← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 9 OF 43

Sashe 9

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Ibrahim a hargitse ya isa gida, yana dai-dai ta parking ya fita da sauri ya nufi sashin Mom d'in sa.
ganin yadda ya fad'o cikin parlour da sauri ta tare shi tana fad'in
"Son lafiya me ya faru mene ne!?."
a binka da d'an gatan da bai saba shiga damuwa ba ya labarta mata abinda ke faruwa cikin matukar damuwa.
Mom d'in sa ta waro ido ta ce
"Wlh karya ne bazai yiwuba dole a wanke zargin da aka maka a gaban kotu, daga zuwa niman aure dan baza'a baka ba sai a bika da mummunar kazafi,
to wlh bazan lamunta ba sai mun d'au mataki."
ta d'aga waya ta kira lambar Dad d'in sa ta sanar masa abin da ke faruwa.
baya kasar amma yace sabo da faruwar haka zai dawo, dan ya ce bazai lamunce wulakanci da tozarci kan d'ansa d'aya tilo ba.
amma da jin ko a wani gida lamarin ya faru ya ce
bazai dawo ba amma zai nimi Alhaji Abubakar d'in da kansa,
dan yana ganin mutuncinsa dan yasan shi mutum ne mai mutunci.
nan da nan ya nimi Daddy a waya, Daddy yana hanyar dawowa gida daga office kiran Dad d'in Ibrahim ya shigo wayarsa.

Umma Karima najin shigowar Daddy, ta nufi sashin Mommy da sauri, tana shiga ta isketa a parlour tun kafin ta karaso take fad'in
"Hajiya Halima taso maza muje naji shigowar Alhaji kafin wancan makiran matar can tasa,
ta rigamu zuwa ta je ta kitsa masa makirci yahau ya zauna a kai,
gara a yi ta ta kare yau 'yar nan ta bar gidan nan,
badun Hajiya bata gari ba, ai da anyi ruwa an d'auke."
"Ai kuwa maza muje dan ni tun da nake ban tab'a ganin makirarriya irin Hajiya Fatima ba,
tagama da Alhaji gaba d'aya wlh ji nake kamar ta mutu na huta."
"Hm kyale munafukar can taurin rai gare ta amma ajuri zuwa rafi saura kiris tulu ya tarwatse."
cewar Umma Karima tana jinjina kai.
suka fita suka nufi sashin Daddy.

Daddy na zaune a parlour'n sa dan da ya shigo a parlour ya zauna bai shige ciki ba.
har suka shigo suka sami guri suka sauna bai d'ago ba yana abinda yake yi.
suka had'a baki sukayi masa sannu da dawo wa, ya amsa, batare da ya d'ago ba.
Umma Karima ta d'an tab'a Mommy tayi mata alamar ta fara magana.
Mommy ta gyara zama tare da fad'in
"Alhaji mun zo gurin ka ne, yanzu fisabilillahi Kai kaji ka amince 'ya'yan ka su zamo tambad'ad'd'u ta sanadiyyar 'yar da ba'a san asalinta ba ma,
bafa zai yuwu ba yazama dole a kawo karshen lamarin,
iskancin yarinyar nan ya tashi a waje ya dawo har cikin gida kana sane kayi shiru,
bari Hajiya ta dawo dan wlh mu bazamu zuba ido muna gani tarika shigo mana da 'yan'iska cikin gida,
ga 'ya'yan mu mata suna cikin gidan ba."

Umma Karima ta ce
"Ato gaya masa dai,
yarinya tasan ta rika kawo 'yan'iska cikin gida suna iskanci ai abin nata ya girmama ya kai makura,
da idanuna na gansu a tsaye a bakin get d'in sashin Hajiya Fatima, ya shige cikin hijabinta suna shagalin su,
ni tun da nake ban tab'a ganin tambad'ad'd'iya irin aljanar yarinyar can ba."

Daddy ya d'ago yana dubansu rai b'ace,
ya nuna Umma Karima tare da fad'in
"Sai da nayi sammanin daga gurin ki maganar nan zai fito, da Alhaji Shitu Abdu ya sanar min,
ke Hajiya Karima ki kiyaye ni wai me ke damun ki ne kam Hajiya Karima?
kin san waye Alhaji Shitu Abdu kuwa?
to bari kiji taken sa mai kud'in shari'a, ba'a tab'a takasa a share lafiya sai ya yi shari'a da koma waye,
me ya kaiki shiga lamarin sa ina ruwanki;
badun yana ganin mutuncina ba da yanzu kinji sammaci daga kotu,
idan kiyi wa Fad'imatu kin share, ko ince ni tunda Feeryal a gurina take nine ubanta,
to Alhaji Shitu Abdu bazai jure tozarta masa d'a ba,
ki dawo hankalin ki nagaya miki ke nan!."
Daddy ya mike rai b'ace ya kwashi wayoyin sa ya nufi bedroom yana cigaba da fad'a.

Umma Karima ta d'a murya ta nad'e taburman kunyarta da bori
"Eh da ma ai zaka ce haka tun da ni mai jinin kule ne, yazo ya yi sammaci na mana muzuba mugani da ni da shi wazai fad'i a shari'ar,
in shi mai kud'in shari'a ne ni mai bakin kare kai ne,
haka kawai ga gaskiya muraran a nimi rufa gaskiya da bayan hanu."
ta mike fuu ta bar parlour'n.
ta bar Mommy nan zaune dan dama ita ce da Daddy.

Koda Umma Karima ta fito zata koma sashin ta can ta hango,
motar Abdurrahim da shigowar sa ke nan yana kokarin gyara parking a babban parking lot.
ta karaso, dai-dai sanda ya fito daga motar ya maida marfin motar ya rufe,
waya na rike a hannunsa yana kokarin tura kira.
ta ce
"Sannu da dawowa Abdurrahim ya aikin dai."
"Alhamdulillah."
ya fad'a a takai ce yana kokarin barin gurin.

Umma Karima tayi saurin fad'in
"Da ma yanzu nake shirin kiranka idan na koma ciki,
na ce da kai idan ka dawo kazo ina niman ka."
bai yi magana ba sai kiran da ya katse yana son jin abin da ke tafe da ita.
ganin hakan ya sata fad'in
"Abdurrahim ace kana cikin gidan nan, abubuwa da yawa suna ta faruwa a matsayin ka na babba a gida, kana ji baka d'au wani mataki ba,
a kaf gidan nan fa daga alhaji sai kai,
ko kannensa Alhaji Sulaiman da alhaji Tukur sai dai su biyo bayan ka su jira umurnin ka,
dan kaine Alhaji karami.
amma ace sanannen gida kamar wannan a aje tukururuwar karuwa aciki tana d'ebo 'yan'iska tana shigo wa da su har cikin gidan nan,
ba'a taka mata burki ba;
ai ko dan gudun gurb'acewar kannen ka zakayi wani abu, kafin ta kai ga lalata musu rayuwarsu suma,
wannan yarinyar da Hajiya Fatima ta tsinto annoba ce a gidan nan,
sam ba yar arziki bace irin tambad'ad'd'un aljanun nan ne,
haka shekaran jiyan can ta ja su Ameerah ta kaisu gurin party, haka ta tsaya a bainin nasi tana rungume rungume da maza,
ga video a wayan Ameerah kowa ya gani iskanci muraran,
yau har gida abokin iskancin nata ya biyo ta,
aka kamasu hanu da hanu,
haba ina amfanin sa abin nata ya yi yawa."

"To ni meye matsala ta da hakan Hajiya Karima?
ki sanarwa Aunty'n da ta kawo ta mana, inaga zai fi."
ya yi maganar yana picking na call d'in da ya shigo wayar sa,
ya kai wayar kunne ya fice a parking lot d'in.

Umma Karima ta bi bayansa da mugun kallo a fili ta ke fad'in
"Wannan d'an iskan yaro har gobe bazai canza halinsa ba,
in banda tsabar rashin daraja,
ni da na zauna shekara da shekaru da uban sa da Hajiya Karima ya ke kirana, sai wancan juyar yake kira da Aunty,
a sannu duk zaku dawo karkashin ikona kai da uban naka."
tayi kwafa a fili, ta juya ta nufi b'angaren ta.

Har ya d'au hanyar sashin sa sai kuma ya juya ya nufi b'angaren Mommy.
a bakin kofar parlour ya tsaya, su Ameerah da Sumayya suna zaune cikin parlour'n ko wannen su da waya a hannunsa suna chatting.
suna ganin sa kowa ya shiga taitayin sa, duk suka aje wayoyon suka shiga gaishesa.
batare da ya amsa gaisuwar tasu ba ya dubi Ameerah fuska a murtuke ya ce
"D'auko wayar ki ki zo nan!."
da sauri ta mike ta d'au wayar ta tako gabansa kirjinta na dukan tara-tara
hannun ta na rawa ta mika masa.
ya amsa tare da kuma tamke fuska ya daddana zuwa can ya d'ago tare da nuna mata screen d'in wayar ya ce
"Uwar me kika ajiye sa kike yi da shi a wayar baki goge ba?."
da sauri tayi kasa da kanta tashiga kame-kame dan irin kallon da yake jifan ta da shi tasan babu ko shakka zata iya samin tsarabar duka.
da sauri ta ce
"Dama..dama.ban..bansan yana nan ba nayi zaton na goge tun ranar."
wani mugun kallo ya wurga mata ta kuma shiga taitayin ta da kyau.
ya mai da idanunsa kan wayar kana ya d'ago ya ce
"Ina video yake?."
da sauri ta d'ago ya tsare ta da ido, baki na b'ari ta ce
"Babu wani video hoto ne kawai."
ganin yadda ya tsare ta da ido murya na rawa ta soma rantse-rantse
"Wlh Ya Abdurrahim iya hoto ne kawai na rantse da Allah babu video kuma ka duba ka gani ma."
bai kuma magana ba sai idon da ya tsare ta da shi.
cikin dakika guda ya karanto iya gaskiyar take gaya masa.
wayar ya wurga mata kad'an ya fad'i kasa tayi saurin taro sa,
ya nuna ta da yatsa tare da kad'a yatsar yana mai taune gefen lips d'in sa alamun gargad'i,
kana ya juya ya fita.

Sumayya da ke zaune cikin ta ya d'ura ruwa.
tana ganin fitarsa ta mike da sauri ta na fad'in
"Ina ga irin ta ina kinga abinda nake guje miki,
hoto kawai kika d'auka a kaci ubanki da duka ina kuma ga kin yad'ashi wa media,
ai wlh da baki da wata mafita gun Ya Abdurrahim zai ce dama aikin ki ke nan, yad'a hotunan bad'ala;
Allah ya taimake ki."
Ameerah ta dalla mata harara tana cewa
"Ke nifa bana son munafurci ina ruwan ki, ai na rantse bazan kyale yarinyar nan ba sai nasa an mata dukan tsiya shegiya mai idon mayu,
ai tun da aka bige ni a kan laifin ta wlh itama sai ta sha duka."
"To Allah ya taimake ki Ameerah ni dai in zaki bi ta tawa da kinyi hakuri kawai."
"Anki a bi takin Sumayya ke nifa bana son shishigi."
Sumayya ta juya ta nufi bedroom d'in su tana fad'in
"Kar ki fasa Ameerah."
cikin d'aga murya Ameerah ta ce
"Ai dama bazan fasa ba, na rantse sai ta duku."
Sumayya bata kuma bi ta kanta ba ta shige bedroom abinta dan tasan halin ta sarai yanzu sai ta huce fushin goge hoton da yayan nasu ya yi a kanta.
Chapter 9 · 0% Book details