Sashe 32
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
nan zai ba da dokar lallai kafin ya dawo ya tarar ta haddace su. Kuma hakan take yi. Ba ta shara bata wanke wanke ba wanki ba guga. Saboda haka sai ta samu enough time to face her studies. Tana kuma da wani web site wanda ita ta lalubo shi da kanta, bai ma san ta kai wayon haka ba. Duk abin da ya kakare mata a wajen za ta duba ta ga yadda zata gyara. A yau da ya fita bai dade ba ya dawo, saboda yana son suje shopping. Tare suka shiga mall din suka nufi wajen kayan mata. Bawan Allah nan ya sai mata kayan mutunci , yaki sai su dogon wando da su three quarter and other revealing out fits yake zabar mata. Da kyar ta samu a wani shagon larabawa ya saya mata dogayen riguna masu kayan gaske. Suka shiga wajen undies. Kunya ce ta kamata ganin shi da kansa yake duba inner wears. Ya gane yanayin data shiga amma sai ya share kamar bai gani ba. “Putri wane size zamu dauka”? ya tambayeta lokacin da ya dakko wata shudiyar rigar ciki mai dan banzan kyau kamar ka saka ta a saman riga. Kudinta ba zai kasa dubu ashirin ba kudin Nigeria. “putri I am talking to you tell me your size”. Ringin din wayarta ne yayi saving din ta daga embarrassing situation data shiga. Tana dubawa taga number Fatu. Wata ajiyar zuciyar ta saki da ta tuno mastalar da take ciki. Ta fara mata zolaya, ta tsai da ita ta kuma juya harshenta cikin larabci tace “ke ki tsaya akwai matsala”. Daga can ta amsa mata “wacce irin matsala me ya faru ina fatan ba ke da bala bane”. “ni da shine mana. Ya kawo ni sayen kaya yanzu muna shagon undies yake tambayata size din na. Kin san kuma kullum kwance ake bani saboda haka lambar duk ta koke ban san size din ta ba. Ni kuma kunya nake ji in sanar da shi hakan. Kuma kin ga na gwanjo ma da muke saye suma ba lamba a jikinsu. Ban san yadda zan yi ba”. Dariya tayi sosai san nan tace “na tuna size dinki kin tuna a lefen kawarmu Salma da aka baki. Ki ka ce baki taba jin dadin saka ta irin ranar ba saboda kin samu perfect size dinki”. “Wai Allah na gode maka. Size nawa ne”? “kice masa 38B’. “Shi ke nan na gode zan kira ki idan na koma gida”. Tana juyowa suka hada ido da shi ta saki murmushin wanda ya katse lokacin da ta ji muryarsa cikin larabci yana fadin “da ma baki tona mana asiri wajen Fatu ba. Mu shiga fitting room in gwada miki da kaina”. Da sauri ta juya zata fita daga shagon saboda tsananin kunya data kamata. Dankota yayi yana kokarin tura ta cikin fitting room din wanda ke kusa da su. “ka yi hakuri zan fada da kaina”. Yana mata cakulkulin wasa yake fadin “zaki kara gulmata da wani yare”? Ita kuma tana dariya tana fadin “a’a kayi hakuri ba zan kara ba”. Haka dai a shiririce kamar wasu kananan yara suna tafe suna wasa a haka aka gama shopping din. A wajen sayen takalmi kuwa shi ya tsuguna a kasa kusa da ita. Duk takalamin da aka kawo ya dora kafarta akan cinyarsa ya gwada idan ya ga yayi masa su saya. Amma fa sun saya da yawa. Domin yadda take da karuwan jiki haka take da karuwar kafa. Duk wanda aka sa sai kaga yayi mata kyau. Har mai shagon ya tambaye shi da turanci saboda ya naji akan wai ita din model ce. “yeh a very expensive one. But only I get to see her in her modelling outfit”. Ya amsa masa. Farkon zuwanta har mamaki take ita kanta da yadda mutane ke tanka kyawunta. Ga shi dai a cikin after dress take, amma hakan bai hana kyawun ta fitowa ba. Shi da kansa in ya zauna ya dinga mata kirari ke nan. Ya kalleta ya ce “my beautiful princess. Elegant while covered, appealing idan ta sauke abaya, idan kuwa a ka zarce haka, you drive me crazy”. Sai da suka huta suna cin abinci tace “yanzu sabo da Allah ashe ka iya larabci amma kana jin mu ni da Fatu kaki nuna mana. Da ma zaginka muka yi fa ai da ka bar mu da jin kunya”. “haba putri kin kasa gaya min kina sona, sai kuma na yi sa’a kin iya gayawa wata da harshen da kike tsammani banji, and you expect me to disclose my secret no way. Yau ma sa’a kika ci. Maza ku canja wani yare mu gani ke da ita”. “a’ai an gama wan nan game din”. Bayan sun kwanta da daddare yake shaida mata gobe zai fita da wuri kuma zai dade a factory. Bayan ya fita ta dauki sugar da lemon tsamin ta ta dafa ta saka a fridge yayi sanyi, saboda tana son yin halawa. Sai da ta shiga sauna bath din da ke bandakin gidan ta turara kanta san nan ta fito bayan ta goge danshin turiri ta fara dana wa jikinta halawa nan tana fizgewa. Sai da kuwa ta dauke duk wani gashi dake jikinta banda na gira da kai. Bayan nan ta dauko dilka cream da ta sayo a shagon larabawan nan ta muttsike jikinta da shi. Duk bata fi tara na safe ba ta gama da wan nan. Sai ta dakko sole tape din data yanka jiya da daddare akan chopping bord dinta. Sai da ta saki murmushi da ta tuna yadda ya dameta da tambayar me zata yi da razor da sole tape da ya ga tana masa wani yanka kamar bille. Murmushi kawai tayi bata ba shi amsa ba. Na kafarta ta fara sakawa san na ta dawo hannu ta saka wanda tayi wa yankan hula daidai saman faratunta na hannu, da ga nan kuma ta nada shi siri siri kamar spring. Shi ma ta yabe da lalle Ta sa leda tadaure ko ina saboda kar yayi saurin bushewa. Barcci tayi ba ta farka ba sai bayan uku. Ta cire lallen wanda tun daga saudiyya tayi dakonsa shi da mahallabiyar da ta sa masa. Dau kuwa ya kama. Hakan ya dada fito da asirin kyawun hannaye da kafafun nata. Lokacin data shiga wanka kuwa saboda santsi da jikinta yake yi, haka nan ruwa ya dinga gangarewa daga jikinta. Tana idar da sallah ta tsantsara kwalliya da daya daga cikin kayan da suka sayo. Dogon wando jeans da kuma T-Shirt wacce ta dada kawata mata figure dinta. Bai shigo ba sai bayan magariba, tana zauna a kujera ta dora kafarta kan center table tana kallon TV. Yana bude kofar cike da gajiya yaji ya wattsake saboda arba da yayi da wata jar kafa da aka yi wa wani rodi rodi kamar kwale. Sakin jakarsa yayi ya dumfare ta. Dagota yayi tana rike a hannunsa yana juyata saboda ya karewa kwalliyarta kallo. “woh! My putri gaskiya kin biya ni. Nawa za a caji wan nan kwalliya haka”? “idan ka bani kyautar zuciyarka, ka biya ni”. “kin dade da samun wan nan putri, nemi wani abu daban”. Da kyar ta lallaba shi yayi wanka sukaci abinci. Ko shi abincin akan kafarsa ya dora ta yana feeding dinta. Lokacin da suka je bacci kuwa sai da ya kusa zaucewa saboda santsin jikinta kawai. Allah ya sani zainab tana tsananin alfahari da kaunar da Al Bashir ke nuna mata. Bata taba sanin somebody can give so much love ba sai a wajensa. Sai da suka dauki wata biyua China ya samu ya rage ayyukan gabansa, san nan suka biya ta England can ma dai dan wani abin na sana’arsa ya dai daita. Suka shiga Turkey suka kwana biyu, san nan suka yada Zango a Dubai. Wanda suka yi kwana goma kacal. Sama da wata uku ba sa Nigeria, san nan suka dawo gida. Ba wani ba ita kanta idan ta kalli madubi bata yarda itace saboda wani irin beuty data kara, balle shi uban gayyar da ko barci take birge shi take yi. Driver ne ya dauko su daga airport inda bai ajiye su ko ina ba sai gidan su Al Bashir. Amma maimakon su shiga gate din main house sai taga sun shiga a smaller version of the main house. Duk da bata kwana a gidan ba, amma she has a good memory of the environment. Inda gidan yake yayi kama da filin da aka yi yinin bikinta. Ganin kamar tana tunani, ya saka shi cewa “sorry putri I remember cewa kin ce zaki iya zama da mamana shi yasa na gina gida gefenta, because having the two of you very close to me zai sani in kasance cikin farin ciki, amma ba zan takura ki if you have any reservation sai mu canza waje”? A dage ta juyo ta kalleshi. San nan tace “ashe kai har zaka ga darajar matar da zata ki zama da mahaifiyarka. Ni Ya Bala ne alkawari muka yi zai ajiye ni kusa da ummansa. Idan nayi laifi tayi min fada. Idan na kuskure ta gyara min. ni kuma in dinga binta sau da kafa ina mata ladabi da kuma koyon lamuran rayuwa a wajenta, saboda ko ba komai ta zama role model a idona ko don Haifa min mijin mai cike da tarbiyya da halin kwarai da tayi”. Ganin driver ne kawai ya hana shi rungomata jikinsa. Itace ta ce da driver “mu fara shiga main haouse tukunna”. Ai kuwa su Umma na jin takun motarsu duk suka fito ita da yayyensa gaba daya cikn murna, sai fadi take “ga bakin China sun dawo. Kuma dan uwana ba sai ku karasa da ita gida ba ta huta tukunna”. “umma is not my fault ita ta fada akan sai tashigo nan san nan zata gida”. Nan dai aka zauna gaisuwa ta musamman. Ruwa kawai umma ta barsu suka sha a wajenta ta kora su gida. Sai da hawaye ya zubo a fuskar Zainab da taga dankareren gidan da wai nata ne. Dan wani zaure suka shiga daga tsakiya, wanda ta nan kofa biyu ce daya ta shiga dakin baki da toilet dinsa, mai kallonta kuma ta shiga wargajejen falon da ke hade