← Book details Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t Local reading mode
READING PART 25 OF 43

Sashe 25

Feeryal Part 2 Complete Hausa Novel.t · about 8 min read

A hankali ta gyara zamanta ta janyo laidar ta bud'e.
ganin kaya ne ciki, a sannu ta cicciro su.
doguwar rigar abaya ne a cikin laidar sa,
da takalmi mara tudu sosai cikin kwalinsa.
sai pant da pat duk a laidodin su sai bra shima sabo guda d'aya, da underwear,
sai turare.
kai ta sunkuyar kamar wacce take gaban sa.
ta kai mintuna biyar kafin ta iya mikewa ta d'au laidar ta shige toilet d'in room d'in.
a gyare tsaf ko ina kwalkwal.
ta aje laidar ta tub'e yagaggun kayan kijin ta.
sai sannan taga in da jini ya b'ata bayan rigar.
wani kunya ya kamata, sai mammakewa take kamar wanda ake ganin ta.
da sauri ta d'ago rigar sa da ya bata ta rufe jikin ta, taga shi jinin bai tab'a ba.
sassanyar numfashi ta sauke.
da kyar ta karasa cire ragowar kayan jikin ta, bra da pant da pat d'in da ya karkace garin kokuwa har jini ya sami damar b'ata mata kaya.
kana tayi wanka da sabon sabulun da tagani a toilet d'in cikin kwalinsa.

Kana ta d'au pat da pant da underwear duk ta saka.
ta d'au abayar ta saka batare da ta sa bra'n ba, dan dama ita ba ma'abociyar sa bra bace, na jikin ta ma dama yana ta damin ta.
kana tayi mayafi da d'ankaalin abayan.
sannan ta feshe jikin ta da dadad'an turaren, tana yi tana lullumshe idanunta dan ba karamin dad'in kamshi ya yi mata ba.
duk kayan da ta cire ta had'a ta zuba su cikin dosbin da ta gani a cikin toilet d'in.
kana ta fito da sauran pant da pat da bra'n da batasa d'in ba,
da kuma rigar sa.
a bakin gado ta zuba su tana zama akayi knocking jin shiru ba'a turo kofar ba ta ce a shigo.
wata ma'aikaciyar hotel ne ta shigo sanye da uniform irin na ma'aikatan hotel.
tana rike da katon tray ta karaso tayi mata sannu sannan ta dire tray'n saman table, ta fita.

Ido ta zubawa tray'n kayan abincin yadda take jin kanta ma bata ko jin yunwa,
burinta yanzu ta ganta kusa da Ammie'n ta.

Ba'a jima ba ya shigo, ganin bata ci komai ba ya tab'e baki.
ta mike da sauri gudun kada ya juya, gashi ya fi ta sauri bazaka fahimci saurin tafiyar sa ba sai idan kuna jerawa,
har da sassarfa sai da ta had'a d'azu kafin ta cim masa.
yadda ta miken ya baiwa jikin ta damar motsawa.
karaf idanun sa ya sauka a kanta.
da sauri ya janye idanunsa tare da sauke shi kan gadon

"Wannan fa kin bar ma wa ko ma ki saka kafin ki fito."
ya yi maganar tare da juyawa ya fita.
a hankali tabi in da yake nunawa kan bra'n da bata sakaba.
ta kuma maida idanunta kan kirjinta
ido ta d'an waro ganin gyalen abayar bai rufe mata kirjin duka ba,
ga kan ababen kirjin a tsaitsaye sunfi to sosai ana iya hango shatin kansu ta saman rigar.
taji matukar kunya sosai jiki a sanyaye ta d'au bra'n sai da ta koma toilet kafin ta saka ta fito.
ta kwashi sauran kayan ta zuba su cikin laida kana ta koma ta zauna.

Ganin shiru bata fito ba ya turo kofar, tana ganin shi ta mike da sauri ta zura takalmin wan da ya yi mata dai-dai kamar an gwada ta,tabi bayan sa.

Tun da suka shiga mota suka fara tafiya ko kyakkyar motsi batayi ba har suka iso gida.
lokacin karfe 3 na dare.......!

17
Tun bayan wasewan 'yan kawo amarya amarya Kuraiba ta mike ta tub'e kayanta, ta fad'a bayi, ta kuma solle wanka,
ta saka wasu kaya da babu marabansu da babu, dan komai na jikin ta a na gani.
ta shafa turaruka ta d'au ko jakar kayan matan ta, ta sha na sha ta cusa na cusawa, sannan ta haye gado.
tana zuba idon ganin angon nata, amma har d'aya tayi biyu ta wuce babu alamar sa.
tayi sintiri cikin d'akin har ta gaji ta kwanta, bacci ya d'auke ta.

Tashin hankalin da Aunty ta shiga ba zai misaltuba.
Daddy yasa aka bincika gidan gaba d'aya babu ita.
bai masa ba ya zaga da kansa,
Mommy da Umma Karima suka rika mita, wai ya tada hankali akan wata da ita ba komai bace, wata kila ma tabi saurayi ne dama ta saba.
Hajiya ko cewa tayi, yaje ya kwanta kar ya yadda ya tada hankalin sa har ciwon sa ya tashi a kanta, dan bata da asara
ita Hajiyar ce da da asara.

A daren Daddy ya baza jami'an tsaro.
dan su tunanin su mai tawagar d'aukar amarya ne ya turo mutanen sa suka d'auke ta.
a b'angaren Ammah ma ita da Miemie Abbie basuyi bacci ba, fargaba da tunanin halin da Feeryal d'in take ciki ya hanasu rumtsawa.
Abbie da Ammah suka sako Miemie gaba da wayarta da sukayi hoto da yarinyar da suka tafi da Feeryal.
sukaje sashin Aunty.
Daddy ya ce a daren nan kuwa zai bada binciken yarinyar, duk suka d'ungumo sukayi waje.

Abdurrahim na gyara parking Feeryal ta kai hannu tana kokarin bud'e motar
maganar sa ta jiyo
"Ina ke aljana ce me ya hana ki iya kare kanki?."
da sauri ta waigo ya tsare ta da ido.
yana nad'e bandaji a hannunsa, daya d'an ji rauni garin dukan su, yana d'an fidda jini.
a hankali ta sunkiyar da kanta,
ta bud'e kofar ta fita.
ta na tsaye sai da yagama wayar da yake kafin ya fito, ya yi gaba ta bi bayan sa.
gidan shiru babu motsin kowa sai security dake bakin get.
da sauri ta d'aga kafa ta biyo shi da sassarfa jin kukan magen Hajiya da ga sashin ta.
dai-dai san da su Daddy suke fitowa.
ganin su tare cikin hanzari suka nufo su.
Daddy yana fad'in
"Abdurrahim tun d'azu da na neme ka security suka ce min ka fita,
nayi ta kiran ka in sanar maka abun da ke faruwa baka d'aga ba,
a ina ka samo ta."
Daddy ya yi maganar dai-dai san da suke karasowa.
Feeryal ta sa gudu ta rungume Aunty, tare da fashewa da kuka.
Aunty ta rungume ta gam-gam tana fad'in
"Feeryal ina kika shiga, nayi zaton wad'an can mutanen ne suka kuma d'auke ki,
mene ne me ya same ki!?."
Miemie ma ta rungume ta ta baya.
baki ya tab'e ganin yadda take wani kukan shagwab'a.

Ya cewa Daddy
"Wayar da kake kira tana gida ne Daddy da d'aya wayar na fita."
"Kai alhamdulillah duk hankalin mu ya tashi, mun d'auka mutanen nan ne suka kuma d'auke ta,
amma dai babu wata matsala ko, a ina suka tsaya ne haka ko can gidan surukanka ne aka wuce da su?
to kukan na mene ne kuma Feeryal ai mun godewa Allah tun da abin da muke zato bai faruba."

kuma tab'e baki ya yi yana shirin barin gurin.

Da sauri Daddy ya ce
"Me ya same ka a hannu haka."
kowa ya maida hankalin sa kan sa, Feeryal ta saki Aunty ta tsaya itama ta kallon sa,
jiki a sanyaye dan tasan garin ceton ta ne yaji ciwon.
"Ba wata matsala ba ce Daddy."
ya fad'a a takaice

Abbie ya ruko hannun nashi yana cewa
"Kamar jini ne ke fita babu wata matsala kace?."
"Eh ba komai Abbieh."
ya fad'a yana wuce wa ya nufi side d'in sa.
Feeryal tabi bayan sa da kallo murya a sanyaye ta ke fad'in
"Ina ga garin dukan su ne yaji ciwo."
da sauri kowa ya dawo da hankalin sa kanta.
Daddy ya ce
"Garin dukan su wa?."
rau-rau tayi da ido sai ga hawaye sharr,
murya na rawa take fad'in
"Wasu ne wasu ne."
sai kuma ta fashe da kuka.
da sauri Aunty ta ruko ta hankali tashe sai yanzu ta lura da kayan jikinta wasu ne daban ba ashobin bikin sa ba.
Aunty da hawaye ya fara zuba mata tashiga girgizata tana fad'in
"Feeryal su waye ne niman gudu da ke sukayi, da niman yi miki fyad'e ko."
kai ta shiga gyad'awa hawaye na zuba.

Aunty ta kankame ta tana cewa
"Allah bazai tab'a baiwa masu mugun nufi a kan ki dama ba, tun kina karamar ki ake bibiyar son ganin an ruguza darajar ki,
Allah bazai basu sa'a ba."
"Insha'allahu kuwa."
cewar Ammah tana bubbuga kafad'ar ta.

Jikin kowa ya yi sanyi Daddy yabi bayan Abdurrahim da kallo da yake shigewa side d'in sa.
ya yi murmushi tare da girgiza kai
"Abdurrahim ke nan da zurfin ciki wato baya son fad'a gudun kada hankali ya tashi."
ya kuma girgiza kai, sannan ya ce kowa yaje ya kwanta ad'an tab'a bacci dan yanzu gari zai waye.

Su Abbieh sukayi musu sai da safe suka wuce sashinsu.
suma suka shige ciki.
Daddy ya wuce bedroom d'in Aunty.
in da Aunty ta ja Feeryal zuwa bedroom d'in ta, dan ta lura har yanzu akwai tsoro tare da ita ba lallai ne ta iya bacci ita kad'ai ba.
kamar yadda bata saba b'oyewa Ammie'n nata komai ba ta labarta mata duk abin da ya faru a daren.
Aunty ta ce sai an nemo yarinyar nan an hukuntata da bata da kishin jinsinta tana d'iya mace.

Washegari a masallaci bayan an idar da sallah Daddy da Abbie suke tambayar Abdurrahim ya hanun nasa.
ya ce ba ko mai ya warke.
Daddy ya dube shi cikin kulawa ya ce
"Jinyar jiya a ce yau ya warke."
"Ba wata matsala ba ce da sauki Daddy."
"Yauwa to dai da saukin zakace."
Daddy ya fad'a ya juya yana amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan suke yi masa.

Dad daya zuba kunnuwan sa gurin su ya ce
"Wai rauni yaji a hannun nasa ne?."
Abbie ya ce
"Eh jiya ke nan da aka nimi yarinyar nan Feeryal, ashe wasu 'yan iskan yara ne b'ata gari suka d'au ke ta,
garin kwato ta ne yaji raunin."
Dad ya kama baki yana cewa
"Amma dai ba kariya ba dai ko?."
Abbie ya ce
"Aa haba ba kariya bane d'an jin ciwo ne kawai."
"To Allah ya sauwaka."
cewar Dad ya zame jiki ya yi cikin gida.
Chapter 25 · 0% Book details