← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 43

Sashe 14

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

[8/6, 23:20] +234 814 948 5104: FINI A UBA I👪👪 IN FIKI A Miji💏💏 PAGE 15 BY HANNE ADO ABDULLAHI A wan nan rana Al Bashir ya zayyana wa iyayensa duk abin da ake ciki game da yarinyar da yake son aura. Hajiya Rakiya watau ummansu tace “to yanzu ta ina za a bullo da wan nan Magana. Dan uwana ko dai hakura zaka yi. Ka nemi wata”. Ta kan kira shi da dan uwana saboda sunan yayanta yaci wanda kuma shidin aboki ne ga mijinta watau Alhaji Usman. Haka zalika ta sanadinsa aure ya kullu a tsakaninsu. Cike da rauni Al Bashir yace “don Allah Umma kar kice in hakura. Addu’a zaki tayani da ita”. Sai da suka kwashe da dariya ita da Abbansa san nan ya fuskanci zolayarsa suke. Suna haka babban amininsa yayi sallama ya shigo. Mujib abokinsa ne tun suna yara. Tare suka yi karatunsu da komai. Bayan gaisuwa iyayen suka shaida masa aikin da ya tunkaro abokinsa. Cikin tsokana yace “ai ina ga Abba abin da za ayi rumfa zaka sama mana a kasuwar mu zauna mu koyi irin nasu kasuwanci saboda kar muje wajen intabiyu a kure mu”. “very good ka kawo shawara mai kyau. Saboda haka gobe ka fito da sassafe ni da kai zamu fara zuwa wambai. Kuma zamuyi haka na tsawon sati guda saboda mu samu experience”. “You must be kidding me”. Mujib ya amsawa Al Bashir cike da mamaki. Su dai iyayen dariya kawai suke musu. Al Bashir cikin dakewa yace “nayi maka alamar ina wasa a cikin wan nan lamarin. So get ready my friend gobe zamu shiga kasuwa”. A haka suka sallami iyayen nasu. Washegari kuwa takwas na safe a kasuwar ‘yan gwanjo ta wambai ta same su. Ita kanta kasuwar da tambaya suka samo ta. San da suka shiga kusan da yawa basu fito ba. Amma yadda suka ga yanayin kasuwar abin ba Magana. Ga shi dama an kwana ana lafta ruwan sama. Ga kasar wajen baka kirin ta dame da ruwa ta koma wata kwata kwata. Site din kawai ya isa yayi discouraging din su. Mujib ya kalli wajen ya ga yadda yake yace “is she worth this wahala’?” “she is worth more than this”. Take ya manta da scenario da ke keyawe da shi ya fara wassafa masa Zainab. Fadi yake “you need to see her long slim fingers. Ga ta da wani irin skin mai wata irin creamy colour. The eyes Subahanallah. Idan ta kalle ka da su, sai ka ji gaba daya ka rasa sukuni…..” “Dakata Mallam sau nawa ka ganta har kake wan nan artist description din”. “Once my friend. Only once but it seems like I met her a thousand times. And the voice. When she speaks mallam the voice is so melodious like that of a trained singer”. Sai da Mujib ya kaiwa wani katon sauro da ke kokarin shan jininsa duka san nan ya sake cewa “just use the conventional way mu saki kudi kawai a bamu aurenta”. Ya shafi fuskarsa cikin damuwa san nan yace “this time around it wont work. Saboda akwai adversaries da ba sa son ta a luxurious life. In ba haka ba ai mahaifinta ma is well off. Saboda shine commisioner of finance na state din nan gabaki daya. I jut don’t know what is wrong wih her step mpther. She is the problem a yadda na samu labari”. “Ina ga the stepping in the mothering is the problem. Amma we will get more details idan muka hadu da ita yarinyar “ Wani saurayi ne ya katse musu hirar tasu a lokacin da yake kokarin bude shagon da suka zauna a bakin rumfar. Nan dai suka nuna masa kaya suke son sara suma su fara sai dawa. Shi kuwa sai murna yake yana fadin “ai bari mai gida ya zo kayan mu giredi ne”. Abin dariya sai da aka bude shagon suka ma fuskanci wadanne irin kaya ake sayar wa a shagon. Su ba su taba sanin wani yana saka kaya idan ya gaji da ita ya cire ya sayar wani ya saya ya saka ba sai a wan nan ranar. Da kuwa warin gwanjon nan ya buge su, sai atishawa tuk tuk. Shi kuwa saurayin sai fadi yake “ai in gaya maka baaba wan nan karon sabulun maganin kwarin da suka saka mai karfi ne. saboda wancan karon da muka dauko kaya da yake sabulun ba shi da kyau har da beraye muka samu a ciki”. Mujib na jin haka ya mike tsaye da sauri jin an ambanci bera yace “please lets get out of here kafin mu samu wani infection”. Jawo shi Al Bashir yayi ya zaunar da shi a gefensa san nan ya ci gaba da tambayar sabon abokin nasu wanda suka fahimci sunan sa Ahmad amman an fi sanin sa da swaggedeen. Nan dai ya shiga gaya musu irin alkhairin da ake samu idan an sai kaya a shagonsu. Yace “ka ga duk kasuwan nan ba wanda ya kai Alhajina sauke kaya giredi. In dai ana maganar shirt shirt to kuwa tamu tafi ta kowa kyau. Idan ka gansu sai ka dauka sabbi ne. gashi dealer ana yanka ta akan dubu sabain mu kuwa tamu sittin da tara ce. Kuma in gaya maka a kowacce dealer idan dai kai ka yanka ta da kanka, baka samu riga ba ka samu dari da ashirin. Kuma in gaya maka ko wacce riga zaka iya sayar da ita a kan dari shida zuwa bakwai. Kuma in gaya maka ranar da kasuwa tayi kyau zaka iya samun ribar dubu daya zuwa biyu. Ga wanka da zaka dinga dauka mallam. Shi ma duk a cikin ribar ne”. Gaskiya Al Bashir ya yaba da iya marketing na bawan Allah nan. Ba su gane kurensu ba, sai da kasuwa ta cika ta batse wajen misali sha daya na rana. Nan suka dada fuskantar yadda cinikin kasuwar ke gudana. Sun kuma yaba da kokarin bayin Allah dake neman halal din su. Amma fa situation report din su, ba dadi. Yanayin kasuwar kadai ya isa yayi discouraging dinka daka shiga saye ma balle sayarwa. Amma su yinin ranar haka suka kashe shi wajen koyon cinikin gwanjo. Da kuwa aka zo yadda ake bend down and pick din proper Mujib yana birkita kaya yana zagin Al Bashir saboda bai ga dalilin da zai basu wan nan wahala haka ba. Daga baya suka ga aikin bana wasa bane suka yi cinikin dealer biyu aka sayar musu da ita. Shi kuwa swaggedeen sai murna yake yi. Har da musayar lambar waya saboda gaba. Sun sai kayan da sunan bari suje su dawo. Kuma har kudin sun biya. San nan suka fita daga kasuwar. Suna isa gida wanka kawai suka shiga kafin suka isa wajen ummansu domin su sanar da ita yadda ta kaya. Yaya Ai da ta shigo ta tarar da abin da ake ciki ta kwashi dariya kamar cikin masaki saboda yadda Mujib ya dinga kuranta irin wahalar da suka sha. Cikin dariya tace “kaga ai kun shiga shadin ‘yan kasuwa”. Shi kuwa Abba da yaji yace “ina fatan zaku dada appreciating talaka da wahalar da yake ta neman halal din sa”. Plan b da suka aiwatar shine na nisanta Sulaiman da campaign headquarters dinsu saboda kar a hadu wata rana ruwa ya balle. Take kuwa Mujib ya bada shawara a tura shi branch office din su na China saboda yayi nisa da su, sai komai ya kankanma. A cikin sati kuwa komai na tafiyarsa shi da iyalinsa ya kankama da sunan zai yi shekara daya a wajen. Shi kuwa Mallam mai gadi da ya ga an dauki tsawon kwana takwas ba Al Bashir ba dalilinsa sai ransa ya baci. Saboda tun da ya ba shi shawarar nan shi kuwa bai tsaya da addu’a ba. Rokon Allah yake ya hada kawunansu ya kuma tabbatar da alkahiria akai. Sulaiman na barin kasar suka shirya da la’asar shi da Mujib zasu zance. Umma na kallonsu kowa ya sha gogaggiyar shadda ta gani ta fada wacce da gani kudin ta ba za su kasa dubu dari ba yadi biyar kawai. Ga uban turare designer da suka bulbula, tace “zancen za’a ne haka”? “Eh Umma” Mujib ya amsa mata”. “Ashe kuwa da kun tonawa kanku asiri. Yanzu ku kuma ai sai dai ku nemi kayan gwanjo ku saka. Kuma a wacce motar zaku”? “Wai da a final din da ake kai Meena makaranta zamuje tun da it’s the cheapest car a gidan nan”. Sai da tayi dariya san na tce da su “shi mai sai da gwanjon ne ya ke da mota kuma final discussion? Ai sai dai ku ari babur din Sale mai guga”. Suka shiga suka canja shiga inda suka saka kananan kaya. Ko ba komai su ana samun irinsu a gwanjo duk da dai nasu sun so su tona musu asiri, amma dai sun dan badda kama. Tun da suka hau mashin din nan suka tafi Mujib yake masifa a hanya. Saboda ko sanda suka yi yayin hawa mashin din nasu bike ne irin dirkeken nan. Fadi yake muna zuwa naga bata kai yadda kake fada ba, I will call off the deal sai dai ka nemi wata”. Shi ma kuwa with full confidence yace “na yarda. Idan har ka ga she is not worth the trouble zan kyaleta in nemi wata”. Wajen Mallam mai gadi suka fara isa. Ba karamar murna yayi ba lokacin da ya gansu. Shi yayi musu iso wajen Dr Abbdullah Zubair watau mahaifin Zainab. Daga falon suka tabbatar da cewar gidan masu shine suma. Momi na gefensa ta hakince. Tun daga amsar gaisuwar da yayi Momi bata sake barinsa yayi Magana da bakin nasa ba. Ita ta sake tambaya inda yake sana’a yace a kasuwar wambai. Tace “rumfa gareka ko kuma rabuwa kake da wani”? Mujib ne “yace gaskiya Momi bamu da rumfa a nan dai muke tsayawa bakin hanya”. “kuma a rana ku kan samu kamar nawa”. Cikin wani irin ladabi na karya yace “a rana mukan samu ribar wajen dubu daya randa kasuwa ta yi kyau har da dari biyu ko uku”. “yama kace sunan ka”? “ni sunana Balarabe Usman”. Al Bashir ya amsa mata saboda shine sunan da kakkarsa ta wajen uwa take kiransa
Chapter 14 · 0% Book details