koyar da ke”. Take kuwa fuskarta ta kasa boye farin cikin da take ciki. Sai da ta shiga ta mayar da kwanukan da ya ci abinci san nan ta fito dauke da school bag dinta. Tare suka fita, shi yana tura mashin dinsa ita kuma tana gefensa suna tafe suna hira. A nan ya samu ya sanar da ita asalinsa da na iyayensa da kuma labarin yayyensa da family dinsu. Duk da dai ya rufe mata level of affluence dinsu, da kuma shi matakin karatun sa. Ya nuna mata shima iyakarsa secondry school daga nan ya shiga kasuwa. Tsoron kar ya kwafsa ya saka shi bai bata detail story na kasuwar ta sa ba. Sun fi minti arbain suna tafiya, kafin suka iso makarantar tasu . tabbas ya jinjina mata nisan makarantar da gidansu, amma ya lura yaga ita ko a jikinta hakan ke nuna ta saba da nisan. A bakin kofar makaranta ya sa hannunsa a aljihu ya dakko wrapper daya ta dubu goma sababbi ya mika mata. Bata amsa ba tsayawa kawai ta yi tana yi kallonsa. “Don Allah kar kice min bazaki karba”. “don Allah kar kace sai na karba. Kudin sun yi yawa”. “ba abin da yake da yawan da zan kasa baki shi. Kuma trust me kasuwar tamu yanzu akwai alkhairi. Please ki karba ko kudin break kya yi da su”. “Duk da haka mu bi komai a sannu. Kar mu durkusar da kanmu”. Yana kokarin yi mata magiya ta karbi kudin daga hannunsa ta zari guda biyar daga wrapper ta bude aljihusa na gabar rigarsa ta zura sauran a ciki. Yana kokarin yin Magana, tace “Please nima na roke ka mu bar maganar haka.in dai kyautar ce wan nan ta ishe ni. Shima dan kar kace naki karba ne”. Tana yi masa sallama ta shige gate din makarantarsu. Ta bar shi yana kallonta cikin tsan tsan tausayi. Yarinyar is so humble yet classy. Ita bata san
Chapter 17 · 0% Book details