← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 8 OF 43

Sashe 8

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

A parlour ta tadda Feeryal ita kad'ai tana zaune tana kallo a TV.
Miemie ta zauna kusa da ita tabuge cinyar
ta tana fad'in
"ke Ibrahim yakirani fa tund'azu,
ya d'agamin hankali shiyasa ma nazo amma tun d'azu ina kwance ne banyi niyyar zuwa gurin ki ba,
tun da ke tsoro ya hanaki fitowa kizo in da nake, matsoraciya kawai,
sai aka ce miki kuma shi Ya Abdurrahim d'in duka yake haka kawai babu dalili,
kuma ma ai dukan da ya min ni nasan har da naki ya had'a dan duka na yafi na kowa tun da tare muke da ke,
tare Ameerah ta kulla mana sharri."
Feeryal ta marairaice fuska batayi magana ba sai narai-narai da ido take suna kokarin kawo kwalla.

Miemie ta ce
"Bari na kirashi dan ya ce yayi ta kiran ki baki d'aga wayan sa, nace kad'an daga aikin ki."
tana kokarin kiranshi Feeryal ta ce
"Ni dai Miemie da kin barshi to mezanmishi."
Miemie ta ce
"Ke dallah wannan had'add'an gayen,
kuma yace zai zo na ce wallahi yazo."
Feeryal taware ido ta ce
"Wallahi babu ruwana Miemie yazo ina baburuwana."
Miemie ta ce
"Ke wlh dad'ina dake tsoro, da har dake aka buga
ranar da ban san ya zakiyi ba nasan har fitsari sai kinyi tsabar tsoro,
ke wallahi Ibrahim dagaske yakeyi ya ce aure yake son yi babu wani bata lokaci,
ya ce yana zuwa yau gobe babansa zaizo."
kafin Feeryal tabata amsa Aunty tafito.

Miemie ta ce
"Yauwa Aunty dama wanine sunansa Ibrahim muka had'u da shi agun bikinan ya ce yana son Feeryal,
abokin yayan Feenat ne ya ce zaizo yau gobe kuma yaturo magabatansa anemamasa izini gurin daddy."

Aunty taware ido ta ce
"Badai shine kuka hadu da shi ya yi mata rashin d'a'ar nan ba?."
Miemie ta ce
"A'a wlh Aunty bashi bane wannan mutumin kirkine kuma yana sonta,
abokin yayan Feenat ne ma har Mom d'in sa ya nuna mata Feeryal."
Aunty tad'anyi shiru sannan ta ce
"Amma dai yafara neman Daddy'n tukunna, in ya amince sai ya zo."
Miemie ta ce
"Ya ce zai turo babansa gobe yau zaizone kawai ya tambaye ta da kansa idan ta ce ya tura sai ya tura."
Aunty tace Allah yakaimu.

Dayamma wajen karfe 4:40 saiga kiran Ibrahim awayan miemie yazo yana bakin gate.
Miemie tazo tasa security suka bud'e masa gate takaishi bakin sashin Aunty.
ita tashiga ta kirawo Feeryal, dakyar Feeryal tafita sai da Aunty ta ce mata taje tadawo karta dad'e.
tafito da babban hijabi tunkafin takaraso inda yake,
ya kafe ta da ido yana fadin
"Masha'allah wallahi kamar da hijab d'inma kinfi kyau."
Feeryal takaraso a hankali ta d'an tsaya gefe da shi ta ce masa
"Inayini."
wani murmushi ya sake idanunsa a kanta.
Miemie ta ce bari tad'an basu guri tayi falon Aunty tazauna.

Feeryal natsaye Ibrahim nata zayyane mata kalan son da yake mata shifa nan da wata d'aya yakeso ya aureta.
Feeryal dai batace kalaba sai hijabin dataja tarufe gefen fuskarta.
yaleko fuskarta yana fadin
"Bud'e mana inata magana bakice komiba,
kitsaramana yadda zamu gudanar da shagalin bikinmu."
jan hijabin tadayi tana murmushi tarufe fuskarta sosai.
salati sukaji abayansu ana tafa hannu.

"Innalillahi wa innailaihirraji'un! lallai kun shahara wato iskancin naki harcikin gida,
abin naki ya girmama har maza kika fara kawo mana su cikin gida kuna sheke ayarku,
iskancin naku har gida!."
Umma karima tayi maganar cike da hayagaga takawo hannu tad'aura abaki tana tana fad'in
"Yihuhu jama'a kuzo nakamasu, na kamasa da idona."
Ibrahim yatsaya yanamata kallon mamaki,
Feeryal ko gaba d'aya jikin ta ya d'au kyarma........!

KUYI HAKURI DAN ALLAH BANI DA BAKIN DA ZAN IYA BAKU HAKURI WLH SAM BANSO HAKAN TA FARU BA AKASI AKE TA SAMU KWANA BIYU,
DA DAREN NAN NASAMU NAYI WANNAN KUYI HAKURI DA SHI DAN ALLAH

*Assalamualaikum barkanmu da wannan lokaci barkanmu da dawowa hutun Ramadan anyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ya karbi ibadun mu*

Ibrahim ya bita da kallo ganin kiri-kiri da gaske sharri take son gina musu,
ya ce
"Me kike nufi ne wai? muna tsaye muna hira ki ce kin kama mu, kin kamamu muna me?."
da karfi ta ce
"Iskanci iskanci na kama ku da idanun nan nawa kiri-kiri ka shige cikin hijabi kana kwakularta,
munafukan Allah ta'ala asirinku ya tonu.
jama'a kuzo na kama 'yan'iska."
kan kace me ma'aikatan da suke aiki a babban kichin sun taho gurin.
Umma Karima bata fasa kwalala ba fad'i ta ke
"Na kamasu wlh na gansu da ido na, ya makale cikin hijabin ta suna aikata masha'ar su.
Mommy da Mom akusan tare suka iso gurin 'ya'yan su sun kaimusu rahoto.
sai tafa hannu suke da sallalami.
Ammah da mai aikin ta ta sanar mata da abin da ke faruwa ta fito abujajan.
Ibrahim na tsaye ya cika da mamaki matuka.
Mom ta rike hab'a tana sallalami, da fad'in
"Ai dama akwan a tashi in dai halin mutum ne sai asirinsa ya tonu,
a had'asu da karnuka da security su rakasu da duka 'yan'iska tambad'ad'd'u, zaku kawo mana iskanci har cikin gida."
cewar Mom tana aika wa Ibrahim da Feeryal banzan kallo.
Ammah data karaso gurin tayi saurin cewa
"A'a baza'ayi haka ba zo ka wuce katafi abinka kaji bawan Allah."
Mommy ta ce
"Kamar ya zakice ya tafi Hajiya Safiyyah ai yazama dole su karb'i hukun ci dukkan su shi da wacce ta jajub'o sa."
Ammah ta girgiza kai ta ce
"Ashsha ai ni banga shaidar da ke nuni da abin da ake zargi ba,
mutum d'aya bai wadatar da bada shaida kan zina ba,
a cikin ku akwai wannda ta gani da idon ta bayan Hajiya Karima?."
Ammah tayi tambayar tana tsaresu da ido.
duk ma'aikatan suka girgiza kai, Ammah ta ce
"To kaje abin ka kaji,
dan kuma Hajiya Halima da Hajiya Nafisat kusan a tare muka iso nan da su,
babu wanda acinin mu zai bada shaidar abin da ake zargi, dan ita zargin zina sai ana da kwararan shaidu guda uku wad'an da suka gani da ido."

Ibrahim yaja kafarsa yana girgiza kai yama kasa iya cewa komai, tsabar mamakin matar,
ya shige motarsa ya bar gidan baya ko ganin gabansa.

Gaba d'aya gurin ya kacame da hayani Mommy da Umma Karima da Mom, sai bala'i suke suna fad'in
yarinyar da kowa yasan ita 'yar'iska ce a filin Allah cikin bainin jama'a take iskanci, har ana d'aukarta hoto da video waye bai san 'yar iska bace.

Aciki kuwa TV da yake a kunne ne ya hana Aunty da Miemie jin abinda yake faruwa da wuri,
sai da hayaniyar ya kara yawa kafin suka jiyo hayaniyar sosai.
da sauri suka nufo waje.

Aunty ta tsaya cike da mamaki tana jin abinda yake faruwa cikin b'acin rai sosai ta dubi Feeryal dake tsaye ta toshe bakin ta da hijabi tana hawaye ta ce
"Ke Feeryal da gaske kin aikata abin da suke fad'a?."
da sauri ta girgiza kai murya na rawa hawaye na zuba ta ce
"A'a Ammie."
hannun Feeryal Aunty ta janyo ta dawo da ita kusa da ita sannan ta dubi Umma Karima ta ce
"Hajiya Karima kin dai ji da kunnen ki ta ce bata aikata ba, to kuwa tabbas bata aikatan ba,
ki tsaya a matsayin ki kada ki sake shiga lamarin ta bai shafe ki ba."
"Iye lallai ma kuwa ba shakka! irin ga waliyyiyar nan wacce bata fad'an karya daga ta fad'i magana gaskiya ce,
tana aikata iskanci kiri-kiri a kamata dan ta ce batayi ba shike nan ya zauna a kan bata yin ba."
Aunty tayi saurin katse ta
"Ni na yarda da d'iyata idan da ta aikata nasan bazata tab'a yi min karya ba zata fad'a min,
dan haka bata aika ta ba,
kowa ya kama gabansa kubar min kofar side!."

Nan da nan ma'aikatan kowa ya kama gabansa.

Umma Karima tayi shewa tare da tafa hanu tana fad'in
"Ahayyeee rass. ke har kina da bakin fad'ar wannan maganar yarinyar da gata nan cikin hoto kiri-kiri tana rungume da wani katoton gardin d'an iska,
a cikin bainin nasi kowa ya gani babu wanda bai sani ba,
an dai ji kunya wlh, an aje katuwar 'yar'iska a gida ana son ta b'ata mana yara"
Aunty ta yi saurin katse ta
"Ki iya bakin ki Hajiya Karima kar ki kuskura ki wuce gona da iri, zakiyi nadamar bakaken kalaman ki."

Mommy ta watsawa Aunty kallon banza tana cewa
"Bafa zai yuwu ba yazama dole ayi zama da Alhaji dan wlh bazamu zauna da 'yar iska ta gurb'ata mana rayuwar 'ya'ya ba, Ameerah Sumayya wuce mujen ku bari Alhajin ya dawo."
Mom ma ta kad'aga keyar Sahla bayan ta gama fad'an miyagun maganganun ta.
Umma Karima ta dubi Aunty tana fad'in
"Hajiya Fatima alkadarin ki na daf da karyewa, dan bazamu bar tsintacciyar agola cikin 'ya'yan gida ta koya musu iskanci ba, na fad'a na kara fad'a,
kiyi abin da zakiyi."
Siyama ta yamutsa fuska ganin kamar tana son yin magana Miemie ta dalla mata harara.
Umma Karima ta kad'a keyar nata iyalan
Bilkisu Rahma Saddiqa Nabila Siyama suna gaba tana bayan su.

Ammah tabi bayan su da kallo kana ta girgiza kai tana fad'in
"Agwagwa ke nan 'ya'yan ki nagaba kina baya, mugun abu yabi dare cikin duhu Allah shi kyauta,
kiyi hakuri Feeryal, Hajiya Fatima sai dai ayi ta hakuri dan wad'an nan mutanen halin su sai su."

Aunty ta ce "Mugun nufin su ya kare a kan su, insha'allah abin da suke son gani kuwa bazasu gani ba,
haka zasu kare da kai kawo."
ta ja hanun Feeryal suka shige ciki Miemie ta biyo bayan su, Ammah kuma ta koma sashinta tana mai mamakin hali irin na Umma Karima da su Mommy masu shaidan zur.
Chapter 8 · 0% Book details