← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 14 OF 43

Sashe 14

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Da sauri ta bubbuga Miemie ta juyo.
tuni hawaye yasoma sauka a idon ta,
Miemie ta ce
"Feeryal mene ne kuma?."
rigar ta d'ago ta nuna mata murya na rawa ta ce
"Ina ta ce miki kizo mu je gashi kinsa na b'ata masa riga."
ido Miemie ta waro ta ce
"Wannan kamar rigar da Ya Abdurrahim da ya shigo da shi a hannunsa, dan singlet ne kad'ai a jikin sa sai wannan rigar dake rike a hanun sa ya shigo, ya wuce d'akin Hajiya kafin shigowar ki."
kai ta gyad'a hawaye ya zubo sharr.
Miemie ta ce
"Munshige su yi sauri muje mu wanke kafin ya fito ya gani."
cikin Feeryal ya dad'a d'ura ruwa cikin muryar da kuka ke son kwace mata ta ce
"Ai ya gani."
kirji Miemie ta dafe da sauri ta jata sukayi waje, sai da suka fita kafin ta ce
"Da gaske yafito ya gani?."
kai ta gyad'a hawaye na zuba.
Miemie ta rike kugu tare da sauke numfashi sannan ta ce
"Muje mu wanke masa da sauri."
Feeryal ta gyad'a kai jiki na rawa suka wuce sashin Ammah.

Suna shiga d'aki Miemie ta ce taje bayi ta gyara jikin ta, tad'u pat da sabon pant ta bata da kaya ta saka.
tafito ta rab'e bakin gado tana ciccire ido, ganin yadda ta tsorata da yawa Miemie ta shiga bata baki tana fad'in
bazai mata komai ba ta saki ranta ai ba da gangan tayi ba, kuma ma ai ita ce da laifi, ita ta sata zama kan kujerar da rigarsa ya ke kai.
ta shiga bayi ta wanke masa rigarsa tas da ruwan kumfa mai kamshi, kana ta sarkakeshi da ruwa mai kyau,
yafita kwal babu ko d'igon jini, kana ta wanke towel da hijabin da Feeryal d'in ta cire.
ta matse a inji ya boshe ta fito da su.
ganin yadda rigar ya yi haske bazaka tab'a ce wani abu ya same shi, nan Feeryal tad'an ji sanyi cikin ranta.
Miemie ta kuma fesa turare har kala uku a jikin rigar sannan ta jona ayon ta goge shi ba rigar ba hatta cikin d'akin gaba d'aya ya garwaye da kamshi.
Miemie ta d'ago ta dubi Feeryal da ta d'an fara dawowa hayyacin ta ta ce
"Yauwa to muje a kai masa."
Feeryal tayi raurau da ido
"Miemie bazai duke ni ba?."
"Babu abin da zai miki muje to ni zan kai masa imma dukan ne ni ya duke ni."

Suka fito Feeryal na jan kafa da ka ganta kasan a mugun tsorace ta ke.
can suka hango sa bakin get na side d'in sa yana tsaye jikin motar da alama fita zaiyi dan ya sauya shiga,
wani riga da wandon yadi ne skai blue d'inkin haf jamfa a jikin sa, ya yi matukar kyau cikin shigar,
murjajjen fatarsa Chocolate colour sai d'aukar ido ya ke.

Miemie ta tsaya da sauri ta dubi ta ce
"Feeryal dole fa ke zaki kai masa, karb'a ki kai masa ki bashi hakuri, nasan idan nakai masa zaice kin rainashi me yasa ke baki kai masa da kanki ba."
nan da nan Feeryal ta dad'a birkicewa har sai da taji wani jiri ya gilma mata.
"Yi sauri ki kai masa kinga zai shiga mota."
Miemie ta damka mata rigar a hannunta.
"Je ki mana Feeryal kar ya tafi."
numfashi ta fizga da kyar kana ta soma d'aga kafarta, jikinta na rawa ta kankame rigar gam-gam kamar mai shirin b'uya jikin rigar, jikin ta na b'ari da kyar take iya d'aga kafarta tana tafiyar sand'a,
gaba d'aya jikinta kyarma yake,
yanayin tsoron da take ciki bazai misaltuba.
da kyar ta isa in da yake, kasan cewar fuskarsa na ta jikin mota ne ya bata baya.
nan ta sami damar iya tsayuwa ta bayansa, da kyar ta iya bud'e baki murya na rawa had'e da sarkewa ta miko masa rigar tana fad'in
"Ka.ka..kayi hakuri ga.ga..rigarka."

Da d'an sauri ya waigo da alama baisan da mutum a gurin ba ga yadda ya juyo d'in,
wani irin dibirbircewa tayi kamar ta kurma ihu ko ta ruga aguje.
sanda idanunta ya sauka cikin nashi.
sabar tsoro sai da rigar ya sub'uce a hannunta ya fad'i kasa.

Ido ta waro tare da kai hannun ta duka biyu ta toshe bakin ta,
sai kuma tayi saurin sunkuyawa ta d'au rigar ta rungume shi a jikinta gam-gam.
ido ya bita da shi fuskarsa babu annuri.
kai ta shiga girgizawa tayi baya da kafarta ta shiga ja da baya murya na rawa ta ke fad'in
"Dan Allah kayi hakuri."
wani kallo ya wurga mata tare da cewa
"Move here!."
ya juya ya shige motar sa yayi wa motar ki ya nufi babban get.

Da sauri Miemie ta fito daga mab'uyarta ta zo in da take da sauri ta ruko ta tana cewa
"Feeryal bai karb'a bane?."
kai ta gyad'a mata hawaye sharr.
Miemie ta ce
"Ai dama da wuya ya karb'a taho muje kawo rigar bazai kuma sawa ba zan baiwa Isa direba"

Ganin yadda Feeryal d'in ta birkice gaba d'aya, Miemie ta rakata sashin su, suna shiga Miemie ta juya,
ita kuma ta shige bedroom d'in ta ta haye can kuryar gado ta dunkule guri guda ta cusa fuskarta cikin blanket.

Miemie na fita tayi gurin Isa direba ta kai masa.
Isa direba ya yi ta murna ganin riga mai kyau da tsada.
kasancewar war yau asabar ne su Ajmal suna gida,
akan idon su tayiwa Isa direba kyautar rigar.
zata koma Faisal ya kira ta, ya ce ta zo ta kaiwa Ammah kulan ta.
ta karaso gurin su.
Faisal ya mika mata kular yana fad'in
"Ke a ina kika sami rigar can da kika bashi."
"La ai bansan kuna nan bama da kai na kawo mawa, ko kuma ba kai bama Ya Ajmal ko Ya Shamsuddin."

Faisal ya harareta "Ke ni sa'anki ne."
Ajmal ya yi dariya ya na fad'in
"A ina kika sami irin wannan rigar haka, ko saurayin ki ne ya kawo miki tsarabar nashi."
"Cap waya bashi kud'in siyan wannan rigar, a ina ma taga saurayin tukun."
cewa Faisal yana hararar ta.
Shamsuddin ya ce
"Wa ya fad'a maka wad'annan yaran ai sai Allah duk suna da samaruka, ranar ma ina jin Sahla wai tana hira da saurayi a waya hmm."
dariya ta yi tana cewa
"Rigar Ya Abdurrahim ne fa dan mun samasa datti a jiki shine wai baya so,
shine nikuma na kawa Isa direba kyautar sa, ban san kuna nan ba da ku na kawo muku."
"Yauwa idan kuka kuma yin datti da wani ya ce baya so ku kawo min, wai ina mutumiyar taki ce yau na ganki ke kad'ai."
cewar Shamsuddin.
ta ce "Yanzu muka rabu tana side d'in su, Ya Shamsuddin kana so Ya Abdurrahim yayi mana kabarin da ba sallah ke nan idan muka kuma sa masa datti a jikin kaya, tap hmm."
ta juya da sauri ta bar gurin..

Tun da Feeryal ta kule d'aki bata fito ba tana nan a dunkule cikin bargo tsabar tsoro har wajen magriba tana kwance, kan kace me jikinta ya had'a zafi rau zazzafan zazzab'i ya saukar mata.

Ganin shiru-shiru Aunty bata ji d'uriyarta ba, nan ta tuna da tun d'azu taga shigowar su da Miemie, Miemie ta fita ita kuma ta shige d'aki,
bata kuma ganin ta ba tun daga lokacin.
Aunty ta nufi bedroom d'in ta na kwad'a mata kira.
ta tura kofar ta leko kanta ciki,
can ta hangota kwance dunkule cikin blanket tana rawan sanyi.

Da sauri Aunty ta iso bakin gadon tana fad'in
"Subhanallah Feeryal lafiya me ya same ki?."
ta hayo gadon tare da zame blanket d'in taji jikin ta zafi rau kamar wuta.
hankalin Aunty ya yi mummunar tashi, nan da nan ta d'aga waya ta kira family doctor su.
ya ce mata ya fita ya yi nisa amma zai dawo zuwa anjima zai zo.
Aunty ta ce
"Dan Allah Dr ka taimake ni kazo yanzu."
"Hajiya kiyi hakuri zan iya kaiwa awa d'aya a hanya ma kafin na iso kinsan yanayin garin akwai gosulo da yawa, kuma na d'anyi nisa wlh amma dai zan iso ko zuwa bayan isha ne in Allah ya yarda,
a bata paracetamol ta sha kafin na iso."
Aunty ta kashe wayar ta mike da sauri ta je d'akin ta ta d'auki paracetamol da ruwa ta dawo ta d'agota ta tallafo ta tana fad'in
"Sannu Feeryal sannu kinji, baki da lafiya shine zaki kwanta kiyi shiru da ciwo na cinki,
sha maganin nan kafin Dr ya zo."

Rau-rau tayi da ido sai ga hawaye masu d'umi sun zuba, cikin galabaitaccen murya ta ce
"Ammie kar yamin Allura dan Allah Ammie kice kar ya min Allura."
"Kiyi hakuri Feeryal kinji jikin ki kuwa, nasan ma dole sai an had'a da allura kafin ya yi sanyi, sannu kin ji, ina ne ke miki ciwo yanzu?
sha maganin maza yanzu kafin ya zo."
Ta saka mata maganin a baki had'e da ruwa ta sha tana matsar kwalla.

Aunty na zaune a gefen ta tayi mata pillow da cinyarta, sai sannu take jera mata.
ko da lokacin sallah ya yi a nan d'akin nata tayi al'wala tayi sallah.
har wajen karfe tara Aunty na zuba idon ganin Dr ganin goma saura ta kuma kiran sa a waya.
ya ce
gashi nan a hanya gosulo ya tare shi.

Aunty tayi salati ta rasa ina zata sa kanta sabar damuwa.
ga shi Daddy baya nan.
a haka suka kwana tare da ita, jikin ya d'anyi sanyi ba sosai ba sakamakon paracetamol d'in da ta sha.
kusan asuba jikin ya kuma yin zafi rau sai rawar sanyi take.
Aunty ta rasa ina zata sa kanta shalelen ta ba lafiya.

Ana idar da sallar asuba ta kira number Dr sai dai akayi rashin sa'a wayar akashe.
tayi ta kiran number har gari yayi haske, ganin hakan ba zai samar mata mafita ba.
tayi waje da sauri tana kwad'awa direba kira.
sanin yanzu suna masallaci ta yi waje da sauri.
Chapter 14 · 0% Book details