← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 30 OF 43

Sashe 30

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Washegari da safe bayan ya fita office ta shirya ta d'au mota sai AA FIYA STREET.
tana isa b'angaren Mommy ta shige.
Mommy na ganin ta ta ce
"Ya akayi Farida ko jiya kinyi mantuwa ne?."
ta ce "Nazo cin uwar mayyar yarinyar nan ne, jiya kwana Faruoq ya yi yana ambaton sunan ta,
zo muje Sumayya ko Ameerah ku kira min ita."
Ameerah tayi kus kamar bataji ba.
Mommy ta ce
"Ke Sumayya tashi kije ki kira mata ita, ai kiyi mata tatas in da gobe bazata kuma bin kurwar sa cikin dare ba."
Farida ta juya ta fita Sumayya ta bita tana fad'in
"Aunty Farida da kin rabu da ita."
hararar ta tayi
bata tsaya ba sai da tafito waje ta ce
"Wuce kije ki kira min ita."
Sumayya ta wuce sashin Aunty.
a parlour ta tadda Aunty ta ce wai Farida tana kiran Feeryal.
Aunty ta d'anyi jim sannan ta ce
"Me ya faru ta ke niman ta?."
ta ce "Ni ma ban sani ba tadai ce na kira ta."
kai ta jinjina ta ce
"Shiga tana ciki."
Sumayya ta shiga ta sameta tana bacci ta tasota ta d'au hijabi suka fito.
har sun kai kofa zasu fita
Aunty ta ce
"Tafad'i abin da zata fad'a ki dawo bance ki amsa ta ba."
Feeryal ta gyad'a kai kana suka fita.
Aunty ta koma ta zauna bataji ko d'arr ba dan tasan ba shegiyar da ta isa tasa mata hanu yanzu ta share, sai dai taji wa jikinta.

Farida na ganin su tasoma tahowa tana fad'in
"Yau nazo naci uwar ki har gida naga wanda ya tsaya miki."
ta na isowa in da take ta shako wuyan hijabin ta.
"Meye had'aki da mijina da zakisa ya koma gida yana kawo min zancen ki,
maitar taki takai har kin fara bibiyar mijina,
me za'ayi dake da ba a san asalinki ba,
to wlh gargad'i na farko na karshe idan na sake ganin ki a inda mijina yake sai nayi miki d'anbanzan duka na b'ata fuskar da yake rud'in ki yake kaiki ga mazajen mutane,
shegiya mayyar banza aljanar ruwa,
nafi karfin ki wlh ba dai miji na ba."

Ajmal dake tahowa ta bayansu ya ce
"Meye haka Farida wani irin abu ne wannan meye amfanin hakan."
cikin masifa fa ce
"Karabu dani Ajmal naci uban yarinayr nan, dan wlh bata isa ba mijina yafi karfin ta."
"Kaji wani shirme dan Allah ita cewa tayi tana son mijin naki."
"Idan ta fad'a ma basai na kasheta ba, wlh mijina ya girmi ajinta 'yar da ba a san asalinta ba ma,
idan bata fita sabgar miji na ba, wlh sai na halakata."
kai Feeryal ta sunkuyar Ajmal na kokarin jan hannun Farida da ke rike da wuyan hijabin ta wayarsa tayi kara.
ya zaro wayar a aljuhu ya kai sa kunne
daga cikin wayar ya ce
"Bawa Farida wayar."
ya zaro a kunnen sa yamika mata yana cewa
"Wai gashi."
sai da ta harare sa kamar ita ce gaba da shi kafin ta ce
"Inji wa nifa baza'a mareni a hanani kuka ba."
ta fizge wayar ta kai kunnenta.
Ajmal yashiga waige-waige yana son ganin daga ina yake har yasan abin da yake faruwa, yana d'aga kai ya hango sa can saman upstairs na side d'in sa yana tsaye rike da Mug a hannunsa ya yin da d'aya hannunsa ke kare da waya a kunnensa.
daga cikin wayar Farida tajiyo muryar sa

"Saketa! baki da hankali ne zaki rika d'agawa mutane murya a cikin gida, oya fita ki bar gidan nan ki koma gidan ki, kar ki kawo wa mutane haukar banza,
kisa ta tarawa mutane jama'a."
Farida ta tura baki ta mikawa Ajmal wayarsa.
ta sake ta tana cewa
"Allah ya taimake ki wlh da sai kin gane cewa mijina ba saranki bane,
mayyar aljana kawai."
ta juya fuu ta yi gurin motarta tashige tabar gidan.

Ajmal ya dubi Feeryal da jikin ta ya yi sanyi yace
"Yi hakuri Feeryal kije abin ki."
a hankali ta juya.
tana shiga Aunty ta bita da kallo ganin jikin ta a sanyaye ta ce
"Me yasa Farida'r take niman ki?."
murya a sanyaye ta ce
"Wai nafita sabgar mijinta wai ya koma gida yana zance na."
Aunty tayi murmushi tare da girgiza kai
ta ce "Je kiyi wanka kizo kiyi breakfast."
ta juya ta shige bedroom d'in ta.

Ji ya yi an rungume shi ta baya, Kuraiba ta manna kanta a bayan shi tana shafa kirjinshi.
cikin narke murya ta ce
"Mijin Kuraiba ba ko zuwa duba ya na kwana ba, kasan da ya nayi bacci kuwa,
gurin nan sai zafi yake min sai da nayita gasashi da ruwan zafi,
ka duba min zafi yake min har yanzu."
hannunta ya b'anb'are a kirjin sa ya juyo tare da wasa mata wani kallo kana ya juya ya bar gurin.
wani uban mika ta sake tana tuna kasantuwarsu har yanzu zakinsa yaki gogewa a kwakwalwar ta,
tana ji ina ma ace ta kasance cikin hakan yanzu..

Umma Karima ce tsaye cikin d'akin ta, rike da waya a kunnenta.
daga cikin wayar ake fad'in
"Hajiya sai yau Allah ya yi aka samo wani da kyar,
in zaki biya million 2 idan guri ya rufa zan kawo miki."
Umma Karima ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya tana fad'in
"Allah na gode maka wahalata tazo karshe, million 3 zan baka shima ka rike ne dai-dai komai ya dai-dai ta zan biyaka kud'in aikin ka mai soka."
"Hahaha Hajiya to na gode anjima zaki ganni."
Umma Karima ta sauke wayar tashiga tika rawa.
tana fad'in
"Sai ni Hajiya Karima bani Dubai London bani England."
tawani shekewa da dariya
"Hahaha yanzu wasan zai soma.......!

21
Guri na rufawa kamar yadda mutumin da sukayi waya da Umma Karima yace zaizo kuwa sai gashi yazo.
a parking lot d'in ta ya tsaya tafito ta sameshi.
ya mika mata wata bakar laida yana fad'in
"Ga sakon ki Hajiya na d'auki kasada sosai amma na shafe duk wata shaida."
har hannunta na b'ari ta karb'i laidar tana cewa
"Kai sannun ka da aiki kayi namijin kokari da kai za'aci arziki saboda kayi rawar gani wajen ganin an samo arzikin,
yanzu ga wannan miliyan ukun ne, kaje ka sha shayi da su kayi murna lokacin arzikin ka yayi."
ta mika masa jaka mai d'auke da kud'ad'en da ta shirya ciki.
ya karb'a da murna yana fad'in
"Lallai kuwa godiya nake Hajiya, ai muna fadarki muci arziki mu barta a inda take."
har ya shiga motar sa bai fasa zuba mata godiya ba, yana fita tashiga kwad'awa Liti direban ta kira.
ya shigo cikin hanzari yana amsa kiran nata.
ta ce
"D'auko makullin mota da sauri fita zamuyi yanzu."
"Ina kuma zamuje Hajiya da magriban nan?."
"D'auko da'alla a hanya kayi min wannan tambayar."
ta shige mota da sauri tana rungume laidar da kyau a jiikinta.
sai da suka haura titi kafin ya dubeta yana cewa
"Hajiya ina muka dosa ko tafiya zamuyi ta yi kawai?."
ta ce "Dajin Mali zamuje kara gudun motar yi sauri hanzarta."
"Hajiya ba dai kud'i kika d'auka a laidar nan zaki kai masa ba, ni fa dama ina da bukatar wasu kud'ad'e sabo da na kwan biyu ban yi aike gida ba."
"Ni matsala ta da kai ke nan, kullum baka da damuwa sai na kud'i, ko an baka sai ka kuma niman su, ka aje bukatar kud'in nan naka yanzu sai an gama komai tukun,
Allah na tuba idan aiki ya kammala meye kud'i kuma ai sai dai ka bawa wasu,
kai dai yi sauri mu isa."
Liti ya kara gudun motar yana cewa
"Wai gara in fad'a miki da wuri ne kar ki kwashi kud'ad'en duka ki kai masa mu mu rasa."

Karfe 7 da rabi suka isa saboda gudun da motar take.
Umma Karima ta sauko a motar guri ya rufa yayi duhu, babu tsoron Allah bare tsoron dukun dajin bare tsoron wani mugun dabba mai cutarwa.
zuciyarta ya kekashe muradin ta kawai take hangowa a gabanta.
ta kunna hasken wayarta ga kuma hasken fitilar mota.
jiki na rawa na son cikan muradinta, sai kakabe laidar take a jikinta.
ta cire mayafi ta kunce d'ankwali ta cire takalmi, ta d'uru cikin duhuwar kogonnan, zuciya a kekashe babu d'igon tsoro bare imani.

"Gafara dai boka yau gani tafe da babban guzuri, nasamo cikon na uku."
wani irin hargitsastsen dariya kogon ya kaure da shi
"Hahahaha kinyi nazari da lissafi mai kyau, saura kiris laya ta gama narkewa jeki sanya shi cikin tukunya."
da sauri ta isa gaban tukunyar kaskon tajefa laidar ciki.
wani irin hargitsewa gurin ya yi da wani irin sauti mai ban tsoro,
tukunyar ta kama tafasa tana dafuwa tamkar wutar zuga,
wani kumfa ya taso fuuu yana bin jikin tukunyar yana gangara zuwa cikin wani rami mai zurfin gaske da ba'a iya hango karshen sa.
jikin Umma Karima na rawa, idanunta a kan tukunyar, har kumfar tagama sauka tas tukunyar ta shafe kamar babu abinda ya tab'a zama cikin ta.
kazamtacciyar dariyar nan ya kuma kecewa da shi yana fad'in
"Aiki ya kammala ikon ki ya soma."
zubewa gaban shi tayi tashiga karanto mishi ayoyin godiya.
ya ce "Tashi kije gaki ga duniya kin samu."
jiki na kyarma ta mike tafito daga kogon ta kwashi kayakin ta, tashige mota bakin ta yaki rufuwa.
Liti ya kunna motar su ka soma fita daga dajin.
ganin yanda yau ta fito cikin mashahuriyar farinci daga gurin bokan nata ya ce
"Hajjaju an samo wata nasarar kenan."
baki ta dad'a washewa ta ce
"Nasara mai girman gaske ma kuwa, kai dai yi sauri mu isa gida kawai."
karfe tara ya kawo su gida, Umma Karima ta shige gida tana jin kanta da girma.
Chapter 30 · 0% Book details