Sashe 32
Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 7 min read
Feeryal ta fito daga bedroom d'in ta d'aure da towel a kirjin ta kanta babu d'anwali, ta nad'e gashinta ta tufkeshi a sakiyar kanta kamar Donut.
kofar Aunty ta nufa ta d'aura hannu kan handle tana kokarin murd'a handle d'in cikin muryarta mai fita da yanayin shagwab'a takuma karo ainihin shagwab'ar ciki tana fad'in
"Ammie wai yanzu ma sai na sa bra, ina breakfast fa bacci zanyi, Ammie kar na sa ko..."
da sauri ta janye hannunta daga kan handle d'in jin an bud'o kofar tun kan takai ga rufa bakin ta.
arba da tayi da shi ne ya sanyata had'iye ragowar maganar ta.
ta matsa gefe ta bashi hanya yasa kai ya fita.
Aunty ta ce
"Feeryal koma ki sa kaya ga Daddy bayida lafiya."
da sauri ta koma ta sako kaya ta zo d'akin Aunty lokacin har bacci ya d'auke shi.
Aunty na zaune da kur'ani tana karantawa a dai-dai saitin kansa.
wannan bacci ya yi shi cikin salama dan kuwa baiyi mafarkin ba,
hakan kuwa baya rasa nasaba da karatun ALQUR'ANI da Aunty take a kansa.
bata gusheba har sai da ya farka da kansa.
ya damke hannunta cikin nashi yana mai dad'a jin girma da kaunarta cikin ransa.
sannu tarika jera masa bayan ta taimaka masa ya yi wanka ta zubo masa abinci ya ci.
Abdurrahim ya kuma shigowa duba shi bayan ya bashi wasu magungunan yafita.
Ajmal ya kira ya ce yarika zuwa yana duba jikin Daddy'n a side d'in Aunty yana sanar masa yanayin jikin nasa, zai tafi asibiti yanzu.
Ajmal dake sashin Hajiya ya mike da sauri yana tambayar dama Daddy'n bashida lafiya ne.
kashe wayarsa ya yi batare da yabashi amsa ba.
Hajiya da taji an ambaci Daddy ba lafiya itama ta mike da sauri tana cewa
"Kai Ajimi Abubakar d'in ne ba lafiya?."
ya ce "Eh Ya Abdurrahim ne ya kira ni wai naje narika duba jikin Daddy yana sashin Aunty."
da sauri Ajmal ya fita hajiya tabi bayan sa tana fad'in
"Au Abubakar d'in ba lafiya arasa wanda zai zo ya gayamin a cikin gidan nan akwai wanda ya haifa min shine, zancen banza kai."
bala'i Hajiya tarika har suka isa sashin Aunty.
Aunty na jiyo hayagagarta ta yi sauri ta fito tana fad'in
"Hajiya sannu da zuwa ga Daddy'n ta nan."
"Eh ba shakka anya Fatima ni da d'ana ma amma wai yana ciwo ban saniba kamar bani na haifa ba,
kin kakabeshi cikin d'aki sai ya mutu tukun kifito min da shi, kice kwana ya kare ko me."
Feeryal da ta mike zata shige d'aki ganin Hajiyar, karaf suka had'a ido aiba shiri ja ta tsaya cak....!
Mommyn Twins ce
22
Hajiya ta yaguna fuska da baki ta ce
"Um gayyar tsiya ana tare da mayu a gida taya za'a zauna lafiya."
Feeryal ta sunkiyar da kai bata d'ago ba sai da Hajiya ta shige d'akin Aunty, kafin tayi hanzarin shiga bedroom d'in ta.
Hajiya na shiga ta rike hab'a tana cewa
"Kai Abubakar ya jikin naka, to mene ne amfanin kakabeka da akayi a cikin d'aki,
kana kwance ciwo na karuwa babu sauki."
ta kalli gefen da Aunty take ta kuma yaguna fuska tana cigaba da fad'in
"Kazo ka kwanta a nan alhalin gacan uwargidan ka, in kwanciyar jinya ce idan bazaka iya yin sa a d'akin ka ba, sai kaje d'akin uwargidan ka,
kafin ka fara sanin kowa ita ka fara sani,
'yar'uwar ka uwa d'aya uba d'aya da mahaifinta da naka,
jinin ka ai sai yafi kula da kai fiye da bare, to banjiba ban gani ba ka tashi ka koma can shashin uwar gidan ka kaje kayi jinya,
mu haka muka sani a hausance baza'a kawo mana wani iyayin zamani ba."
Aunty tayi murmushi tare da girgiza kai.
Ajmal ya ce
"Haba Hajiya sai wani surutu kike ko a ina in dai jinya ce ai za'ayi, surutun nan na damin Daddy kiga yadda yake rumtse ido."
"To ai sai ka rufa min baki ka hanani magana, ina ganin gaskiya a zane bazan sallaka ba."
Ajmal ya masa kusa da Daddy yana masa sannu.
sai a sannan ita ma Hajiyar ta maso tana cewa
"Abubakar ya jikin naka abokin turawa ya baka magani kuwa, to ma wai ina yatafi ne kai kana nan a kwance,
yaran yanzu wai tausayin iyaye ma babu a ransu,
na dai gaya maka maza ka tashi ka koma d'akin uwar gidan ka, mu a al'adarmu ta hausa haka muka ni, miji ya yi jinya ad'akin uwar gida,
kai dama Allah yasa 'yar'uwar ka ce uwar 'ya'yan ka."
cikin muryar ciwo Daddy ya ce
"To naji Haji amma anan nafi samu nutsuwa."
"Nutsuwar hofi na dai gaya maka maza ka tashi ka tafi, kafin kasan nan d'in can ka fara sani,
me ya kashe ka dacan, zancen banza kai, kana tare da mayu guri guda ina jiki zaiyi sauki."
ta juya tayi waje tana masifa.
Ajmal ya ce
"Kai wannan mata akwai fitina, gara da kika tafi ma, ki bar mutane suji gari,
Daddy ciwon kan na nan ko yana d'an sauka?."
Daddy ya ce "Da sauki."
Ajmal ya fita yana kiran Abdurrahim a waya ya sanar masa da sauki.
Aunty dake gefe tana tsaye, Daddy ya kirata da hanu.
ta karaso in da yake.
ya ruko hannunta murya a raunace ya ce
"Kiyi hakuri Fad'imatu."
da sauri ta ta tare numfashin sa
"Daddy gaskiya Hajiya ta fad'a can ne ya kamata ka zauna ba nan ba."
"Kinfi so naje na mutu a can d'in bazaki cigaba da taimaka min ba?."
kai ta girgiza zuciya cike da rauni ta ce
"Bazaka mutu ba Daddy sai in kwanan ka ya kare, amma fa ka san da cewa idan bakayi abin da Hajiya ta fad'a ba za'a sami matsala."
ido ya rumtse bai kuma cewa komai ba, tabbas anan ne kad'ai yasan zai rika samin sassaucin abin da yake ji.
Akai-akai Ajmal ke zuwa duba shi kamar yadda Abdurrahim ya ce mishi.
Aunty kuwa time d'in shan magani nayi zata bashi, bayan ta tabbatar da yad'an ci wani abu.
Mommy ta tada bori in da akayi duniya bata yadda ba an d'au kwanan ta a kaiwa Aunty.
taje ta sami Hajiya
Hajiya ta taso ta shigo da bala'i tace dole sai Daddy ya tashi ya koma sashin Mommy, ai batasan yana nan ba tayi zaton ya tafi tun da safe.
dole Daddy ya tashi ya koma sashin sa, sabo da masifar Hajiya, ta ce eh gara ya zauna a sashin nasa bazai zauna a gurin Aunty ba.
har dare Umma Karima bata shigo ta duba Daddy ba tana can tana bidirin ta tana ta shirya yadda abubuwa zasu tafi mata yadda take bukata.
Tun da dare ya yi hankalin Daddy ya yi masifar tashi, ko da Abdurrahim yazo masa allura ya ce kar yayi masa, yana fargabar kada ya yi bacci.
Daddy ya yi ta iya bakin kokarin sa gani bai kwanta bacci ba, amma fa ina bacci b'arawo sai da ya sami nasarar sacesa.
ai kuwa yasha fama cikin bacci,
igiyar wuta tana cinsa suna daf da caka masa mashi.
wani haske yazo yagilma a sakanin su,
duk suka dare.
daga can yaji ana cewa
"Ka kamo haskem can kar kabari ya tsere kayi gaggawan taro shi, shine tsiran ka,
ya zauna cikin rayuwar ka tanan ne zaka kub'uta, idan ya kub'uce shike nan babu tantama zaka mutu a wannan tsekon!."
hasken yatafi can da nisa sannan ya juye zuwa mutum, sai dai an bashi baya baya iya ginin fuskar mutumin.
yana b'acewa wad'an nan halittun suka kuma tasowa suka dawo suka cigaba da azabtar da shi.
dakyar ya farka ya had'a zufa sharaf.
ciwo ya dawo sabo.
Mommy na d'akin amma bata iya taimaka masa da komai ba sai sannu da take ta jera masa.
Har sai washegari Umma Karima ta shigo duba shi, ta koma da karfin gwaiwar ganin aikin ta na tafiya dai-dai yadda take so.
A b'angaren Aunty kusan kwana tayi tana sallah da nima masa sassauci a gurin Allah.
da sassafe taje ta duba shi ganin yadda yadad'a fita hayyacin sa.
ta dawo sashin ta tashiga rusar kuka.
waya ta d'aga ta kira Hajja Umma tana d'agawa takuma saka kuka,
hankalin Hajja Umma yatashi matuka tashiga tambayar ta me yake faruwa,
da kyar ta samu tayi shiru nan take gaya mata abin da ke faru.
Hajja Umma ta sauke numfashi gwuiwa a sanyaye ta ce
"Amma ni a gani na jinyar nan nasa a had'a da na gida, a gani ko za'a dace,
Allah ubangiji ya bashi lafiya, bari Alhaji ya shigo zan sanar masa."
Aunty ta ce to sukayi sallama ta kashe wayar.
tausayin Daddy ya cikata ciwon kwana biyu ya jijjigashi ya fita hayyacinsa gaba d'aya.
Motar Abdurrahim ne yashigo gidan.
yana gyara parking ya fito yashiga sashin Daddy.
ganin jikin Daddy na yau sai da jikin sa ya d'anyi sanyi, bayan ya bashi kulawar data dace ya fito ya wuce ide d'in sa.
yana tsaye cikin bedroom d'in sa yana rage kayan jikin sa yaji an rungume shi ta baya.
tawani lumshe ido
cikin makirarren murya ta ce
"Sannu da dawowa mijin Kuraiba an dawo lafiya ya aiki."