← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 39 OF 43

Sashe 39

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read

Ganin ya kashe wayar Dr L-cana ya d'aga kafad'a tun da ya yi ko oho da maganar shiko yana ganin kud'i bazai barsu ba, komai ya faru ma daga baya ne.
ya koma ciki yasata ta tube ta haye gado.
ya had'o kayan aikin sa batare da b'ata lokaci ba ya burge cikin. ya bata magunguna suka nufo gida.
suna isa gida Umma Karima ta jata d'aki ta sunkiya mata bala'i.
"So kike ki samu a bakin mutanen gidan nan, badun na ankara da wuri ba ai da zance ya kwab'e,
idan mutane suka sani har ya shiga kunnen Abdurrahim ai shike nan kuma, sai mun nimi yadda zamuyi mu rufa bakin sa,
kar ki kara irin wannan ganganci;
ki cigaba da shan magani ki warke ko su Bilkisu kar ki bari su gane komai."
tayi waje tana janyo mata kofar.

A b'angaren Abdurrahim bakin cikin kiran da Dr L-cana ya yi masa akan Siyama da Umma Karima,
an danganta shi da su da abun bakin cikin da sukaje yi yaji,
ya tattari abubuwan amfanin sa yazari makullin motar sa yabar asibitin.
yana isa gida ya gyra parking yafito ya nufi side d'in sa.
direct upstairs bedroom d'in sa ya nufa.
yana tura kofar yaja ya tsaya cike da mamaki yaji b'acin ransa ya karo.
masu aiki yagani guda biyu cikin d'akin,
d'aya tana d'ale a kan gadon sa tana gyarawa d'ayan kuma tana cikin bathroom d'in sa
tana wankewa.
wani uban tsaya ya buga musu, a razane duk suka taho gaban sa suka zube.
cikin muryar b'acin rai sosai ya ce
"Waya baku damar shigo min side d'ina har ku wuce ko ina ku shigo min har cikin bedroom!?."
murya na rawa suka ce
"Mai d'akin ka ce Hajiya Kuraiba."
wani b'acin ran yakuma jin ya ziyarce sa.
cikin tsawa ya ce
"Ku fita ku b'ace min da gani! ko da wasa na sake ganin wata ta sako kafarta cikin side d'in nan ba ma d'akin nan ba, wlh sai kun raina kanku."
a zabure sukayi waje jiki na kyarma. a stairs sukayi kiliya da Kuraiba da taji dawowarsa ta shigo gefen sa.
ganin yadda suke sauka kamar ana biyo su ta ce
"Kai wai har kun gama gyaran ko ya?."
basu iya bata amsaba sukayi waje da gudu."
da sauri ta karasa haurawa tana shiga ta gansa yana tsaye yana rage kayan jikin sa, fuskarsa babu annuri.
ta karaso tana kokarin rungume sa ya buga mata tsawa tare da nunata da yatsa
murya cike da b'acin rai ya ce
"Waya baki ikon shigo min da wad'an can abin cikin d'aki, ke kanki albarkacin Mommy kike ci, badun haka ba na rantse baki isa ki taka kafarki cikin bedroom d'in nan ba, gargad'i na karshe,
kada ki sake ki sake gayyato min wasu 'yan'aiki cikin side d'innan ma gaba d'aya."
duk da taji tsoron yadda yake magana cikin fusata sosai, amma sai ta waske cike da salon bariki ta narke murya
"Haba mijin Kuraiba ai yanzu ni nake da ikon sawa ko hanawa a cikin gida na,
wai kullun ina gidan amma wai sai Ajmaal ya shigo ya gyara maka bedroom's zuwa parlour,
shine yau na ce yabari ni zan sa masu aiki su gyara idan sun gama gyaran nawa."
wani irin mari ya d'auke ta dashi tun kan ta kaiga rufe bakin
ta.
cikin karaji ya ce
"Bakiji me nace bane!?
masu aikin ne bana so su tab'a komai nawa, idan kika sake gigin gayyato su nan wallahi! sai kin raina kanki,
akwai kofa ta can sakanin inda kike da waje ki bud'e surika shigo miki ta can, ban yadda na gansu a area'n nan ba!
fita a d'akin nan yanzun nan!!."
yakuma buga mata tsawa, ta juyo da sauri dafe da fuska tayi waje tana fad'in
"Ka mare ni Abdurrahim."
tsaki yaja ya shige bathroom.

Yana fita ya tarar da Missed call d'in Mommy a wayar sa.
yana saka kaya ya fita ya tafi sashin Hajiya.
Hajiya na ganin sa ta ce
"Yauwa abikin turawa da ma yanzu nake kan cewa Kulu ta kira min kai,
ciwon gwuiwan nan ya sako ni gaba kwana biyu."
zama ya yi yana fad'in
"Muga kafar."
ta ja zani saman gwuiwar tana cewa
"Ka ganshi nan zugi kamar ya kwana biyu hanani bacci yake, yanzu ko na sha na shafa maganin da ka banin nan baya dai na zugin."
yatsar sa ya d'aura kan gwuiwar yana d'an daddannashi sannan ya d'ago ya gyara zaman sa ya ce
"Za'a canza miki magani, anjima zan kawo miki."
"Yauwa ai gara a kawo min wani, wannan gwuiwa ya sako ni gaba."
bai kuma magana ba sai wayarsa daya zaro yana daddannawa.
Hajiya ta gyara zama ta dube shi tana rike hab'a tare da fad'in
"Wai ni kam abokin turawa har yanzu banji
ana fad'in yarinyar nan Kuraiba ta d'auki ciki ba, ko baku fad'a bane? to ai ko baku fad'a bama za'aga alamar ciki tare da ita,
akwai cikin kuwa?."
baki ya tab'e batare da ya ce komai ba.
Hajiya ta ce
"Ni halina da kai ke nan, ana ma magana kayi banza da mutane, gara ka fad'a tun da wuri a sani a nemo maganin tsari a sunkuya bata,
dan gidan nan yanzu ya zama abun da ya zama miyagu suna son kafa sansanin su,
ban san me ke damin Abubakar ba wannan yarinyar Feeryal ba abin a zauna da ita a guri bane,
bari zanyi tattaki naje Yelwa na karb'o mata magani a rufa idon makiya akan abun cikin,
idan ta bar gidan ba shike nan ba kowa ma ya huta, wannan karo ko ba'a gama bincike ba zata koma,
iya shegen banza kawai ina gashi nan ni ina ganin ku ina jin dad'i,
shine bazai so ganin jikokin sa ba, idan aka barta tayi wa cikin wani abu fa tun da su dama jinnu sunfi son karnin jini,
kafin a sake samin wani ai sai an kuma yin wani watannin,
ba gara a tare ko mai tun da wuri ba, bari Abubakar zai zo ya same ni."
d'ago idon sa ya yi daga kallon waya ya kalle, wato ita a lissafin ta ciki Kuraiba take da shi.
baki ya tab'e ya mike yana fad'in
"Da ma tana da ciki ne?."
"Yo iyashegen banza ai kai kafi kowa sani in tana da shi ko babu, kardai kuyi irin abun zamanin nan aure kusan wata 6 ai yaci ace yanzu tana da cikin wata 5 ko shidan ma."
takalmansa ya zura ya fice
daga nan ya wuce masallaci...

Bayan wata biyu da cire cikin Siyama
Bilkisu da Saddiqa suna zaune a d'aki wanda dama su biyu d'akin su d'aya,
Rahma da Nabila suma d'akin su d'aya, Siyama nata daban.
Saddiqa da yawu ya cika mata baki ta mike taje ta zubar a toilet ta dawo.
jim kad'an ta kuma zuwa ta zubar.
ta kuma mikewa zataje zubarwa Bilkisu ta ce
"Ke dalla kin dami mutane da tofe-tofen yawu, wai ba dama mutum ya zauna kusa da ke sai yawu,
wani iskancin saran da kika samu kwana biyun nan ke nan, kibi ki ishi mutane da yawu da kakarin amai."
Bilkisu bata rufa baki ba Saddiqa ta kuma mike wa da gudu ta shige toilet tashiga kakarin amai.
Bilkisu ta mike tsaye ta taho bakin kofar toilet d'in ta ce
"Ke Saddiqa wai me ke damin ki, baki da lafiya ne bazaki fad'a a kira Family Dr ya zo ya duba ki,
ko kije ki gayawa Ya Abdurrahim ya baki magani ba."
Saddiqa ta mike tana kuma tofar da yawu.
Bilkisu ta harare ta tana kuma fad'in
"Wlh ni ni yanzu bamma yadda da ke ba, jiya maganar me kike sakan dare a waya,
duk da a bacci na tashi amma na fahimci akwai wani abun da kike b'oyewa."
ta juya da sauri tafita a d'akin ta nufi d'akin Umma Karima tana shiga ta ce
"Wallahi Umma ban yadda da Saddiqa ba, ki kirata ki binciketa wlh kamar ciki take da shi, tabi ta dame ni da amai da zubda miyau."
Umma Karima ta zabura tare da buga kirji ta ce
"Ciki! nashiga uku ina Saddiqa'n ta ke."
ta mike a haukace tayi waje tana kwad'awa Saddiqa kira.
Saddiqa ta fito da sauri jiki a sanyaye.
Umma Karima ta dubeta sama da kasa tana haki sannan ta ce
"Biyo ni nan maza ki bani fitsarin ki na gwada in dai ciki ne kin gama da ni Saddiqa."
Bilkisu Rahma Nabila Siyama duk suka rufa musu baya.
Kulu mai aikin Hajiya da tazo karb'awa Hajiya hayaki gun Umma Karima, taja ta tsaya tare da rike baki tana binsu da kallo har suka shige d'akin Umma Karima.
Chapter 39 · 0% Book details