← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 18 OF 43

Sashe 18

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Su Hajiyan Dubai da 'ya'yan ta Umaima da Unaisa, suma sun hallaro.
Kamar yadda Mommy ta fad'a satin aure za'a kai lefe,
aure na da sati guda ke nan su Hajiyan Dubai da wasu dangin Mommy da Daddy da kawayen Mommy suka kai lefe gidan amarya.
abun da ya yi mugun tadawa Siyama hankali ganin irin tulin
kayan da aka kaiwa Kuraiba.
a haukace ta shigo d'akin Umma Karima, Umma Karima tana zaune tana waya da bokan ta.
Siyama ta shiga kai kawo cikin d'akin ta kasa zama.
"Boka a maganar da nake maka saura sati d'aya fa bikin nan,
sai yaushe ne za'a wargaza auren aure saura kwana kad'an.
boka ka taimake ni kar kabari ayi auren nan."
"Maganar waya bazata yi ba kizo kiji binciken kaddarar ki."
"To to gani zuwa ni dai buri na naji daddad'an kaddadar bincike, dan Allah boka a zurfafa bincike, sai nazo."
Umma Karima ta sauke waya ta dubi Siyama tana fad'in
"Akan ido na aka fita da kayan nan bakin ciki ya hanani fita, ta turo nazo muje kai kaya nace ace mata yau na tashi da ciwon kai,
boka ya ce nazo ya yi bincike ya gano wani abu, zan je naji dan nasan bazai bamu kunya ba."
"Aunty Karima kin ga kayan kuwa ashe Hajiyan Dubai ta kuma zuwa da wasu, cikin mota uku fa aka tafi da shi, ban da wan da suka saka a sauran motocin da suka tafi."
"Ke duk wannan ba wani abu bane in zamu sami abun da muke so nawa ne wannan kayan da bai wuce kud'in shan shayi ba,
ki natsu cip zan je naji me boka zai ce."
Umma Karima ta mike ta zari mayafi ta fita.

Umma Karima zaune gaban boka Mali ba mayafi ba d'ankwali ba takalmi ta nad'e kafa kamar mai niman gafara.
boka Mali ya d'ago ya dube ta bayan yagama zane-zane da buga kasa ya ce
"Akwai yuwuwar yin auren nan babu yadda za'ayi dole sai anyi sa,
idan kuma aka matsa wajen hana yiwuwar sa to wasu aiyukan zasu iya rushewa, musamman aikin cikin tukunyar can shima zai iya tarwatsewa."
ta girgiza kai da sauri
"A'a boka bana son aikin can ya rushe zan iya hakura ayi auren, amma bazan iya jure rashin wancan aikin ba."
"Hahahaha kinyi nazari mai zurfi."
ta mike tana fad'in
"Yanzu boka babu wani d'an taimakon da za'a iya yimin,
amma dan Allah kar ya tab'a aikin can."
"Bazamu iya yin komai ba yanzu ki bari ayi auren."
"Nagode ubanmu maganin kukan mu idan ina bukatar wata taimako zan dawo dan kai ne kad'ai mai iya share min hawaye,
duk abin da na nima na samu in kana numfashi Allah ya kara tsoron rai."

Ta fice daga cikin kogon inda ko da yaushe take tub'e mayafi da d'ankwali da takalmin ta ta isa,
ta d'auka ta saka kana ta karasa gurin mota in da direban ta ke zaune cikin mota yana zaman jiranta.
ta bud'e gefen mai zaman banza ta shiga ta zauna sharap.
Liti direba ya dube ta yana fad'in
"Ina muka dosa hajjaju?."
gajeren tsaki ta ja ta ce
"Mu tafi hotel gaba d'aya yau raina a b'ace yake."
"An gama ranki shidad'e."
yaja motar suka nufi in da ta umurcesa..

"Feeryal yi sauri dan Allah mu tafi, idan fa bamu je mun zaunawa telan nan bafa ba bazai mana d'inki kan lokaci ba."
"Miemie wai dole kuma sai munje bayace zai kawo da kansa ba, mu jira mugani ko zaikawo anjima."
"Ke baki san halin teloli ba ne,
ba ga su Sahla sunje sun amso nasu jiya ba, kuma ai duk tare ya ce zai kawo mana, me yasa bai kawo mana ko ya basu su kawo mana ba,
muje kawai mu amso muma."
Feeryal ta mike tana gyara gyalen abayar jikin ta, ta saka takalmi mara tudu suka fito.

A can jikin get d'in side d'in Hajiya suka hangi Hajiyan Dubai da su Unaisa.
Miemie ta ce
"Taho muje Feeryal ga Hajiyan Dubai can yanzu sai tace mun ganta bamu zo mun gaishe ta ba, shegen son a gaishe ta matarnan ko me gaisuwar yake badawa oho mata."

Tun kafin su karaso Hajiyan Dubai ke bin Feeryal da kallo har suka karaso.
a tare suka had'a baki wajen gaishe ta ta amsa tana dad'a karewa Feeryal kallo
"Lafiya lau sannun ku."
har sun juya zasu tafi Hajiyan Dubai ta ce
"Ke Miemie a ina kika samo wannan, ko cikin ba'in Lebanon ne da suka iso."
"A'a Feeryal ce yarinyar Aunty."
"Wacce Aunty wai Hajiya Fatima, Aunty naku yaushe ne ta haihu bamu sani ba,
au kar dai ace 'yar da ta tsinto d'in nan ce."
Umaima da Unaisa da suke jingine jikin mota dukansu rike da waya suna latsawa,
da alama fita zasuyi da uwar tasu,
sai a lokacin suka d'ago suka kalli Feeryal.
Unaisa ta d'an yi murmushi
"Miemie sannun ki."
Miemie ma guntun murmushin tayi mata.
dan tasan halin su ko wannen su d'an ji da kai ne suna ganin sun fi kowa, suna rayuwa a Dubai.
ta ce "Sannun ku kuma Feeryal muje ko."
cewar Miemie tana jan hanun ta.
"Yanzu ke Miemie baki jin kishin kanki, kina yawo da wacce ta fiki,
taya za'ayi saurayi ya ganki ya ganta ya d'auke ki a kanta,
ni sam bana son yarinyar data fiye kyau haka tana huld'a da 'ya'ya na,
ita uwar taki ma bata san me take yi ba da ta zuba miki ido ta barki kuna yawo tare da ita."

Miemie bata ce kala ba ta ja Feeryal sukayi gaba, tamkar basuji me take fad'a ba.

Acikin mota ne Miemie ta dubi Feeryal da jikin ta ya d'an sanyi.
ta ce
"Hm matar nan fa duk bakin ciki ne ya dame ta, dan taga saura kad'an Ya Abdurrahim ya yi aure,
ai da ta so had'a shi da Umaima shi yaki."
Hmm kawai feeryal ta ce tana juya lamarin cikin ranta.

Ko da sukaje suka samu telen ya gama d'in kin su,
babban shago ne da ma'aikata da yawa,
har zasu tafi d'aya daga cikin telolon ya ce musu ga sauran kayan Ameerah su tafi mata da shi.
Miemie ta ce bazasu karb'a ba tazo da kanta ta karb'a,
ai suma da suka zo suka karb'i sauran kayan su basu karb'a musu nasu da aka gama ba.
Feeryal ce ta karb'i kayan suka nufo gida Miemie na ta mita.
"Yarinyar da ba a yi mata gwanin ta ba burgeta zakiyi ba."
"Nima ba so nake na burge ta ba, kawai taimako nayi yiyyar yi mata."
Miemie ta yamutsa fuska.

Suna isa gida Miemie ta dubi Feeryal tana cewa
"To ai sai ki kai mata tun da wulakanci bai ishe ki ba dan ni dai bazan kai ba."
"Ni ma ba zuwa zanyi ba zan dai baiwa masu aiki su kai mata."
tana rufa baki suka hango ta ita da su Unaisa da Umaima Sahla Nabila Sumayya, sun fito daga sashin Hajiya.
"Muje daga nan ki mika mata mu wuce."
suna zuwa sashin Mommy su suna tafiya sashin Aunty a tsakiya suka had'e.

Sumayya ta ce
"Yauwa Miemie Hajiya ta na niman ki."
"To daga gun d'inki nake sai na je na ajiye kayana kafin naje, me zata min ma tukun."
Sahla ta ce
"Ina zamu sani mu, yauwa ya gama miki d'inkin duka kuwa?
mu ma can zamuje mu amso sauran kayan Ameerah."
"Ya gama duka har da na Feeryal, d'in ki ya zuba kyau sai kowa ya saka a tantance,
Feeryal mika mata kayan ta, gashi nan ta karb'a mata."
laidar kayan Feeryal ta mikawa Ameerah da tayi gum da bakin ta kowa yana magana ita bakin ta a suke kamar ruwa ya shanye ta.
sai cika da basewar da take ita fa a dole boss ce a cikin su.
ta amshi laidar har lau bata ce kala ba ta soma tafiya.
Unaisa ta dubi Feeryal ba yabo ba fallasa ta ce
"Feeryal sunan ko ba laifi kam akwai kyau."
takaotaccen murmushi tayi mata.
Nabila ta ce
"Mujen ku dan Allah."
suka bi bayan Ameerah suka nufi sashin Mommy.

Miemie ta juya tana kallon bayan su, dariya ta tuntsure da shi tana cewa
"D'an iska na kauye sai tsoron d'an'sanda, dubi Ameerah yadda ta nutsu,
karyar iskanci take,
duk shan kwayar ka ai akwai wanda ya d'are ka,
gargad'in ya shige ta ke nan."
Feeryal ta bita da ido dan bata fahimci abin da take nufi ba..

Ana saura kwana uku biki Farida da mijin ta suka duro Nigeria da baby girl d'in su mai suna Neezrah.
sun kuma dawo akan dai-dai kab'ar da mijin nata ya kammala aikin da ya ajiye shi a Uk.
gida ya cika makil da 'yan'uwa da abokan arziki.
in da tuni sabbin ma'aikatan da Mommy ta d'ibo damin bikin suka had'e dana gidan suka cigaba da d'aura manyan tukwane suna sauke wa.

Dr Imran ne ya shigo bedroom d'in Abdurrahim cikin shigar sabbin kaya masu kyau.
tsayuwa ya yi cikin d'akin yana binsa da kallon mamaki ganin sa kwance, yana baccin sa cikin kwanciyar hankali.

Da sauri ya karaso bakin gadon yashiga bubbugashi yana fad'in
"A.A wai bacci ka wanta yi a wannan lokaci?
ai kai da bacci sai bayan biki, dalla tashi ga ba ba'i can suna jiran ka."
tsaki ya ja
"Wai meye haka ne kam Imran ina ruwan ka da bacci na."
"Da ruwa na mana taya za'ayi ma ka kwanta bacci ne kam, to ko ni nan tun baccin jiya da daddare da na tashi da asuba ban kuma komawa ba har yanzu,
bare kuma kai uban gayyar da kanka,
mutanen Germany fa sun iso gana Abuja ma,
ko wanne nasa an musu masauki a hotel daban daban,
ya kamata ka tashi kaje ku gaisa dan kai fa sukayi tattaki suka zo,
musamman ma wad'an da suka taho daga wata kasar."
Chapter 18 · 0% Book details