Sashe 29
Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read
Feeryal ce tafito daga bedroom d'in ta.
Aunty na zaune a parlour ta karaso ta tana kokarin zama Aunty ta kura mata ido da sauri ta ce
"Ina bra baki saba, koma kisa."
baki ta cuno ta langwab'ar da kai
"Ammie ban gani bane fa."
"Bra'n ne baki gani?."
kai ta gyad'a tana dad'a shagwab'e fuska.
Aunty ta mike tana fad'in
"Ni zan gani ai bari naje na nemo miki tun da sun b'ata."
ta biyo ta tana bubbuga kafa kasa
"Ammie duka wardrobe d'in fa babu."
"Ai shine nace ni zan nimo, tun da sun b'ata miki ni zan samo su."
tabi Ammie'n nata da sauri suka shige d'akin tana dariya da fad'in
"Ammie numfashi fa yake hanani."
"Ni dai a barni na nimo kawai tun da b'ata sukayi."
cewar Aunty
Aunty ta bud'e wardrobe ta rike baki tana kallon side d'in bra, tari guda har da sabbin da bata tab'a sawa ba.
ta ciro mata d'aya ta ce
"Gashi na samo miki daga in da suka b'atan,
maza karb'a ki saka."
ta na kokarin rufe wardrobe d'in ta hango laida, ta zaro shi tana cewa
"Mene ne acikin nan ko har laida aka nemo na b'oye su ciki."
ta yi maganar tana bud'e laidar
ganin pant da pat da riga a ciki ta zaro rigar tana kare masa kallo.
ido Feeryal ta waro ita sam tagama mancewa da rigar a gurin.
tun ranar da suka dawo ta jefashi duka da laidar cikin wardrobe ta mance da shi.
"Wannan rigar fa kamar ta maza ce ai wannan."
cewar Aunty tana duban ta.
"Laa namance na wannan ne daya bani a hotel d'in nan da suka yaga min kaya na saka."
"Wai na Abdurrahim ke kamma Feeryal akwai shiririta, shine tun washegari baki mayar masa da kayan sa ba,
to ai sai ki kai masa kayan sa kya aje a nan."
ta mika mata rigar.
"Kai masa yanzu ki dawo karb'i hijab ki saka."
ta miko mata hijab ta karb'a ta saka.
Aunty sai binta da kallo take tana murmushi,
tayi kyau sosai cikin hijab d'in tamkar balarabiyar asali.
Ido ta lumshe jin iskar waje ya bigeta.
tun ranar da ya citota ya dawo da ita gida, bata kuma sa kafa cikin gidan ba sai ya.
koda Miemie ta zo sunyi hira iyakar rakiyan ta da ita bakin kofar parlour.
hango get d'in su Miemie tayi tana lissafin taje ta kirata ta rakata ta kaimasa.
"Ko zai karb'a ma oho to amma ai jini bai tab'a masa rigaba ranar."
tayi maganar ita kad'ai.
ta sa kai tana shirin tafiya sashin su Miemie taji karar mota a bayan ta.
da sauri ta waigo tare da matsawa gefe.
motar tawuce.
batasan wa ke ciki ba dan gilashin motar mai duhu ce.
sai da ya wuce tasoma takawa a hankali.
a gaban side d'in su Ajmal motar ta tsaya.
Ajmal ya fito daga side d'in su ya zo jikin motar.
tazo daf da motar ganin Ajmal a gurin ta juyo tana shirin gaida shi, idanunta ya sauka kan nacikin motar.
idanunsa kan wasu files yana dubawa sannan ya mika wa Ajmal d'in.
shi kuma ya karb'a yana yiwa Feeryal murmushi.
itama ta maida masa a gajarce ya juya da sauri ya nufi parking lot yana gyara rikon files d'in.
Ganin shine a motar tashiga takowa a hankali zuciyarta na tsalle, a sannu ta karaso jikin motar kanta a sunkuye.
ta d'ago ta kalleshi,
idanunsa na kan wayar da yake dannawa,
tun ranar da ya taimake ta taji girmansa ya shinfid'u a ido da zuciyarta.
a hankali ta miko masa rigar cikin siririyar muryarta ta ce
"Nagode Sahab ga rigar."
yakai 1min kafin ya d'ago idanunsa ya sauka cikin nata.
"Sahab."
sunan da ta kira shi da shi ya nanata a ransa.
da sauri tayi kasa da kanta.
shiko ya yi wa motar key ganin haka yasa ta d'an matsa gefe yaja motarsa ya wuce sashinsa.
Kallon rigar tayi kana ta kalli bayan motar nashi, sai kuma ta juya.
dan dama ta sammaci haka daga gareshi,
tasan ba lallai ne ya karb'i rigar ba dama,
ko ya yi sammanin da jini a jikin wannan rigar ne shima.
rau-rau tayi da ido ta juya.....!
20
Tana daf da shiga side d'in Aunty tajiyo muryar Miemie tana kiranta.
ta juyo ta tsaya tanata murmushi.
Miemie ta karaso rike da yarinya a hannunta.
"Ina kika fito ne Feeryal, shine kin fito ko nimata bakiyi ba ko."
tab'e fuska tayi ta ce
"Wannan Sahab d'in ne na kai masa rigarsa da ranar ya bani, yauma yaki amsa."
"Ranar d'in ma jinin ya tab'a ne?."
kai ta girgiza.
"To ki ajiye idan kika kuma bashi bai karb'arb'a ba, sai ki bawa wani,
um ga motar Ya Faruoq can mijin Aunty Farida, yazo zasu tafi bari na kai mata 'yarta, ko zaki rakani?."
"Aa jike ina jiran ki anan."
"Dalla zo muje ke zaman guri d'ayan ma ko damin ki baya yi, kullum kina nanike a ciki, ni ina zan iya ai sai dai in ciwo nake, shima ina jin dama-dama bazan zauna ba zanyi waje na mike kafa,
d'an rike min ita na gyara."
Feeryal na karb'ar ta ta ce
"To muje."
Miemie tayi sauri tayi gaba.
Feeryal ta biyo ta tana fad'in
"Miemie ki karb'e ta dan Allah."
Miemie ta dad'a sauri tana dariya har suka karaso gurin motar Faruoq daya fito yana tsaye jikin motar.
"Ya Farouq ina yini."
cewar Miemie tana waigen Feeryal tana mata dariya.
ya amsa idanunsa akan Feeryal data kwab'e fuska kamar zatayi kuka.
hannu ya mika mata alamun ta miko masa 'yarsa da take ta tsallen ganin uban nata a hannunta.
ta miko masa ita tare da gaishe shi.
ya amsa idanunsa a kanta kana ya dubi Miemie ya ce
"Miemie dariyar zolaya ko, me kikayi mata take b'ata rai."
ta ce "Ni ban mata ko mai ba kwad'ayin kuka take ji, yanzu zakaga tana yi."
tayi maganar cike da zolaya tana kallon ta.
dariya ya yi yana cewa
"Au haka take da saurin kuka, to gaskiya ya kamata a sami mai rarrashi, meye sunan kyakkyar?."
Miemie ta ce
"Feeryal sunan ta."
kai ya jinjina yana cewa
"Sunan dai-dai da yanayi."
zai kuma magana Farida ta fito.
wani irin daramm taji ganin Feeryal a gaban mijinta idanunsa tarr a kanta yana ta mata dariya.
Miemie ta ce
"Aunty Farida ai Neezrah ko kuka batayi ba tana ta wasan ta, zan zo har gida na d'auke ta muzo mu wuni."
wani irin abu ta had'iye tamkar kayoyi a makoshinta, kai kawai ta iya gyad'awa Miemie ta bud'e mota ta shiga.
Farouq ya ce
"Anya kuwa Miemie ni dai a hannun Feeryal naga baby Neezrah ya tabbata dai ta iya raino ba ke ba."
ya yi maganar yana bud'e gefen direba har lau yana yiwa Feeryal murmushi.
Miemie ta bigi kafad'ar ta ganin tayi murmushi tace
"Hum wai har taji dad'i sai kace ita tayi rainon."
tafiya ta soma tana fad'in
"Ai nima nayi daga can zuwa nan."
Har suka fice a gidan Farida bata iya cewa komai ba tana zaune zuciyarta na tukuki.
tun a hanya Farouq ya ke ta kawo mata maganarta ya na cewa
yarinyar she is so cute completely.
hirarsa d'aya biyu sai ya sakota, har duka isa gida
bai fasa ba.
suna shiga parlour'n su ta kwab'e mayafinta tana haki da yadda take jin zuciyarta kamar zai yi bindiga.
Neezrah ya aje kan kujera yana fad'in
"Zauna 'yar rainon Feeryal ko gobe zakije gidan su ne, dan naga ke ma sai murna kike a gidan su."
cikin masifa da tafasar zuci ta ce
"Badai gidan su ba sai dai gidan mu dan ba gidan uban Feeryal bane can."
ta juya fuu ta shige d'aki.
murmushi ya yi dan bai kawo komai a ransa ba ya cigaba da yiwa 'yar sa wasa.
Da daddare har ya yi nisa a bacci ta tashe shi, dan ita takasa baccin, sabar masifar kishi.
ta bubbugashi tana fad'in
"Faruoq ta shi ka gaya min mene ne dalilin dayasa kake ta kawo min maganar mayyar aljanar yarinyar nan, tun a mota har a cikin gidan nan, wace munafurci kake kullawa cikin ranka."
ido ya bud'e cike da bacci ya ce
"Haba Farida a tsohon daren nan zaki tada ni da wani magana mara kan gado, babu ko Abba'n Neezrah ma yau to me zan gaya miki, me kuma zan b'oye miki cikin raina,
dan nayi maganar kanwarki shine wani abun tashin hankali."
"Dakata Faruoq ba kanwata ba karka sake had'a ni da ita, dan babu abun da ya had'ani da 'yar da ba'asan asalinta ba,
tsintacciyar cikin ruwa,
daga yau karka sake kawo min batun ta cikin gida har in kana son zaman lafiya a gidan nan."
janyo ta ya yi jikin sa ya ce
"To naji shike nan Sleep please bazan kara ba."
Farida bata iya bacci ba sabar yadda take
jin zuciyarta, kamar ana mata luguden tab'are.