← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 4 OF 43

Sashe 4

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read

Feeryal taware ido ta ce
"Zan iya kuwa abarshi kawai."
sukace zaki iya mana jikinshi kawai zai tab'a shikenan kin rama abunda yayi miki.
takarba tabude drower tasaka tadawo suka cigaba da hirar su.

Da sauri Umma Karima ta nufi sashin Mommy.
ta jata suka shige can kuryar d'aki.
Mommy ta dube ta tana zama bakin gado ta ce
"Allah dai yasa lafiya Hajiya Karima, irin wannan shigowa a bujajan haka."
"Inako lafiya Hajiya Halima, kwana uku boka Mali ya bani zai turo bakin aljani ya gama da waccan matsiyaciyar juyar,
kusan kwana goma ke nan nake zuba ido naji shiru,
ba na fad'a miki yadda mukayi da shi ba."
Mommy ta ce
"To ni ma dai har yanzu ban ga alamun hauka a jikin ta ba,
to ko watakila bai gama aikin bane,
amma kinsan maganar boka Mali baya fad'u kasa."
Umma Karima ta ce
"To ai nima shine na gani watakila bai gama aikin bane dan ya ce min aikin yana da wuya, sai anyiwa aljanin shiri,
kai nifa kinsan bana son jira da yawa, nafi son komai cikin gaggawa;
yau zan koma gurinsa kawai, naje naji mekefaruwa, in kina da aike ki kawo."
Mommy ta ce
"Ai kuwa ina da sako, batun auren yaron nan Abdurrahim da Kuraiba,
jiya na tsare shi da batun tun da ya dawo ayi-ayi-ayi auren nan,
mahaifiyar yarinyar nan kusan kullum sai ta kira ni,
'yar nan bata tab'a ganin sa ba sai a hoto amma ta ce taji ta gani sai shi,
Hajiya Luba ta ce kullum sai ta taso ta gaba itafa shi take so a aura mata shi kawai har kuka take a kansa;
amma yaron nan nayi ta binsa yaje gidan su yaki kin san sa da masifaffen taurin kai,
ki fad'awa boka Mali ya karkatar da hankalinsa yaje su dai-dai ta ayi auren nan."

Umma Karima taji wani dum a kirjinta amma sai ta waske ta yab'o murmushin yake a fuskarta ta ce
"Ai kuwa in banda Abdurrahim me yake jira da bazai yi aure ba, to amma fa kinsan sai kin kawo kafin alkalami kafin a fara aiki."
"Ah ai dama dole bari na baki wani abu ki bashi."
ta mike taja drower ta d'au dubu d'ari biyar ta mika mata ta ce
"A kai masa wannan idan ya ce da kari ba matsala za'a kara masa."
Umma Karima ta karb'a ta mike tana fad'in
"To bari naje duk yadda ake ciki zakiji."
ta fice ta koma sashinta ta shirya ta garzaya dajin boka Mali.

Umma Karima na zube a gaban boka
bayan ta gama sanar masa da rashin nasarar su,
har yanzu dai Hajiya Fatima na nan daram babu abin da ya same ta.
tana zaune ta kasa kunne tana jin jawaban boka Mali cikin b'acin rai yake fad'in
"Mun tura bakin aljani sai dai anyi rashin sa'a,
basuyi ido da ido da ita ba;
alamu na nuna mana wani ya haukace a madadin ta,
sai dai abin bakinciki tun ranar nake zuba idon ganin bakin aljani da kyakkyawan labari,
amma har yau bai waiwayo ni ba,
wannan yarinyar da take rukonta hatsabibiya ce nayi tason ganin ta cikin duban tsafi na kasa,
wannan yarinyar tana da had'ari dole sai ta kauce a gareta kafin a sami biyan bukata."
ta ce
"Boka babu yadda za'ayi a kawar da yarinyar ita?."
ya ce "Ke zakiyi hakan idan kikayi mukuma zamu karasa sauran aikin,
dan bama iya ganin ta a cikin duban tsafin mu."
Umma Karima ta jinjina kai da tunani iri-iri a ranta.

Umma Karima ce zaune a d'akinta ita da kanwarta Siyama,
washegarin da ta je gurin boka Mali.
ta sa Siyama tayi wanka ta shirya cikin wasu,
d'amammun kaya wanda ya bayyana surar jikinta gaba d'aya.
ta mikawa Siyama wani kwalli a cikin d'an tandu da kwalbar turare wanda boka Mali yabasu ta ce
"Saka wannan kwallin a idon ki, ki shafa turaren a fuskarki, kud'in aikin da ta bayar ayiwa d'an ta a kan wata shi na bada ayi a kanki zuwa kan d'anta,
Hajiya Halima ke nan har yanzu da sauran ki kar nake ganin ki,
kin haifi 'ya'ya maza, a yau Alhaji ya fad'i ya mutu kin mallake gidan,
tun da nayi-nayi ban samo d'a na miji ba,
to ki sani akan d'anki zan samo d'a na miji, daga nan kuma zance ya kare."
Siyama ta karb'i kwalbar turaren tana dariya ta shafa.
tana fad'in
"Sai dake Aunty na."
Umma Karima ta ce
"Yauwa to yanzu komai yayi dai-dai Abdurrahim yana ido biyu dake,
shikenan burinmu yacika yanzu iwar haka yananan a sashin Hajiya Halima;
jeki can in baki sameshiba ki garzaya sashinsa basaina gayamikiba ko me zakiyi kinsa meyakamata kiyi,
d'an ta zai shigo hannun mu reshe zai juya da mujiya."

Siyama tashige sashin mummy da sallama tana wani kararraya tazauna akan kujera inda ta taddasu Ameerah da Sumayya tagaida,
mummy data fito daga bedroom d'in ta.
Sumayya ta bita da kallo tana fad'in
"Irin wannan kwalliya haka Aunty Siyama, ina zuwa haka?."
"Kai Sumayya sai kace bana kwalli, babu inda zani."
Sumayya ta yi dariya ta ce
"Ai kwalliyar tayi kama da ta zuwa party ce."
Ameerah ta kallete ta da wutsiyar ido,
ta yamutsa fuska ta cigaba da dannan wayarta.
Siyama ta ce
"Wai Ameerah ba magana ne?."
Ameerah ta d'an d'ago ta ce
"Sorry hankali na na wani wajen."
Siyama tayi shiru da bakin ta dan ta san halin Ameerah sarai bata kyale kowa ba.
ta gyara zaman ta
tana d'an satan kallon gun bata dai ganshiba.
zuwa can ta mike ta fita.

Tana sako kanta zata fice daga parlour Mommy sukayi kicub'us da shi yana kokarin shigowa.
ta wani sake jiki tana wani yauki, ta narke murya
"Barka da warhaka yallab'oi, ina yini."
"Lafiya."
ya amsa a takaice
ko in da take bai kallaba ya rab'a gefen ta ya shige cikin parlour.
wani irin lumshe idanu tayi tare da jan numfashi ta na shakar daddad'an kamshin sa.
da sauri ta bud'e idanunta, ta taune baki tana dana sanin da ta fito da ta cigaba da zama har ya shigo.
da sauri ta juyo ta koma ciki a zaune ta ganshi gefen Mommy.
ta zo ta gaban shi ta wuce tans kad'a mazaunan ta,
ta zauna kusa da Sumayya kujeran da ke fuskantar sa,
Sumayya ta ce
"Aunty Siyama baki tafi ba ashe."
ta d'an saci kallon in da yake fatanta ya d'ago su had'a ido,
shiko baima san tana yi ba idonsa akan waya.
ta ce
"Am Sumayya dama aron wayarki zaki bani nakira tawa bansan ina na jefa ta."
Ameerah ta kalleta tana mara baki ta lura da satar kallon da take wa yayan nasu.
"Yar wahala."
ta fad'a a kasan ranta.

Sumayya ta ce
"Ina ma wayar tawa take."
ta waiga gefe da gefen ta
"Yauwa ga shi can."
ta nuna kujerar da Abdurrahim ke zaune gefen sa wayar take,
shigowar sa Sumayya ta tashi a kujerar ta bashi gurin zama kusa da Mommy.
Sumayya na kokarin mikewa ta d'auko mata, tarigata mikewa.
ta isa gurin ta kai hannu kamar zata d'au ka sai ta tura wayar ya da d'a matswa jikin sa.
ta saka hanu ta gogi jikin sa.
da sauri ya d'ago suka had'a ido, tawani narke murya
"Oh yihakuri waya zan d'auka."
gajeren tsaki yaja ya maida idanunsa kan waya.
da sauri ta juya cike da farincin burin ta ya cika, tad'an lallasa wayar kana ta mikawa Sumayyar wayarta ta ce
"Naji muryar Nabila wayar tana hannunta."
ta juya da sauri ta fita cike da farin ciki.

Tana komawa sashin su ta rungume Umma Karima tana fad'in
"Aunty Karima ya ganni na ganshi."
Umma Karima tayi makirin dariya ta ce
"An gama 'yar gari, kwantar da hankalin ki kin sami Abdurrahim a tafin hannunki."
suka wani kwashe da dariya suka tafa.

Mommy ta dubi Abdurrahim da tun shigowar sa daya gaisheta bai kuma magana ba, sai aikin danna wayarsa ya ke.
ta ce
"Kaje kun gaisa da Kuraiba'n kuwa?."
"Mommy abani breakfast."
ido ta bisa da shi sarai tasan so yake ya kawar da maganar nata.
ta ce "Ameerah je kice Shatu ta had'o masa breakfast."
"No ki barshi."
yafad'a tare da mike wa tsaye.
Mommy ta ce
"Ai nasan dama ba ci zakayi ba shiyasa ma ban sa an kaimaka ba,
ina tayi maka magar yarinyar nan baka cewa komai."
"Banje ba."
ya fad'a a takaice
Mommy ta ce
"Amma ai yakamata ace kaje, ko da sau d'aya ne ku gana, kafin akai sadaki."
ya zura takalman sa baiyi magana ba yafice.

Sashin Aunty ya nufa dan yasan can ne kawai zai sami abincin da zaici cikin kwanciyar hankali.
da sallama ya shigo Aunty na kokarin shiga kichin.
ta dakata ya karaso suka gaisa,
yanayin sa ya tabbatar mata da abinda ya kawo shi,
dan tasan gadon Daddy ne ajikin sa,
shima baya cin abincin masu aiki.
Aunty tayi murmushi ta ce
"Abdurrahim ka isa dinnin bari na kawo maka breakfast."
ta wuce kichin shi kuma ya kara dinnin ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in.
ta had'o masa breakfast mai rai da lafiya ta kawo masa.
kana ta koma kichin tacigaba da ayyukan ta.
Chapter 4 · 0% Book details