← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 19 OF 43

Sashe 19

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Kwafa ya yi tare da mike wa zaune yana aikawa Dr Imran mugun kallo
"Amma nace ban yarda ka gayyaci ko wanne daga cikin su ba ko."
"Au da so kake sai dai suji kayi aure, haba su da kullum suke maganar Allah ya kaisu ranar auren ka,
nasan suna yi maka fatan kar ka mutu tuzuru ne,
suma jajayen fata sukayi aure a kan lokaci bare kai da ka fisu kwari da lafiya,
taso kaje kayi wanka ka shirya da'alla mu tafi,
kar ka mance dai 8:30 na dare akwai kamu kuma kasan dole zamu je."

Tsaki yaja ya mike ya nufi bathroom yana fad'in
"Ai sai ka jani ka kai ni."

Kafin ya fito Dr Imran ya zab'ar masa kaya cikin sababbi kuma tsadaddun d'inkunan da Daddy ya yi masa.
ya feshe su da turaruka masu dad'i da sanyin kamshi.
ya d'auko hula da takalmin da zasu shiga da kayan suma duk sababbi ne, ya aje masa su kusa.
yana fitowa ya ce
"Yauwa yi maza ka hanzarta ga kayan da zaka saka."
baiyi magana ba sai hararar sa da yayi.
ya wuce gaban mirror ya zauna ya d'au Body lotion yasoma shafawa fuskarsa a murtuke.
Dr Imaran ya ce
"Yi da jikin ka mana kayi ka sa kaya."
ta cikin mirror ya hararesa
"Kai kafa dame ni ba maganar ka ce zata sani fita ba,
sai dun kada wad'an can mutanen da ka gayyato su suce sunzo kasar mu anyi musu wulakance,
badun haka ba babu abin da zaisa na katse bacci na."
"Eh na dai ji tun da zakaje ai shike nan karb'i kasa."
ya mika masa kayan.
sai da ya kuma hararar sa kafin ya amsa ya saka.
tun kafin ya gama shirin ai nihin kyansa da cikar halittarsa da kwarjinin sa had'i da cikar haiba suka bayyana a gare sa.
kayan ba karamin amsar kalar fatar sa wankan tarwad'a ya yi ba.
sai wani sheki fatarsa chocolate color keyi.
ya d'aura tsadadden agogo a tsintsiyar hanunsa kana ya murza huta a kansa,
ya zura takalmi a kyawawan kafafunsa masu d'auke da zarazaran yatsu da fafaren farce.

Dr Imran ya bud'e baki da hanci yana kallon sa,
sai yau ya dad'a ganin ainihin sagwaran kyansa a fili.
duk da shi ba fari bane amma ko kyawawan fararen fatan da suke kasashen ketare, basu isa su nuna masa ko mai ba.
ganin yadda Dr Imran ya bud'e baki da hanci yana kallonsa.
yaja tsaki ya zari makullin mota ya yi waje.
da gudu ya biyo sa na fa d'in
"Innalillahi kai ka ganka kuwa had'uwa iya had'uwa, wlh aure rahama ce tun ba'a d'auraba har ka kara kyau."

Bai kula shi ba ya yi gaba.
sai da yafito harabar side nashi ya dubi parking lot nasa, yaga motoci hud'u ne a ciki,
makullin motar daya d'auka kuma ya mance jiya ya faka motar a babban parking lot na gidan.
gajeren tsaki yaja,
sam baya son fita cikin gidan ya had'u ma da kowa, sai dai kuma ya fito baya son kuma komawa.
haka ya nufi get d'in sa badun ya so ba,
Dr Imran ya rufa masa baya.

Ai kuwa yana fita hankalin jama'a ya dawo kansa.
aka sunkuya masa kirari irin na ango.
Dr Imran kuwa sai washe baki yake yana d'agawa mutane hannu, har suka isa parking lot.
ya jefa ma Dr Imran key'n motar, ya cab'e yana cewa
"Ai dole na tuka ango."
ya shiga mazaunin direba shi kuma ya zauna d'aya gefen, Dr Imran ya yi wa motar key mai gadi ya bud'e musu get.

Suna fita hotel in da aka sauke 'yan Germany suka fara nufa.
yaga ko mai an tanadar musu na bukata
ya yi musu barka da zuwa, ya zauna suka d'an tab'a hira, kana suka fita suka je d'aya hotel d'in da aka sauke ma'aikata likitocin su na Abuja.
suma an tanadar musu komai na bukata,
bayan d'an hirar da sukayi da su ma.
kana yasa Dr Imran ya dawo da da shi gida.

Suna shiga gida ana kiran sallar magriba.
dan haka suka sauka suka nufu masallaci, sai da akayi sallar isha kafin suka shigo gida.
yana shiga bedroom d'in sa yashiga rage kayan jikin sa.
Imran ya karaso yana cewa
"Yauwa A.A yi wanka ka sauya kaya da sauri kaga time na zuwa kamun nan ya yi,
na gayawa Dr Sharif da Dr Taj mu had'u a can,
bai kyautu ace bamu je musu ba."
"Kai nifa babu in da zani, ka dai na cika min kunne zaka iya tafiya dan bacci zanyi."
yana kaiwa nan ya shige bayi bai jira jin amsar sa ba,
tun da ya shiga kuwa bai fitoba.
Dr Imran yasan sarai so yake ya tafi kafin ya fito.
ya lekashi ta jikin glass d'in kofar bayin,
ya hango sa kwance a cikin bathtub daya cika sa da ruwa.
idanunsa a lumshe.
kai ya girgiza ya juya ya fita dan yasan dama da kamar wuya yaje.
yaje ya had'u da sauran abokan nasu suka tafi gurin kamun........!

*Nima ina da biki yau da gobe da jibi sai kuyi hakuri bazaku ji ni ba sai an gama,
kafin nazo muje mu leka bikin Abdurrahim da amaryar sa Kuraiba*🤗

13
Ahankli ya bud'e idanun sa da suke a lumshe ya mike ya fice cikin bathtub d'in.
ya ja towel ya d'aura a kugun sa ya fito.
ya tako zuwa in da fridge ya ke ya d'au gorar ruwa mai sannyi ya bud'e ya kai bakin sa, ya kusa san rabin gorar sannan ya mayar da ragowar.
ya tako izuwa gaban wardrobe yabud'e ya ciro gajeren wando da singilet ya saka, ya isa gaban mirror ya feshe jikin sa da turaruka masa dad'i da sanyin kamshi kana ya fito parlour.

Ya haye kan doguwar kujera ya kwanta tare da d'aukar rimut ya sauya tasha izuwa MBC2.
Ajmal ne ya shigo da sauri had'e da sallama, ya karaso cikin parlour'n ya d'an rusuna tare da sosa bayan keyarsa
"Bar ka da dare brother."
da kai ya amsa shi
yana d'an kallon shi ganin kamar da magana a bakin shi.
Ajmal ya dad'a sosa bayan keyarsa yana fad'in
"Am Ya Abdurrahim dama so nake so ka d'an bani hula nawa sunyi datti sauran suna gurin wanki."
"Je ka d'auka."
yafad'a a takaice.
da sauri Ajmal ya ce
"Godiya nake bro."
ya wuce da sauri cikin bedroom d'in nasa ya zab'o hula cikin tarin hulunar sa yafiyo yana washe baki, da gwada hular a kansa,
har ya hango had'uwar da zaiyi da wannan tsadadden hular.
yana fita ya dad'a yi masa godiya bakinsa ya kasa rufuwa,
har ya isa bakin kofa zai fita ya kira sunan sa.
"Ajmal je ka karb'o min Sudan tea a gurin Aunty."
ya ce to.
da sauri ya fice yana duba agogo tara saura.
kuma karfe goma amarya Kuraiba ta ce masa za'a tashi a hall d'in, gashi sai kiran sa take yazo-yazo, dan tasan yayan nasa kam ba zuwa zaiyi ba,
so take shi d'in yazo ta b'adda kafa gun kawayen ta.

Da sauri ya shigo parlour'n Aunty d'auke da sallama a bakin sa.
Aunty na kichin ta fito tana amsa sallamar nasa.
"Aunty barka da dare."
"Yauwa barka dai Ajmal "
"Aunty wai inji Ya Abdurrahim wai ki basa Sudan tea,
amma dan Allah Aunty ki d'ansa wani ya kai masa, wlh sauri nake tun d'azu amarya take ta kira na, gashi ko wanka banyi ba bare na shirya."
Aunty ta ce to.
"Yauwa Aunty nagode." da sauri ya juya har ya kai kofa ya juyo
"Aunty dan Allah kar ace ban tsaya na karb'a ba, ace natafi ne zan dawo in karb'a da aka gama kuma aka kai masa kafin na dawo."
Aunty ta yi dariya.
shima dariyar ya yi kana yafita da sauri.
Aunty ta koma kichin da sauri, dan girkin Daddy take yi.

Nan da nan ta had'a masa Sudan tea ta zuba shi cikin Mug kana ta fito.
d'an jim tayi da tunanin wa zai kai masa, gashi Baba Rabi ta gama aikin ta ta koma b'angaren su na masu aiki.
kira ta kwad'awa Feeryal ta fito tana amsa kiran.
"Zo ki kaiwa Abdurrahim tea d'in nan yanzu ki dawo,
babu wanda zai kai masa, yi sauri girki na zai kone."
d'ankwalin material d'in kanta ta warware tayi mayafi da shi, kasan cewar yana da d'an girma, kana ta karb'i Mug d'in.
Aunty ta koma kichin tana cewa
"Kina kai masa ki dawo."
har ta nufi kofa ta tuna da abun da su Chuchu suka bata suka ce ta sa masa ya tab'a jikin sa.
ta juya cikin sand'a ta na kallon kofar kitchen gudun kada Aunty ta ganta.
ta shige d'aki ta isa in da ta aje ganyen da suka bata silli d'aya ta d'auka, har yanzu yana nan kore sharr d'in sa.
ta fito da sauri tayi waje.
magana taji a bayanta ta juya da sauri sai kuma ta saki murmushi.
ganin wad'an da suke bayan ta.
"Ai mun d'auka kin mance da abun ne, ashe kin tuna muje to mu rakaki."
suka soma tafiya tana cewa
"Na tuna ai ko na saka masa cikin tea d'in ne.'
"Aa kar ki sa a ciki jikin sa kawai muke so ya tab'a."
kai ta gyad'a dai-dai san da suke fitowa daga sashin Aunty.

Cikin gidan tamkar rana hasken wuta ta ko ina,
mutane ba'i 'yan biki suna ta zirga-zirga, bazakace dare bane.
a sannu suka isa bakin get d'in b'angaren nasa.
Chuchu da Chulu suka ce
"Anan zamu tsaya ki shiga muna jiran ki, kar ki bari ya gani kisan yadda zakiyi yad'an tab'a jikin sa kawai."
"Amma dai bazai duke ni ba ko?."
"Har yanzu tsoron sa kike ji ne?."
"Da ne yake bani tsoro da yawa amma yanzu ba sosai ba."
"Yauwa to ai gamu a nan kina sa masa zamu iso in da yake, bazamu bari ya yi miki ko mai ba."
"Kun tabbata dai ko?."
kai suka gyad'a mata.
ta tura karamar kofar ta shiga, tsayuwa tayi tana karewa side d'in nasa kallo,
wan da tun da take gidan bata tab'a shiga ba.
iyaka ta hangi get d'in da ido.
Chapter 19 · 0% Book details