← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 35 OF 43

Sashe 35

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

Da sauri Umma Karima ta shigo sashin Daddy, lokacin ana daf da kiran sallar magriba.
tasan yanzu kowa ya koma sashin sa, Ajmaal da yake kwana tare da shi ma yanzu ya fita shirin zuwa masallaci.
Daddy na kwance kan sallaya yana zaman jiran a shiga sallah ya mike ya gabatar.
ta shigo ta hakimce kan kujera ta ce
"Tashi Alhaji muyi magana."
nan da nan ya aiwatar da abun da ta ce
ya mike ya zauna.
zama ta gyara tana kallon shi sannan ta ce
"Ina takaddun kadarorin ka suke ina so ka tattaro su duka ka bani, yanzun nan."
ya ce "To Hajiya Karima amma basa d'akin nan, ni da Abdurrahim ne kad'ai muka san in da suke, gashi ni bani da lafiyan da zan iya zuwa na d'auko miki."
ta ce "Kira shi Abdurrahim d'in yanzu kace ya taho da su."
ta d'auko wayarsa ta mika masa bayan ta danna kira wa lambar Abdurrahim.
ya yi ta ringing har ya yanke ba'a d'aga ba.
takuma mai da kiran a karo na biyar shima har yakusa yankewa kafin aka d'aga.
da sauri ta saka wayar a amsa kuwa ta mika masa.
daga cikin wayar aka ce
"Ayi hakuri ranka shidad'e Sir yana Operating room yana surgery."
karb'ar wayar tayi ta kashe sannan ta ce
"Yana dawowa kasashi ya kawo maka a daren nan, zan zo na karb'e su da safe."
ya ce To.
ta mike ta fita.

Bayan sallar isha Aunty Ammah Mommy Mom Hajiya, da 'ya'yan su.
duk suna cikin parlour'n Daddy,
in da Abdurrahim da Abbie da Dad suke ciki tare da Daddy dan yau jikin nasa ya tashi fiye dana kullum.
Aunty dake zaune tayi jugum, sai addu'a take cikin ranta.
gaba d'aya hankalin ta baya jikin ta yana gurin Daddy, sai kwalla take ta sharewa a b'oye.
Aunty ta nisa ta ce
"Hajiya nace ko za'a kai Daddy gurin magani ne a d'an tab'a na gida, a had'a jinya biyu ko Allah zai sa aci karfin lamarin."
"Ba ke zaki bada wannan shawarar ba mu zamu yanke."
cewar Umma Karima da ke shigowa parlour'n maganar Aunty ya dira a kunnenta.
ta karaso ciki tana cigaba da fad'in
"Mu masu 'ya'ya da mukasan zafin sa mu zamu yanke hakan, bake da bakisan zafin sa ba,
sabo da kin raina kulawar da Abdurrahim yake bashi, likitan da likitotin kasar waje suka yadda da aikin sa fiye da nasu, yake jinyar sa shine zaki kushe kokarin sa,
to mu masu 'ya'ya mun yadda da aikin sa bamu yarda akai shi wani guri ba,
ke da baki haifi ko d'an hanji da shi ba baki isa ki rika nuna mana yadda zamuyi ba."
Aunty ta girgiza kai tana murmushin takaici ta ce
"Idan ma tunanin ki hakan nake nufi Abdurrahim yakasa kula da shi, to kicigaba da sawa ranki hakan,
sannan baki da ikon hanani magana akan Daddy, yadda kike auren shi haka nima nake auren shi,
'ya'ya kuma wannan kin shiga hurumin Alla dan shi ya tsara hakan,
dan Allah Hajiya Karima ki barni naji da abin da ke dami na."
Aunty ta karasa maganar tana had'a hannayen ta biyu zuciyar ta na d'aci.
Mommy ta ce
"Mttss aikin banza sai arika nuna an fi kowa damuwa da Alhaji,
idan gurin magani ne ma ina ne za'a kai shi, a fidda shi makiya su ji dad'in samin galaba a kanshi."

Hajiya ta ce
"Eh to nima dai zuwan Baba Salehu na Yelwa kafin su koma yake min maganar ko za'a had'a dana gida ne, sai a gwada a gani baza'a fasa na asibitin bama."
Umma Karima tayi saurin cewa
"To idan ma za'a had'a dana gida mu bamu amince a d'auke shi a kaishi ko ina ba, sai dai a kira mai maganin yazo gida nan,
kuma mu zamu nemo mai maganin idan akayi ba'a dace ba sai ta nimo nata,
ko ba haka ba Hajiya Halima?."
Mommy ta ce
"Kwarai kuwa."
Hajiya ta ce
"To ai shike nan mudai sauki muke fata masa, sai ki kirashi mai maganin yazo gobe idan Allah ya kaimu,
idan baiyi ba ni da kaina zan d'auke shi mutafi Yelwan Shendam, abokin turawa yaje yana masa nasa jinyar ana kuma na gida,
ni wannan ciwo na Abubakar ma yana min kamar aljanu ne, amma dai mai maganin yazo dai mu gani."
kowa yarika tofa albarkacin bakinsa a gurin Aunty bata kuma cewa komai ba.
tana rayawa a ranta ita da kanta zataje ta karb'o masa magani tazo ta masa.
su Abdurrahim suna fita ta shiga.
batabar sashin ba sai kusan karfe 1 bayan tayi masa addu'o'i ta shafa masa.

Washegari Aunty tana idar da sallah taje ta duba Daddy,
tayi mamakin ganin sa har lokacin yana bacci.
Ajmaal ya ce mata ya tashi ya yi sallah yakuma komawa ne.
ta tofa masa addu'a kana ta koma sashin ta ta soma had'a masa gwaten acca, wanda shi ne yanzu yake d'an iya ci.

Wani irin zabura Feeryal dake bacci tayi.
da karfi ta ce
"Ammie kar ku barshi ya shigo gidan nan!."
Aunty da ta fito rike da basket mai d'auke da abincin Daddy ciki,
cikin hanzari ta shige bedroom d'inta.
akwance ta isketa idanunta a rufe da alamu dai bacci take.
Aunty ta juya tana kokarin fita.
taji an kuma fad'in
"Kar ku bari ya shigo gidan nan!."
da sauri Aunty ta juyo, jin wani irin murya ne ya yi maganar ba irin na Feeryal d'in ba.
ido Aunty ta waro ganin yadda jikinta ke jijjiga hatta gadon jijjiga yake, tamkar zai karye.
kafin tayi aure tayi wani irin
mikewa tsaye da kafafunta a kan gadon.
cikin wani irin hargitsastsen murya ta ce
"Kar ya shiga ya dakata a gurin!!."
tayi maganar tare da fasa wani irin kara mai firgitarwa.
da sai da gidan gaba d'aya ya d'auki amon sautin mai tarin tsoratarwa da rikitarwa.
kafin Aunty ta ankara har ta duro a gadon tayi waje a guje.
Aunty ta bi bayanta tana kira dan kayan bacci ne riga da wando a jikin ta.

Umma Karima da me maganin da ta kawo suna daf da shiga side d'in Daddy.
Feeryal kamar mai gudu kan walkiya ta iso gurin,
wani irin damka tayiwa rigar sakin da ke jikin sa ta baya, ta finciko shi kamkar kwali ta d'auka ta jefashi can ya fettu da jikin garu. ta saki wani irin. haniniyar ihu, tayi kansa ta mika hannu zata damko shi......!

Mommyn Twins ce

Da karfi aka rike hannayenta duka biyu ta baya, tayi wani irin ihu tare da kokarin fisgewa.
tana wani irin gurnani tana sunkoyowa kan boka Mali, ya yin da fuskarta ke rufe da gashin kanta.
Abdurrahim ya yi baya tare da kuma janyo hannayen ta daya rike duka biyu ta baya, har sai da bayan ta ya garu da kirjin sa.
da sauri boka Mali ya dafa jigin bango ya mike ya tattari kwaryar da ya toho da shi a hannunsa wanda sanadin feud'e shi da akayi jikin bango ya tarwatse.
yashiga tattara fasassun da sauri jikin sa na kyarma.
Feeryal na ihu tana tuma niman kwacewa a hannunsa tayi kan boka Mali.
ai yana gama kwashe fasassun kwaryar ya d'au sandarsa ya zura a guje.
Umma Karima ta bi bayansa tana kira tuni yafita a gidan da mugun gudu.
Aunty ta sa hannu a kai tana salati ganin yadda Feeryal take niman kwacewa a hannunsa.
tuni ya murd'eta ta zube kasa ya danneta.
kana ya shiga karanto wasu ayoyi daga cikin alkur'ani yana tufa mata.
Umma Karima ta dawo da sauri kamar hauka sabon kamu,
tana fad'in
"Gantalalliya asararriya kin fasa kwaryar hankalin ki ya kwanta."

A ciki kuwa Daddy na kan azabtuwa cikin bacci.
yau abubuwan da yake gani masu firgitarwa da ban tsoro sunfi na kullum.
wannan hasken da yake zuwa taimakon sa cikin bacci shi yakuma zuwa a yanzu ma, dai-dai sanda aka danna masa mashin wuta a kahon zuciya ana daf da burma masa.
wannan hasken ya bayyana.
hasken ya tarwatse halittun, da suke zagaye da Daddy suna azabtar da shi. kana hasken ya wuce.
daga can ya soma jin muryar da ke magana a duk san da hasken nan ya gifta.
"Kar ka bari tayi nesa da kai ka janyo hasken can cikin rayuwar ka, idan yau ka kub'uta gaba ba lallai ne ka kub'uta ba, tabbas za'aga bayan ka, kar ka bari ta yi nesa da kai ka janyo sa cikin rayuwar ka, ana daf da ganin bayan ka,
hasken kub'utar ka ce ka rike ta kar ta tsere daga rayuwar ka!!."
da karfi yake jijjiga daga d'aurin da akayi masa,
da igiyar wuta, dake shiga sokar jikin sa.
yana ta fafutukan niman ta inda zaiyi ya kunce ya juya yaga hasken kub'utar sa.

Su Mommy Hajiya da ihun Feeryal tun na farko kafin ta iso gurin ya fito da su daga sashin Daddy.
Mommy da jike ke rawa ganin tashin hankali a idon ta ta ce
"Wannan yarinyar ban yarda da ita ba, ke nan jinyar Alhajin ne bata so ayi, saketa ta tafi duk in da zataje Abdurrahim!."
Hajiya kuwa kirji ta buga ta ce
"Yau naga siddabaru to baza'a kawo min tashin bori cikin gidan d'ana ba, daina tofa mata addu'ar nan abokin turawa jata ka fita mana da ita anan."
Aunty ta maso da sauri hankali tashe ta ce
"Dan Allah Abdurrahim ka tai make ni ka kaimin ita side d'i na, dan Allah."
ta had'a hannayen ta biyu.
baiyi magana ba har ya kai karshen ayar da yaja.
ya d'ago yaga kaf 'yan gidan maza da mata idanunsu a kan su,
Zaraddin na ta gaba-gaba ya kafe ababen kirjinta tarr da ido.
wan da babu bra iya rigar baccin ce mai tsamtsi a jikin ta.
daga kasan rigar ma yad'an bud'e har kusa da cibiyarta, ana ha hango farin fatar shafaffen cikin ta.
da hannu ya yi musu alamun kowa ya watse.
Zaraddin yad'an sosa keya yawani lumshe ido tare da jan numfashi.
yana jin hannunsa na kaikayi ina ma ace yaje ya damki balambalon kirjinta.
Chapter 35 · 0% Book details